KANUN LABARAI
Zanga-zanga- ‘yan sanda sun kama likita da ya harba bindiga a Kano
Nasiru Yusuf
Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wani likita bisa zargin harba bindiga yayin arangama tsakanin masu zanga-zangar #EndSARS da kuma yan daba a nan Kano.
Kano Focus ta ruwaito kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Habu Sani ne ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Talata.
Mista Sani ya ce rundunar ta kuma samu harsashi mai yawa daga wurin likitan da ta kama.
Ya ce ko da yake har yanzu rundunar ‘yan sandan bata samu rahoton mutuwar koda mutum daya ba, amma mutane shida sun jikkata.
Ya kuma ce masu tarzomar sun kone matoci bakwai inda kuma suka farfasa guda takwas, yayin da kuma suka kone Babura biyu.
Mista Sani ya kara da cewa masu tarzomar sun kuma tarwatsa wani Gidan shakatawa a yanin Hausa da ke Sabon Gari.
Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa babu abinda ya samu dukkanin wuraren bauta da suka hadar da masallatai da majami’u(coci-coci).
Haka kuma dukkanin makarantun da ke yankin da al’amarin ya faru an basu kulawar da ta da ce.
Sai dai Kano Focus ta gano masu tada husumar sun lalata wani kantin saida kayayyaki mai suna Galaxy da ke kan titin Sarkin yaki da kuma shagon saida abinci na chicken republic duka a unguwar Sabon Gari inda kuma suka yi awon gaba da kayayyaki masu yawa.
Haka kuma masu husumar sun kone wani Otal mai suna hotel, Summit Lodge, da ke kantitin Hausa a unguwar Sabon Gari.
Haka zalika a kan titin zuwa filin jirgin sama masu ta’asar sun kone motoci dab da makarantar sakandire ta St.Thomas.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
Hausa
Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.
Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.
Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.
Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.
Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.
“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.
“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”
Hausa
Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote
Nasiru Yusuf Ibrahim
Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.
Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .
Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.
“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.
Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun da basu samu damar biya ba a baya.”
Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari, gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.
“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al’umma.” Dangote.
Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.
“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”
Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada rade-radi da jita-jita.