Connect with us

Hausa

Ba za mu janye daga tuhumar Aduljabbar ba- Malaman Kano

Published

on

Malaman Kano

Mukhtar Yahya Usman

Gamayyar Malam Kano da suka hadar da ‘yan Izala da na Tijjaniyya da kuma Kadiriyya sun ce suna nan kan bakansu,  ba za su janye daga tuhumar Abduljabbar Kabara ba.

Kano Focus ta ruwaito gamayyar malaman sun cimma wannan matsaya ne ya yin zaman gaggawa da suka gudanar a masallacin Usman bn Affan da ke kofar Gadon Kaya  da yammacin ranar Asabar.

Malaman da suka gudanar da zaman sun fito ne daga dukkanin bangarorin akida da ke jihar nan, da suka hadar da Izala da Qadiriyya da kuma Tijjaniyya.

Da yake jawabi a madadin malaman Dakta Muslim Ibrahim wanda shi ne shugaban zaman ya ce ko kadan ba za su janye shirinsu na tuhumar Abduljabbar ba.

Ya ce tunda kotu ta dakatar da zaman, kuma gwamnatin Kano ta karba, to za su jira lokacin da kotun za ta bada dama a gudanar da mukabalar.

A cewarsa basu ji dadin matakin da kotun ta daukaba, amma za su yi biyayya ga umarnin kotun har zuwa ranar 22 ga Maris da kotun ta sanya domin ci gaba da sauraron karar.

Ba zan taimakawa Abduljabbar ya yi suna ba -Sarkin Musulmi

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Masoyana ku janye karar da kuka kai Ganduje-Abduljabbar Kabara

Dakta Muslim ya kuma yi kira ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kada ya janye kudirinsa na mukabalar, a cewarsa ta haka ne za a tsamo jama’a daga halaka.

“Muna cikin shirin ko ta kwana na zaman tuhuma.

“Muna jiran kotu ta baiwa gwamnati damar ci gaba da wannan shiri nata

“Muna tabbatarwa da kowa babu komai cikin wannan tuhuma fa ce alkhairi, don warware duk wata shubuha, ya taimakawa mutane fitda daga duhun bata da zandiganci.

“Muna tabbatarwa da gwamnati da duk wani mai fatan alheri ga al’umma cewa mu masu biyayya ne ga duk wani tsari da zai wanzar da zaman lafiya da ci gaban al’ummar Manzon Allah

Ba musan manufar lauyaba

Haka zalika malaman sun nuna bacin ransu ga lauyan da ya shigar da karar ya nemi a dakatar da zaman.

A cewar Dakata Muslim basu san manufar lauyan na shigar da karar ba kuma basu san wa ya dauki nauyinsa ba.

a cewarsu sai da ya dubi ranar juma’a daf da za a yi zaman sannan ya yi karar da ta ruguza komai.

A don hakan ne suka kirashi da ya ji tsoron Allah ya sani zai tsaya gaban Allah ya kuma amsa tambayar abinda ya aikta.

Hausa

Mahaya dawaki sun kashe mutune 2 a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wasu magidanta biyu ‘yan gida daya sun rasu sakamakon banke su da mahaya Dawaki su ka yi yayin da suka bisa babur a titin  Sokoto Road da ke Kano.

Kano Focus ta ruwaito cewa ranar Asabar ne mahaya Dawakin suka kashe Inuwa Sani da Abdulrahaman Sani ‘yan unguwar Yakasai a Birnin Kano.

Mahaifiyar su, Rukayya Ali ta ce an kashe ‘ya’yan na ta ne akan hanyar su ta zuwa gaishe ta.

Ta ce kowanne daga cikin marigayan  ya mutu ya bar mata daya  daya ‘yaya shida.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta Abdullahi Haruna Kiyawa.

Ya ce suna zargin wani matashi Sadiq Adamu, 22, da abokansa bakwai ne suka shirya hawan Dawakin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen.

Ya ce sun kama biyu daga cikin wadanda ake zargi kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su gaban kotu.

Masarautar Kano dai ta haramta hawan Dawaki a cikin birinin Kano sakamakon jikkatawa ko hallaka jama’a da mahayan ke yi.

