Connect with us

KANUN LABARAI

Kishiya ta babbaka kishiyar ta a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wata kishiya ta yiwa uwar gidanta da ‘yar ta mai shekaru uku wanka da tafashasshen ruwan zafi a unguwar Sheka Sabuwar Abuja dake karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Kano Focus ta ruwaito cewa wacce ake zargin Hauwa’u Auwal mai shekaru 30 ta kwarawa abokiyar zamanta mai suna Sha’awa Muhammad ruwan zafinne bayan da suka samu sabani a ranar juma’ar data gabata.

Sha’awa Muhammad ta ce kishiyarta ta zargi ‘yar ta mai suna Aisha da yi mata fitsari a ruwan wanka data kai ban daki.

“Da ta shiga bandaki sai ta fito tace yarinya ta tayi mata  fitsari a cikin ruwan wanka kuma na tambayi ‘yar tawa ta ce min ita bata yi mata komai ba.

“Lokacin da ta ce anyi mata fitsarin ni ban yi mata magana ba mijina na fadawa kuma na ce idan har tace anyi matan to tayi hakuri,” a cewar ta.

Ta kara da cewa tana zaune a kofar daki tare da ‘yarta kawai sai ji tayi ta kwara mata ruwan zafi wanda ya sabule mata jiki tare da yarinyar ta.

“An kwantar da mu a asibiti guda daya nida ‘yar tawa amma daki daban daban.

Da aka kawomin ‘yar tawa saida ta tsorata saboda kasa ganeni da tayi sakamakon konuwar dake fuska ta da jiki na.

“Wallahi bana iya kwanciya, bacci ma baya yiwuwa, ina rokon abi min hakkina akan abinda ta aikatamin, kuma da rana abin ya faru ba da daddare ba” a cewar Sha’awa Idris.

A nata bangaren wacce ake zargi Hauwa’u Auwal dake dauke da juna biyu  ta ce an sha zuba mata abubuwa a cikin ruwa idan ta ajiye.

Ta kara da cewa abokiyar zaman nata tana da son fitina hakan tasa take yawan takalarta fada a koda yaushe, amma mijin su baya daukar wani mataki.

Ta kuma ce bada sanin ta takwara musu ruwan zafinba, don kuwa ta dauko ruwan ne zuwa bandaki domin ta wanke kanta a nan ne ya zube daga hannunta inda ya kona su a cewar ta.

“Nan take da abun ya faru ya sakeni saki uku saboda lokacin yana daki su kuma suna Kofar daki.

“Gaskiya nayi nadamar abinda ya faru wallahi da nasan hakane bama zanyi magana akan ruwan ba,” a cewar Hauwa’u.

A nata bangaren rundunar “yan sandan jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin.

Mai magana da yawun rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an mika wadanda abin ya shafa zuwa asibiti.

Ya kuma ce wacce ake zargin ta shiga  hannun su kuma da zarar an kammala bincike zasu gurfanar da ita a gaban kotu.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending