Connect with us

Hausa

Cin zarafin mai babur: KAROTA za ta hukunta jami’anta

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar KAROTA ta ce za ta hukunta jami’anta da aka gano a wani faifan bidiyo na cin zarafin wani mai babur  bisa zargin  karya dokar tuki.

Kano Focus ta ruwaito wanan na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar ranar Laraba a nan Kano.

A wani faifan bidiyo da ya karade gari an ga wani  jami’in KAROTA ya shake wani matashi a cikin mota, yayin da matashin ke kokarin kwatar kansa.

Haka kuma anji jami’in KAROTA na ta surfawa matashn ashariya.

daga wajen motar kuma aba hango wasu jami’an na KAROTA a kewaye da su

Sanarwar ta ce shugaban hukumar Baffa Babba Dan Agundi ya bada umarnin a fadada bincike domin gano musabbabin al’amarin , tare daukar matakin da ya da ce.

Ya ce za a hukunta duk jami’in da aka samu da nuna rashin kwarewa a wurin aiki.

Ya kuma bukaci jama’a da su dinga basu haɗin kai domin ci gaba da gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Hausa

Ba a nada Sarkin Sharifai na kasa idan ba daga Kano ya ke ba – Zuri’ar Almaghili

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Masarautar sharifai ta kasa da ke da shalkwatarta a Kano ta koka kan yadda wasu da ke kiran kansu sharifai suke amfanin da sunan wajen barace-barace da neman mulki.

Babban wakilin masarautar Sharifai ta kasa karkashin zuri’ar Sheikh Salihu Almagili Sharif Abdulkarim Sahrif Ali ne ya yi wannan korafi yayin taron maneman labarai a Kano.

Sharif Abdulkarim ya ce abin takaici ne a samu wasu na kokarin cusa kansu cikin shugabancin sahrifai na kasa bayan ba su gada ba, har ma su yi ikirarin cewar su ke jan ragamar sharfai a kasar nan.

Ya kara da cewa shekara da shekaru zuri’ar Sheikh Salihu Almaghili  ke jagorancin Sharifai a kasar nan kuma tun wancan lokaci har yanzu ba a sauyaba.

Sai dai wani abu da ya ja hankalinsu shi ne yadda suka ji wani mutum ya fito daga jihar Zamfara da ke ikiran shi ne sarkin Sharifai na kasa.

A cewarsa wannan ya saba ka’idar yadda ake nada shugabancin sharifai a kasar nan.

Sharif Abdulkarim ya kara da cewa wanda ke ikirarin kansa sarkin sharifai na kasa na yin amfani da damar kasancewarsa Sharifi ne kawai yana damfarar al’umma.

Har ma aka jiyo shi ya ziyarci gwamnan Zamfara ya kuma nada shi garkuwan sharifan, da a cewarsa wannan duk wani salo ne na damfara.

Ba a sarkin sharifai ba a zuri’ar Almaghili ba.

Sharu Abdulkarin ya ce a yadda aka san sarautar Sharifai dole ne arkin sharifa ya zama ya fito da ga tsatson Almagili, haka kuma fadar sarkin sahrifai na kasa ta kasance a unguwar sharifai Zauren Tudu da ke nan Kano.

Amma saboda son abin duniya da kuma kawo wargi cikin al’amarin ya sanya wasu ke ikirarin sarautar Sharifai, su ke kuma tafiya neman kudi da ita.

A don hakan ne ya ja hankalin jama’a da masu madafun iko su dinga tantance suwaye sharifai na gaskiya da kuma na bogi.

Masu madafan iko su dinga tantancewa kafin hukunci

 Sahrifin ya ci ga ba da cewa akwai bukatar masu mukamai da ake zuwa musu da irin wannan damfara su dinga bin diddigin duk mutumin da ya zo musu da sunan sarautar sharifa.

A cewarsa galibin masu zuwa wurinsu da sunan sarautar sharifai na zuwa ne kawai domin neman na abinci.

Ya kuma ce tuni suka fara bin diddigin inda matsalar ta samo asali har wani daga jihar Zamfara ya ke kiran kansa da sarkin sharifai, kuma za su dauki matakin gaggawa.

Continue Reading

Hausa

Mutum dubu 43 ne za su sauke farali daga Najeriya-Saudiyya

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Hukumomin a kasar saudiyya sun baiwa kasar nan adadin mutun 43,000 da za su sauke farali a bana.

