KANUN LABARAI
‘Yan wasan Hausa a Kano sun yi tofin alatsine ga shugaban Faransa
Aminu Abdulahi
Wasu daga cikin jaruman Kannywood a nan Kano sun yi tofin alatsine ga shugaban kasar Faransa Emanuel Macron bisa nuna goyan bayansa kan batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Manzon Allah (S.A.W.)
Kano Focus ta ruwaito jaruman na ci gaba da yin tofin alatsine ne a shafukansu na Instagram, Twitter da kuma Facebok.
Emanuel Macron dai ya fito fili ya nuna goyon bayansa kan zanen barkwanci da wani kamfanin kasar Faransa ya wallafa kuma siffantashi da Annabi (S.A.W), da wani malami a kasar ya yada shi ga dalibai.
Wannan dalili ne ya sanya musulmi a fadin duniya ke caccakar shugaban kasar ta Faransa bisa goyon bayan da ya bayar na cin zarafin annabin rahama.
Cikin dubban masu yin tofin alatsinen har da juramai da masu shirya fina-finan Hausa da suka dinga yin rubutun tsinuwa, wasu kuma suna wallafa hoton bidiyo da tsinuwa ga Emanuel Macron.
Falalu A Dorayi
Falalu Dorayi mai bada umarni ne kuma mashiryin fina-finai, cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya bukaci jama’ar muslmi da su tsinewa shugaban kasar ta Faransa da ‘yan koransa.
Ya kuma ce jihadi ne jama’a su yi iya kokarinsu na la’antar sa, musamman ma a shafukansu na sada zumunta.
A cewarsa abin kunyane a ce matasa sun kasa yin yin wani rubutu a shafukan su na sada zumunta da zai kare martabar shugban hallitta.
“Idan har zaka iya yin rubutu ko saka bidiyo don taya kanwar ka ta Likoro ko Fandogari murnar zagayowar ranar haihuwar ta, ko taya abokin ka murna idan wani abu ya same shi, amma ‘dan karamin rubutu da za kayi kace kana nuna bakin ciki kan masu cin zarafin manzon Allah S.W.A sai ya gagara, wannan abin takaici ne” inji Falalu.
Ali Nuhu
Shi ma guda cikin jaruman fina-finan Hausa Ali Nuhu ya wallafa wani rubutu a shafin sa na Facebook da ya yi yabo ga fiyayyen halitta tare da yin tsinuwa ga masuyin batanci ga shugaban halitta Manzon Allah S.W.A.
“Ya Rasulallah S.A.W. Kai Rahmane garemu a duniya kai Rahma ne gare mu a Lahira.
“Muna sonka fiye da kanmu, da Iyayenmu, da ‘Ya’yanmu, muna sonka fiye da duk abinda muka mallaka.
“A shirye muke mu bayar da jininmu akan ka ya Rasulallah.
“Allah kai tsinuwa ga duk wanda sukai batanci ga Annabin mu Muhammad S.A.W Allah ka wulakantar da su tun anan duniya #WeLoveMuhammad,” inji Ali Nuhu.
Haruna Salisu (Cizo)
Shima daya daga cikin mawaka a masana’antar mai suna Haruna Salisu da ake kira ‘Cizo One Germany’ ya yi kira ga al’ummar musulmi da su kauracewa siyan duk wani abu wanda ya kasance mallakin kasar Faransa ne.
Ya ce matukar al’ummar musulmi suka kauracewa siyan kayayyakin da ake sarrafawa daga kasar tabbas hakan zai sa kasar ta shiga taitayin ta.
Ya kara da cewa addinin musulunci addinine dake son zaman lafiya hakan ta sanya mulunci ke mutunta kowane addini a duniya.
Umar Nagudu
Mawaki Umar Adam Gambo Nagudu ya wallafa bidiyo a shafin sa na Instagram inda ya yi kira ga sauran mawakan Hausa da al’umma da su sani cewa kare mutunci da martaba ta manzon Allah shi ne gaba da komai.
Nagudu ya ce da yawan mawaka sunki cewa komai kan batancin da akayiwa ma’aiki duk kuwa da irin lokutan da suke shafewa a kafafen sada zumunta.
Ya kara da cewa babu amfanin cigaba da kasancewa a kafar sada zumunta da wasu jarumai da mawaka keyi matukar ba za su fito su nuna fushinsu ga irin cinkashin da akeyiwa al’ummar musulmi ba.
“Wani zaka samu yana da mabiya a kafa guda daya da suka haura miliyan biyu.
Kullum yana kasancewa tare dasu, amma ba zai iya yin rubutu na minti biyu ba don yin Allah wadai da abubuwan dake faruwa.
“Wannan abin kunya ne kuma kalubalene a garemu.” a cewar sa.
Ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da su hade kansu, a cewarsa ta hakane kawai za su iya kawo karshen cin kashin da kafirai kewa musulmi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
Hausa
Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.
Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.
Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.
Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.
Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.
“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.
“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”
Hausa
Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote
Nasiru Yusuf Ibrahim
Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.
Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .
Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.
“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.
Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun da basu samu damar biya ba a baya.”
Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari, gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.
“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al’umma.” Dangote.
Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.
“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”
Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada rade-radi da jita-jita.