KANUN LABARAI
Lafiya jari: Illoli 10 da kaciyar mata ke haifarwa
Zulaiha Danjuma
Wani kwarraren likitan mata da ke asibitin koyar na jami’ar Jos Dakta Kenneth Egwuda ya bayyana matsaloli goma da kaciyar mata ke haifarwa musamman ga ‘yan mata.
Yayin tattaunawa ta musamman da jaridar Kano Focus likitan ya ce kaciyar mata na jawo matsalar da ba safai ake iya maganceta ba.
A cewar sa matsalolin sun hadar da shigar cuta, karewar jini, wahala yayin haihuwa, da rashin haihuwar ma baki daya, sai kuma yoyon fitsari da kuma rauni yayin kaciyar.
Sauran sun hadar da Kaduwa, da daukewar sha’awa da kuma daukewar dararjar mace sai kuma mutuwa.
Shigar cuta
Dakta Egwuda ya ce yin kaciyar mata na gayyato cutuka iri-iri da kayayyakin da akayi amfani da su wajen kaciyar ke haifarwa.
Ya ce wasu cutukan da ake dauka sakamakon yin afani da karafan kaciyar sun hadar da cutar kanjamau (HIV), da cutar hanta da kuma ciwon sanyi.
“Dukkanin wadannan cutukan ba wadanda za a dauke su da wasa ba ne.
“Ba ko shakka mata na iya kamuwa da wadannan cutukan sakamakon yi musu kaciya.
Haka kuma matakur aka kamu da cutukan ba a dauki mataki da wuri ba shakka babu za a rasa rai.
Rasa jini
Likitan ya ce yiwa mata kaciya na jawo rasa jini a jiki da hakan ke jefasu cikin hadduran kamuwa da cutuka daban-daban .
“Rasa jini sakamakon yiwa mata kaciya shi ne mafarin bude Kofar kowacce cuta a tare da su.
“Babu yadda za a yi ka cirewa mace wani abu a matucinta ka ce jini ba zai fita, kuma fitar da ya ke yi yana saba ka’idar yadda ya kamata da hakan ke zama babban hadari a gare su”.
Wahala yayin haihuwa
Likitan ya ce matan da ake yiwa kaciya na fadawa cikin matsala ya yin haihuwa da ka iya sanyasu rasa abinda ke cikin su.
“Suna cikin hadari mai tsanani ya yin haihuwa musamman ma lokacin da suka zo turo jaririn su waje.
Hakan kuwa na faruwa ne sakamakon yadda aka yayyanka hanyar da jarin zai fito ya yi rauni harma ya zama tabo.”
Rashin haihuwa
Dakta Ggwudu ya kara da cewa kaciyar mata na iya jawo rashin haihuwa ga mata sakamakon matsalolin da ake samu yayin saduwa.
Ya ce matan da aka yiwa kwaciya na samun matsala sosai wajen samun ciki da haihuwarsa.
“A wasu lokutan daukar ciki kan zame musu matsala saboda raunukan da aka riga aka yi musu yayin kaciyar.”
Yoyon fitsari
Haka zalika likitan ya ce yoyon fitsari wata babbar matsalace da matan da aka yiwa kaciya ke fuskanta.
“Idan tsautsayi ya sa aka yanko mace da nisa har aka taba mahadar fitar fitsari to hakan na haifar da yoyon fitsari marar tsayawa.”
“A wasu lokutan musamman ma wanzamai na yankewa har su ta ba blader da hakan ke haddasa ,matsala domin idan an yanke ba zai sake tofowa ballantan ya koma ya rufe.
Rauni
Dakta Ggwuda ya ce tabon raunin da ka yiwa mata yayin kaciyar na ci gaba da girma a gaban mace lokaci bayan lokaci da hakan ke tsuke musu gaba.
“Tudun tabban da ke samu na toshe Kofar gabansu sosai da har ta kai mazajensu ba za su iya biyan bukatun su da su ba.
A cewarsa hakan kan jefa matan cikin matsanancin hali da wasu lokutan man har sai an yi musu tiyata.
dauke sha’awa
Likitan matan ya ce yiwa mata kaciya na rage sha’awar su ainun da hakan ke sanyawa suji basa bukatar saduwa da mazajensu baki daya.
Haka kuma ya ce a duk lokacin da mazajensu za su sadu da su suna fuskantar zafi mai tsanani da ke jefa su cikin damuwa.
Wannan kuma na taimakawa wajen daina shawa’awa baki daya.
Kaduwa
Likitan ya ce a mafiya yawan lokaci matan da aka yi wa kaciya na kaduwa ainun da hakan ke sanya su cikin damuwa a kowanne lokaci.
“Matan da aka yiwa kaciya na fadawa cikin damuwa tsahon rayuwarsu sakamakon yadda aka basu wahala lokacin yi musu.
“Kaduwar da suke yi lokacin da suke ganin yadda ake zurmuka musu karfe mai kaifi a gabansu, kuma suji ana yanka wani abu jikinsu na haifar da kaduwa mai yawa da galibinsu ke sanya su jijjiga
Rasa darajar ‘ya mace
liktan matan ya ci gaba da cewa kaciyar mata na sanya mata suji cewa sun koma ba ya, ba kamar sauran ma ta ba.
Ya ce matukar sauran mata ‘yan uwanta da suka san anyi mata kaciya to suna daukarta wata daban a cikinsu da hakan ke sayanta taji ta zama koma baya.
“Wannan na da alaka da yadda mace ke kallon kanta a matsayin wata marar daraja a cikin mata ko da kuwa tana da dararjar.
Mutuwa
Dakta Ggwuda ya ce mafi tsanani ga dukkan haduran da aka lissafa shi ne mutuwa.
Ya ce abu ne mai sauki mace ta rasa ranta sakamakon kamuwa da cutukan da ke tattare da yin kaciyar.
Mai ya kamata jama’a su sani
Dakta Ggwuda ya ce duk da cewa a yanzu matsalar ta ragu a birnin sai dai kauyuka, akwai bukatar a ci gaba da wayar da kan jama’a har a kawo karshen matsalar.
A cewarsa ko kadan kaciyar mata bata haifar musu da da mai ido ta kowacce fuska.
Haza zalika ya ce yiwa mata kaciya bashi da wata fa’ida ta bangaren lafiya face jefa lafiyar tasu cikin matsala.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
Hausa
Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.
Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.
Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.
Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.
Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.
“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.
“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”
Hausa
Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote
Nasiru Yusuf Ibrahim
Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.
Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .
Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.
“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.
Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun da basu samu damar biya ba a baya.”
Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari, gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.
“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al’umma.” Dangote.
Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.
“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”
Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada rade-radi da jita-jita.