Connect with us

KANUN LABARAI

Muhimman abubuwan da suka faru a Kano cikin shekarar da muke bankwana da ita

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

A yayin da muke bankwana da shekarar 2020 Kano Focus ta yi nazari kan muhimman abubuwan da suka faru a jihar Kano da al’umma ba za su mace da shi ba.

Shekarar 2020 shekara ce da ta zo da sammatsi iri-iri da suka dagula lissafin al’umma da tabbas jama’a za su dade suna tuna ta.

Zuwan baturiya Kano

Janine Sanchez Weds Sulaiman Isa Isa

A cikin watan Janairun shekarar da muke bankwana da ita ne wata baturiya mai suna Janine Sanchez ta zo Kano domin auren wani matasi dan asalin unguwar Panshekara da ke nan Kano.

Zuwan baturiyar dai ya jawo ce-ce kuce a tsakanin al’umma, inda wasu ke ganin sa ce ta zo yi, yayinda wasu ke ganin wata bukata ce da ita akan sa ya sanya ta biyo shi.

Haka zalika wasu ba’arin al’umma na ganin cewa kwadayi ne irin na Sulaiman ya sanya shi soyayya da baturi.

To koma dai mene yanzu haka an dauran auren Sulaiman da baturiya kuma sun koma kasar Amurka.

Bude kotun daukaka kara a Kano

A rananr 11 ga watan Fabrairun shekarar da muke bankwana da ita ne aka bude kotun daukaka kara a Kano.

Shugabar kotun daukaka kara ta kasa Zainab Bulkacuwa ce ta jagoranci bude kotun domin saukaka al’amuran shari’a a kasa.

Haka zalika bayan da aka bude kotun an turo mai shari’a Abubakar Datti Yahya a matsayin alkalin kotun, yayin da mai shari’a Habib Adewale da kuma A.A Wambai za su dafa masa.

Idan za a iya tunawa kafin bude kotun, sai anje Kaduna ko wata jihar kafin a daukaka kara akan dukkan wata shari’a, amma da aka bude kotun an samu sauki kan wannan.

Tube Sarki Sunusi

A ranar 9 ga watan Maris din shekarar da muka yi bankwana da ita ne gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tunbuke Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II.

Gwamnan ya ce ya dauki matakin tunbuke Sarkinne bayan da ya samu amincewar dukkanin ‘yan majalisar Zartaswarsa.

Haka zalika ya ce ya tunbuke sarkinne domin a kare mutunci da al’ada da kuma addini da ya yi zargin sarkin na watangaririya dasu.

Aminu Ado ya zama sarki

A dai wannan rana da aka cire Sunusi ne kuma aka sanar da Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano.

Anjiyo sakataren gwamnatin jiha Alhaji Usman Alhaji na cewa an zabi Aminu Ado a matsayin sabon Sarkinne domin cancantarsa da kwarewarsa akan sha’anin mulki.

Kafin nada shi Sarkin Kano shi ne Sarkin Bichi na farko a tarihi tun da aka kafa masarautar.

Idan za a iya tunawa Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya kirkiri sabbin masarauti hudu baya ga ta Kano inda ko wacce ya yi mata sabon sarki.

Bullar Korona a Kano

A rananr 11 ga watan Afrilun shekarar 2020 ne aka fara samun bullar cutar kwarona a Kano.

Rahotanni sun ce wanda aka fara samu din ya shigo jihar  Kano ne daga Birnin tarayya Abuja.

Haka kuma bayan an gwadashi ne aka killace shi a inda aka tanada domin killace masu dauke da ita a asibitin Kwanar Dawaki.

Kuma tun da ga wannan lokacine aka ci gaba da samun bullar cutar har zuwa wannan lokaci.

Buhari ya kulle Kano

A ranar 27 ga watan Afrilun shekarar da muka yi bankwana da ita ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya dokar kulle a jihar Kano ta sati biyu saboda bullar cutar Covid-a19 a Kasa.

Shugaban kasar ya ayyana dokarne lokacin da yake bayani ga al’ummar kasa kan halin da ake ciki dangane da cutar Covid-19.

Ya kuma bukaci al’umma da su zauna a gida ba shiga ba fita ba mu’amala da juna tsahon wadannan kwanaki.

Mace-macen Kano

A watan Afrilun shekarar bara ne dai aka dinga samu yawaitar mace-mace a Kano da aka kasa gane dalilinsu.

Sai dai wani likita a nan Kano Isa Abubakar ya ce mace-mace na afkuwa ne saboda dalilai guda uku.

Na daya zai iya kasancewa masu dauke da cutar Korona ne da ba a gwada an tabbatar da su ba.

Na biyu akwai mutane masu bukatar kulawar gaggawa ta likita amma saboda bullar Korona anyi watsi dasu.

Sai na uku ya ce marasa lafiya da yawa na kasa zuwa asibiti saboda kulle, suma kuma asibitocin basa karbarsu.

Soke bukukuwan salla

A ranar 18 ga Mayun shekarar bara ne gwamnatin Kano ta ce ta suke dukkanin shagulgulan Sallah sakamako bullar annobar Korona.

Ko da ya ke gwamnati ta bada kofa aje masallacin idi a yi salla amma da sharadai masu tarin yawa.

Karo biyu ke nan a wanna shekara ana hana bukukuwan salla, da ya hadar da  na sallah karama da kuma babbar sallah

Mutuwar Umar Sa’idu Tudun Wada

A ranar 30 ga wantan Yuni ne fitaccen dan jaridar nan na Kano Umar Sa’idu Tudun Wada ya rasu sakamakon hadarin mota.

A cewar makusacin sa Umar Sa’idu Tudun Wada ya yi hasashen mutuwasa  mako guda kafin ya rasu.

A cewarsa hakan ce ta sanya yayi ta aikata abubuwan alheri daf da rasuwar tasa domin neman kusanci ga Allah ta’ala.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending