LABARAI
Masu zanga-zanga a Kano sun nemi a biya musu bukatu uku
Zulaiha danjuma
Yayin da zanga-zangar juyin juya hali ta shiga kwana na hudu a Kano, masu zanga-zangar #EndSARS, #Endbadgovernance da dangogin su sun nemi da a biya musu bukatu uku kafin su janye.
Kano Focus ta ruwaito masu zanga-zangar sun nemi gwamnati da ta kawo karshen mulkin kama karya da kawo sauye-saye a ayyukan jami’an tsaron kasar nan da kuma kawo karshen matsalar tsaro a arewacin Najeriya.
Matasan sun faro zanga-zangar ta yau litinin ne da misalin karfe bakwai na safe, da ga kan titin Sarkin yaki da ke unguwar Sabon Gari zuwa Faransa road suka bi ta No mansland, zuwa Zungeru suka tike a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.
da yake zantawa da Kano Focus guda cikin mansu zanga-zangar Ahmad Aminu ya ce sun fito ne domin su nuna rashin jin dadin su da yadda al’amura ke tafiya a kasar nan.
Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta yi abin da ya da ce wajen gyara fasalin jami’n tsaron kasar nan.
Ita kuwa Fatima Sani cewa ta yi ita fa ta fito ke nan sai kuma yadda Allah ya yi da ita ko kuma gwanmati ta gyara rayuwa jama’a.
“Zamu ci gaba da yin zanga-zangar nuna adawa da masu garkuwa da mutane, da masu kisan jama’a ba gaira ba dalili, da kuma uwa uba boko haram” a cewar ta.
Ita kuwa Jane Mbah ta ce zanga-zangar ta wuce batun a kawo karshen SARS, sai dai batu ne na kawo karshen gwmnatin kama karya a kasar nan.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Headlines
Kano State Reforms: Sa’adatu Rimi University Reverts to College of Education Status
The Kano State Executive Council has approved the conversion of Sa’adatu Rimi University of Education back to Sa’adatu Rimi College of Education, Kumbotso, while maintaining its status as a degree-awarding institution.
In a statement issued by the Commissioner for Information and Internal Affairs, Baba Halilu Dantiye, the decision was made to enhance educational quality and streamline management in the state’s higher education sector.
The move follows the 18th meeting of the Executive Council, held on September 18, 2024, after extensive consultations with stakeholders and recommendations from a high-powered committee tasked with reviewing the institution’s status.
The committee raised concerns over the transition to university status, citing risks such as the potential loss of experienced lecturers, salary disputes, and administrative challenges.
Dantiye noted that similar institutions nationwide have operated successfully as colleges of education while offering degree programs through the “Dual Mode” system, as introduced by the National Commission for Colleges of Education (NCE).
This system allows institutions to maintain their core structure while expanding their academic offerings.
Governor Abba Kabir Yusuf has approved the immediate dissolution of the university’s management, with the Vice Chancellor directed to hand over to his most senior deputy.
The government assured that current students would not be affected, as they will continue their studies without disruption.
Additionally, the university’s certificate will be preserved for future use, and the institution will continue to offer both its traditional courses and new degree programs.
This strategic decision underscores the Kano State Government’s commitment to ensuring the growth, stability, and academic excellence of its educational institutions.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.