Connect with us

KANUN LABARAI

Gwamnatin Kano za ta mayar da ma’aikatan wasu hukumomin ta  zuwa makarantu

Published

on

 

Mukhtar Yahya Usman

Gwamnatin Kano ta ce za ta zakulo masu shaidar karatu na koyarwa da ke aiki a ma’aikatu daban-daban a jihar nan domin mayar da su aikin koyarwa.

Kano Focus ta ruwaito sakataren gwamnatin jiha Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da hakan a ranar Talata ya yin da ya ke kaddamar da kwamitin da zai lalalubu matsalolin da ke hana shirin Ilimi kyauta kuma dole na gwamnantin Kano ya ci gaba.

Usman Alhaji ya ce bai dace mutum na da shaidar karatu na koyarwa ba kuma ya tafi yana aiki a wasu bangarorin da basu shafi Ilimi ba.

A cewarsa a don hakan ne ma aka dorawa kwamitin alhakin zakulu irin wadannan mutane a kuma mayar da su makarantu domin su ciyar da harkar Ilimi gaba.

Ya ce wadannan mutane za su koyar ne a dukkanin bangarorin makarantu da ake da su da suka hadar da firamare da sakandire har ma da manyan makarantun gaba da sakandire.

Haka kuma kwamitin zai yi aikin nazartar dukkanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati domin gano wadanda ayyukan su suka yi  iri daya domin hadesu wuri guda.

Ya ce bayan hadesun ragowar ma’aikatan za a mayar da su bangaren koyarwa domin su tallafawa jihar su.

Kwamitin mai mambobi 19 na da tsohon babban sakatare a ma’aikatar ilim ta Jiha Alhaji Danlami Garba a matsayin shugaban.

Sai kuma Abdullahi Balarabe daraktan gudanarwa a ofishin sakataren gwamnati, da kuma Abba A Dungurawa da ga ofishin shugaban ma’aikata na jihar Kano a matsayin sakatare na biyu.

Haka zalika Usman Alhaji ya kaddamar da wani kwamitin da zai duba yadda za a farfado da tattalin arzikin Kano bayan wucewar COVID-19

Ya ce gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi hangen irin halin da za a shiga  na rayuwa bayan Corona musamman ma matsin tattalin arziki da hakan ya sa ya farga tun da wuri.

Kwamitin da Sakataren gwamnati Usman Alhaji ke shugabanta ya hadar da mambobi da ga dukkanin bagarorin da suka shafi tattalin arziki a jihar nan.

Hausa

Abun da yakamata a sani game da ‘Tofa Cup’

Published

on

Jamilu Uba Adamu

Jamilu Uba Adamu 

Tarihi abune mai muhimmancin gaske, musamman na abun da yashafi wasanni.

Amma mu anan Nahiyar ta Afrika, musamman a arewacin Najeriya ba a dauki tarihi da muhimmanci ba.

Shi tarihi na wasanni, yakan taimakawa ma su sha’awar sa sanin abun da ya faru a baya, dama wadanda suka ba da gudummawa, har aka kawo yanzu don kara shirin yadda za a tunkari gaba.

Don haka ne, a wannan dan shafin wasanni zan  kawo tarihin gasar cin kofin Kwallon k’afa na Tofa. Wanda ake bugawa a Jihar Kano.

Wannan gasar cin kofi mai tarihi, wanda yanzu haka shine kofi mafi daraja a rukunin kofuna da ake bugawa a duk gasannin kofuna da hukumar Kwallon kafa ta kano take sakawa.

Itadai wannan gasar Kofi mai dinbin tarihi a harkar wasan kwallon k’afa a wannan Jiha ta Kano ta samu asali ne a tun shekarar 1979, a lokacin ana kiranta Danwawu Cup.

Alhaji Dan wawu (Ya taba rike matsayin mai kula da harkar wasanni na Arewa, a zamanin firamiyan Jihar Arewa na farko Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto). A wancan zamanin shi ne wanda yake daukar nauyin gasar, wacce aka fara da Kulub guda Takwas ( 8 ), wanda suka hada da; Zumunta dake Unguwar Fagge da Super Star (Goro Dutse) da Sanka Vipers (Unguwar Sanka) da Kofar Mata da Kofar Wanbai da Yakasai Rovers da Y.B.C Kano da Golden Star da kuma Gwagwarwa Yaks.

