KANUN LABARAI
Hisba ta kama matasa uku a Kano da ta ce sun kulla mata sharri
Amniu Abdullahi
Hukumar Hisba ta cafke wasu mutane uku da ta ce sun yi mata kazafin kone shaguna a kasuwar Badume, ya yin da ta kai sumamen hadin gwiwa da hukumar NDLEA a makon jiya.
Kano Focus ta ruwaito wadanda hukumar ta kama sun hada da Gambo Babangida da Isma’il Ahmad da kuma Abubakar Kanabaro.
Wadanda ake zargin dai sunyi rubutu a shafukan su na Facebook inda suka ce hukumar ta kone musu shaguna ya yin da taje kamen masu aikata badala da ta’amali da miyagun kwayoyi.
Saidai sun lashe aman su bayan da hukumar ta kama su tare da karyata rubutun da sukayi.
Gambo Babangida ya ce tabbas ya janye kalaman sa domin kuwa yasan cewa masu aikin Allah ba za su aikata abinda ya fada ba.
“Nayi kuskure a rayuwa ta da ban taba yi ba, nafi shekara hamsin da bakwai tabbas harshe na ne ya jawomin kuma bazan kara ba,” a cewar sa.
Isma’il Ahmad cewa ya yi maganganun da yaji mutane sunayine ya kaishi ga aikata haka kuma ba tare da yayi bincike ba.
Ya kara da cewa ya yi nadama daga baya don kuwa ba a kone masa shagon sa ba.
Shima Abubakar Kanabaro cewa ya yi jita-jita ce tayi tasiri akan sa har takai ga ya dora a shafin facebook.
“Nima nayi na dama don har ga Allah nagano basu da hannu a cikin abinda ya faru,” a cewar sa.
Ya kara da cewa a shirye suke da a dauke su aikin hukumar Hisbah don kawar da badala da kuma jaddada ayyukan alkairi a tsakanin al’umma.
“Zamu taimakawa Hisbah wajen bincike gurbatattun abubuwan dake faruwa a kasuwar,” a cewar sa.
Da yake nasa jawabin babban kwamandan Hisbah Muhammad Harun Sani Ibn Sina ya ce sun bi diddigin wadanda suka yada labarin na karya ta shafin facebook tare da kamasu.
Ya ce bayan da aka kamasu ne kuma sai suka karya ta kansu.
Ibn Sina ya ce tunda har sun tuba kuma sun amsa laifin su to hukumar za ta yi musu afuwa kamar yadda ta saba.
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
Hausa
Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.
Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.
Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.
Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.
Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.
“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.
“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”