Continue Reading

Hausa

Kishi: Mata a Kano ta hana a yiwa mijinta jana’iza a gidansa

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Tsananin kishi ya sanya wata mata Jamila Muhammad hana shigar da gawar mijinta cikin gidansa domin yimasa jana’iza bayan rasuwarsa.

KANO FOCUS ta ruwaito al’amarin ya faru ne ranar Litinin a unguwar Gwazaye da ke yankin Dorayi a karamar hukumar Gwale, da ke nan Kano.

Abdullahi Mustapha guda ne daga cikin wadanda suka sheda al’amarin ya shaidawa shirin ‘yan zazu na gidan rediyon Dala cewar tsananin kishi ne ya hana matar amincewa a ajiye shi a gidanta.

Ya ce matar na zaune ne a gidan mijin bayan da kotu ta raba aurensu ta kuma umarceshi da ya bata dama ta ci gaba da zama a gidan saboda yara.

Ya kara da cewa matar ta nemi su rabu da mijin ne don kawai ya auri wata matar.

Sai dai bayan auren sabuwar matar ne kuma auren ya rabu, haka kuma gidan ya koma hannunta.

Mustapha ya ce bacin rai da takaicin matar ne ya haifarwa mijin ciwon zuciya har ya mutu.

Bayan mutuwar tasa ne kuma aka daukoshi daga asibiti aka kuma kaishi gidan da matar take amma fafur ta ce ba za a yi masa sutura a gidan ba.

A cewar Mustapha ba irin bakin da ba a baiwa Jamila ba, amma ta ce sai dai a kaishin gun amarya a yi masa jana’iza.

Hakan ta sanya wani dattijo a unguwar ya bada damar a shigar dashi gidansa domin yi masa jana’iza.

Tuni dai yan uwan Jamila suka dauke ta zuwa garinsu da ke Gezawa domin gudun abinda zai faru.

Continue Reading

Hausa

Hisbah ta nemi taimakon Saudiyya kan dakarunta

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta nemi taimakon kasar Sadiyya da ta tallafa mata wajen horar da jami’anta akan sha’anin aikinsu.

Kano Focus ta ruwaito babban Kwamandan Hisbah, Muhammad Harun Sani Ibn Sina ne ya yi rokon a ofishinsa ranar Lahadi.

Wanan na zuwa ne bayan da hukumar ta karbi bakuncin daya daga cikin limaman Masallacin Harami na Makkah Farfesa Alhassan Bin Abdulhameed Albukhary tare da ayarinsa.

Ayarin Limanin sun ziyarci Kano ne bisa gayyatar Jami’ar Bayero don horarwa ta musamman ga alkalai da daliban ilimi wanda wannan ita ce horarwa irinta ta hudu da suka yi a kasar nan.

Hisbah ta kama matar da ta yi safarar jariri daga Delta zuwa Kano

Ramadan:Hisbah ta kama Gandaye 11 a Kano

Shigar mata: Hisba ta kama wani saurayi da ya rikide zuwa Amina a Kano

“Babban kalubalenmu shi ne rashin wurin da za mu horar da jami’anmu domin su kara samun horo a kan ayyukansu.

“Zai yi kyau idan har za mu samu tallafi daga Hukumar Kasar Saudiyya mai albarka wajen samar mana da wuri ko kuma makarantun da jami’anmu za su dinga samun horo ko da kuwa a kasar Saudiyya din ne.” cewar Ibn Sina

A nasa Jawabin Imam Albukhariy ya yaba wa hukumar Hisbah akan ayyukan da take gudanarwa a fadin jihar nan, inda ya nemi su rubanya kokarinsu akan ayyukansu.

“Shi aikin umarni da aikin alheri da hani da mummuna abu ne babba a harkar zamantakewar al’umma.

“Wasu malamai suna cewa da za a kara wani abu a kan rukunan Musulunci to da abin da za a kara ba zai wuce umarni da aikin alheri da hani da mummuna ba saboda muhimmancinsa a Musulunci.

“Don haka ’yan Hisbah ku sani aikin Allah kuke yi.”

Farfesa Albukhari wanda shi ne Shugaban Sashen Larabci na Jami’ar UmmulQura da ke garin Makkah ya bayyana cewa, Hukumar Kasar Saudiyya za ta taimakawa hukumar Hisbah da duk irin abin da take bukata, matukar dai bai ci karo da tsarin mulkin kasar ta Saudiyya ba.

Continue Reading

Trending