Connect with us

Hausa

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Inganta tsaro: Alfindiki ya samar da kofofin unguwannin masu kudi a cikin lokuna

Published

on

Aminu Abdullahi

Shugaban karamar hukumar Birni Fa’izu Alfindiki ya samar da wasu kofofi a lokuna da sakuna na wasu unguwanni a karamar hukumar Birni domin inganta tsaro.

A wani kewaye da Kano Focus ta gudanar, ta gano yadda aka samar da kofofin a unguwar Alfindiki, da Kwanar Goda, domin kulle lokunan idan dare yayi.

Wannan dai shi ne karo na farko da aka fara ganin irin wadannan kofofi na killace unguwanni a cikin birni, da galibin lokuta ana ganin irinsu ne kawai a unguwannin masu kudi.

A zantawar Kano Focus da wasu daga cikin mazauna unguwannin, su nuna jin dadin u da aikin da a ke yi musu, a cewarsu ko ba komai za a kara inganta tsaron yankin nasu.

Usman Balarabe mazaunin Alfinidiki ya ce a baya ba a saba ganin irin wadannan kofofi ba a unguwannin talakawa ko cikin birni.

Ya kara da cewa mafi a kasari layukan da ke unguwannin masu kudi ne ke samar da irin wadannan kofofi, tare da kullesu idan dare yayi.

“Wannan tsari ya yi sosai domin zai inganta tsaro a unguwanninmu, musamman a wannan lokaci da barayi kan haura gidajen al’umma da tsakar dare.

“Sannan kaga kowanne loko akwai wadanda aka dorawa alhakin rufe kofofinsa da zarar sha biyu na dare tayi,” a cewar sa.

Shima Musa Ibrahim mazaunin Kwanar Goda ya ce bai taba tunanin unguwanni irin nasu masu ginin kasa za su samu irin wannan cigabanba duba da cewa anfi samunsu a unguwannin masu hali.

“Daga lokacin da aka sanya mana wadannan kofofi ji nake tamkar muma ‘yan kasar waje ne,” a cewar sa.

Sai dai Bashir Muhammad Hassan ya ce samar da kofofin na da amfani, sai dai za su iya haddasa rikici a tsakanin makota.

Ya ce wasu magidanta basa komawa gidajensu da wuri sai bayan karfe goma sha biyu na dare.

“Idan kadawo katarar da kofar shiga lokon da gidan ka yake a rufe, kaga ai akwai matsala, kuma zaka iya kiran wayar wadanda mukullin gurin ke hannunsu a kashe.

“Ni ina ganin idan har kullewar ya zama dole to kowanne magidanci a bashi mukulli, ta yadda komin dare idan ya dawo zai iya budewa ya shiga,” a cewar sa.

Continue Reading

Hausa

Daliban Kano sama da 20,000 ba za su shiga manyan makarantu ba

Published

on

Aminu Abdullahi

Daliban sakandiren fasaha a jihar Kano 10,691 da kuma na bangaren Arabiyya 13,210 ne ba za su samu shiga manyan makarantu a bana ba.

Wannan ya biyo bayan rashin fitar sakamakon jarrabawar kammala sakandire da suka rubuta tun a bara.

Kano Focus ta ruwaito cewa kimanin watanni bakwai kenan da daliban suka rubuta jarabawar, sai dai sun gaza samun sakamakon saboda kin biyan kudin jarrabawar da gwamnati tayi.

Idan za a iya tunawa dai anyi ta kai ruwa rana da gwamnatin jihar Kano kafin ta biya wani ba’ari na kudin jarrabawar dalibai ta NECO.

Wannanne ma ya sanya daliban da suka dauki jarrabawar (NABTEB) da kuma ta (NBAIS) a jihar Kano ke ganin su kam ci gaba da karatu a bana sai dai su ji ana yi.

Yajin aikin malaman jami’o’i baraza ne ga ilimi a arewacin kasar nan-Danmaje

Matasan Arewa ne koma baya a bangaren fasahar sadarwa-Kungiya

Da gan-gan gwamnati ta ki biyan kudin NECO-Iyayen yara

Rilwanu Sulaiman dalibin Arabiyyana ne da ya rubuta jarrabawar, ya ce watanni shida kenan da kammalawa, amma har yanzu ya gaza samun sakamakon sa.