Sune kulubluka na farko da suka fara bugawa a shekarar da aka fara wannan gasa mai tarihi.

A shekarar 1985  gasar ta koma Tofa Cup, bisa daukar nauyin gasar da Alhaji Isyaku Umar Tofa ( Makaman Bichi ) ya yi, bayan rasuwar Margayi Alhaji Danwawu Fagge.

Daga baya a shekarar 1999, aka canzawa gasar tsari da kuma fasali, inda ta koma TOFA Firimiya Lig.

Wannan gasar kofi mai tarihi ta taimaka kwarai da gaske wajen bawa matasan yan kwallon kafa, damar gogewa da kwarewa har zuwa babban mataki na k’asa.

Yanzu haka a wannan shekara da muke ciki ta Dubu biyu da Ashirin da daya, akwai kulubluka sama da ashirin da biyar dake fafatawa a wannan gasa mai tarihi a kwallon kafa a jihar Kano.

Jamilu Uba Adamu,

Mai sharhin kwallon k’afa ne.

jameelubaadamu@yahoo.com

Continue Reading

Hausa

Wani direban adaidaita sahu ya mayar da kwamfiyutar da aka manta a mashin dinsa

Published

on

alam Habibullahi Ali Alkali

Nasiru Yusuf

Wani direban adaidaita sahu Malam Abdullahi ya mayarwa da wani fasinja kwamfiyutar da ya manta a mashin din sa.

KANO FOCUS ta ci karo da wani rubutun wani mai sharhi a sahar Facebook Shehu Mustapha Chaji inda ya ce a ranar Juma’a 3 ga watan Disamba Malam Abdullahi ya dauko Malam Habibullahi Ali Alkali daga Sabuwar Jami’ar Bayero Kano, zuwa Gwanmaja a adaidaita sahu.

Sai dai Malam Habibullahi ya sauka ya manta Jakara kwamfiyutarsa a adaidaita sahun.

Bayan har ya fitar da rai kan kwamfiyutar, sai ga direban adaidaita sahun ya dawo masa da ita har gida.

Chaji ya ce wannan direban adaidaita sahu ya cancanci yabo. Saboda lokacin suke tare da Malam Habibullah har matarsa ce ta kirawo shi, tana jaddada masa cewa “ya samu kuwa ya kai kwamfiyutar nan ga ma’abocinta?”

“Hakika itama wannan mata ta cika mace ta gari mai karfafar gwiwar mijinta akan gaskiya da rikon amana, tare da cewa kuwa masu karamin karfi ne.

Da fatan kungiyar ‘yan a daidaita sahu a Jihar Kano zasu rika karrama ire-iren wadannan ya’yan nata masu amana da riko da gaskiya.”

Continue Reading

Hausa

Malaman Tijjaniyya na Kano sun kai wa Khalifa Muhammad Sanusi ll mubaya’a

Published

on

Nasiru Yusuf

Majalisar Shura ta Dariqar Tijjaniyya ta Jihar Kano ta kai wa Maimartaba Sarkin Kano na 14 Malam Muhammadu Sanusi II mubaya’a bisa nadin da aka yi masa na babban Khalifan Shehu Ibrahim Inyass a Nigeria.

KANO FOCUS ta ruwaito cewa Malaman sun yi wa Malam Muhammadu Sanusi ll mubaya’ar ne ranar Asabar karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Awaisu Limanci.

Malaman da suka kai ziyarar mubaya’ar sun hada da Khalifa Tuhami Shehu Atiku da Shehi Shehu Maihula da Imam Muhammad Nura Arzai da kuma Sheikh Dayyabu Dan Almajiri.

Sauran sun hada da Khalifa Hassan Sani Kafinga da Khalifa Bashir Musa Kalla da Khalifa Fatihi Uba Safiyanu da Khalifa Kamilu Yalo da Sheikh Tijjani Maisalati Indabawa da kuma Sheikh Kabiru Zango.

Tawagar kuma ta kunshi zuriyar Shehu Ibrahim Inyas mazauna Kano karkashin jagorancin Sayyada Rahama Ibrahim Inyas.

Continue Reading

Trending