Ya ce da yawa daga cikinsu ba za su samu gurbin karatu a jami’o’in da suka nema ba, sakamakon rashin sakin sakamakon.

“Muma ‘yan jihar Kano ne muna kira ga mai girma gwamna da ya taimaka a sakar mana sakamakonmu ko ma cigaba da karatu”

“Sai da muka biya kudin rijista sannan muka rubuta jarabawar duk da cewa gwamnati na ikirarin ilimi kyauta ne,” inji shi.

Ya ce rike sakamakon nasu tamkar hana su cigaba da karatune, kasancewar da yawansu, iya jarrabawar kawai suka rubuta.

Shima Auwalu Ibrahim dalibin da ya rubuta jarrabawar ta NBAIS ya ce rashin karbar sakamakon na su yasa ya yanke shawarar rubuta jarabawar (WAEC) wadda itama aka ce ba za a yi a wannan shekarar ba.

“Bamu da yadda zamuyi, amma muna fata gwamnati za ta duba halin da muke ciki, tare da sakar mana sakamakon jarabawar mu,” injishi.

To ko me gwamantin jihar Kano ke yi gamme da rashin fitowar sakamakon jarabawar daliban?

Aliyu Yusuf shi ne jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ya ce bashin da hukumomi ke bin gwamnati ne ya sanya aka gaza sakin sakamakon.

Aliyu Yusuf wanda ya yi magana a madadin kwamishinan Ilimi na jihar Kano Muhammad Sunusi Kiru ya ce da zarar gwamnati ta biya kudaden za a saki sakamakon.

Ko da dai Aliyu ya gaza yin cikakken bayani kamar yadda jama’a za su fuskanta, amma dai ya bayyana tsananin bashin da ake bin gwamnati ne yasa aka kasa fanso jarrabawar.

Continue Reading

Hausa

‘Yan sanda a Kano sun kama makocin da ya jagoranci yiwa makocinsa fashi

Published

on

Aminu Abdullahi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi Sa’id Abubakar da ya jagoranci mutane uku wajen yiwa makocinsa Nasiru Sulaiman fashi a Unguwar Maidile dake karamar hukumar Kumbotso a nan Kano.

Kano Focus ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan ranar Juma’a a nan Kano.

Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce tun a ranar 29 ga watan da ya gabata ne suka sami rahoto daga wanda aka yiwa fashin.

Ya ce sun shiga gidansa ne da misalin karfe 1:30 zuwa biyu na dare inda suka yi amfani da bindiga wajen yi masa fashi.

Ganduje ba zai iya biyan cikakken albashin watan Maris ba-Kwamishina

An sace mutane 12 ‘yan Kano a Kaduna

Kotu a Kano ta aike da ‘yan sanda biyu gidan yari

Kiyawa ya ce wadanda aka kama sun hadar da Sulaiman Ja’afar wanda shi ne makocin daya jagoranci yin fashin.

Sai kuma abokan aikin sa da suka hadar da Sai’du Abubakar mazaunin Gaida, da Adamu Ya’u Muhammad dake unguwar Sharada sai Isyaku Mudi dan asalin jihar Kebbi dake zaune a unguwar Hotoro.

Haka zalika Kiyawa ya ce  ‘yan fashin sun kwace masa kudade da agogo da kuma motar sa kirar Ford inda aka samota a Zamfara ana shirin sayar da ita.

Ya ce bayan da suka samu rahoton ne kuma suka baza jami’an su inda suka samu nasarar kama su.

Da yake shaida yadda aka yi masa fashin Nasiru Sulaiman ya ce sun balle kofar gidan sa ne bayan da yaki budewa suka kuma tsira shi  da bindiga.

“Sanda suka shigo na shiga tashin hankali sosai.

“Sun nemi dana basu kudi,  suka kuma dauki mota ta da sauran kayayyaki,” a cewar sa.

Shima matashin da ya jagoranci fashin Sulaiman Ja’afar ya ce shi ya jagoranci abokan nasa uku zuwa yin fashin.

“Munje gidan sa da daddare mu biyar da bindiga da wukake.

“Ni ban tabayi ba wannan shi ne karo na farko amma su ragowar dama suna yi,” a cewar sa.

Continue Reading

Trending