Babban sakataren hukumar Jin dadin alhazai na Kano Muhammad Abba Danbatta ne ya sanar da hakan yayin taron manema Labarai ranar Laraba.

Danbatta ya ce wannan ya biyo bayan yadda kasar ta Saudiyya ta ce adadin mutun Milyan daya ne kawai za su gudanar da aikin hajjin bana a fadin duniya.

Ya ce wannan adadi da aka baiwa Najeria na da alaka da yawan mutanen da Najeria ta ke da shi.

Muhammad Danbatta ya ce ko dayake har yanzu NAHCON bata fitar da kudin aikin hajjin bana ba Amma alamu na nuna kudin zai karu.

Ya ce a baya an canja Dala akan 350 yanzu kuma ta Kai 408 da ke nuna lallai za a samu Karin kudin.

A yanzu dai ana jihar hukumar Jin dadin alhazai ta kasa ta baiwa kowacce jiha adadin kujerunta tare da bayyana adadin kudin na bana.

Continue Reading

Hausa

Ta hanyar ‘Interfaith Dialogue’ ne Shari’ah ta tabbata a ‘Constitution’ din Nigeria

Published

on

 

 

Prof. Salisu Shehu

 

 

Na ga ‘yan uwana almajirai, a dalilin rashin fahimtar turanci da kuma rashin sanin cikakken tarihin Nigeria, har cewa suke wai Interfaith Dialogue kafirci ne. Duk da Malamanmu kamar Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo da Professor Mansur Sokoto sun yi bayani cewa akwai banbanci tsakanin Interfaith Dialogue (Hiwarul Adyan) da Unification of Religions (Wahdatul Adyan), amma na lura da yawa sun kasa fahimtar wannan banbanci. Suna hakikancewa wai Interfaith shi ne “shigar addini cikin wani addini”.

Wanda duk ya ce wai Interfaith Dialogue ba shi da wani amfani ga Musulmi, to sai mu ce masa watakila yana da nakasu/gibi a saninsa ga tarihin Nigeria.

Sai da aka yi zazzafar muhawara tsakanin Musulmi da Kirista a Constitutional Assemly a shekarar 1978, har kamar za a yi kutufo tsakanin juna tsakanin Musulmai da Kafirai a kan Shari’ah kafin aka tabbatar da Shari’ah a Constitution din Nigeria. Tsayuwar daka da Musulmai suka yi babu tsoro, da kuma nuna babu gudu, babu ja da baya da kuma kwararan hujjoji da Musulmai suka gabatar akan cewa idan ana son zaman Nigeria a matsayin kasa daya dunkulalliya dole a tabbatar da Shari’ah ga Musulmai a cikin Constitution din Nigeria. Da wannan ne Allah Ya taimaka suka yi galaba akan Kiristoci aka tabbatar da Shari’ah a 1979 Constitution.

A dalilin tabbatar da Shari’ah a 1979 Constitution ne Allah Ya taimaka da aka zo bitar Constitution a Shekarar 1999 Shari’ah ta kara tabbata daram, daram dam dam daram. Amma shi ma sai da aka kai ruwa rana a muhawara tsakanin Musulmai da Kiristoci a National Constitutional Conference na 1995/1996.

Wannan tabbatuwar Shari’ah a Constitution din Nigeria ta hanyar muhawara tsakanin Musulmai da kafirai shi ne ya zamanto Babbar majingina ko madogara da Excellency Ahmad Sani Yariman Bakura lokacin da ya kuduri aniyar fadada Shari’ah a shekarar 2000. Kuma a videon da ya yi ta yawo kwanan nan an ji yanda aka yi muhawara da Shugaban Kasa na wannan lokacin Obasanjo da sauran kiristoci akan Shari’ah. Dole suka hakura saboda kokarin da Musulmai suka yi a baya wajen tabbatar da ita a Constitution din Nigeria.

Kuma bayan fadada Shari’ah a Jihar Zamfara da sauran jihohin Arewa kafirai sun ci gaba da yakarta ta kafafe daban – daban. { یُرِیدُونَ أَن یُطۡفِـُٔوا۟ نُورَ ٱللَّهِ بِأَفۡوَ ٰ⁠هِهِمۡ وَیَأۡبَى ٱللَّهُ إِلَّاۤ أَن یُتِمَّ نُورَهُۥ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡكَـٰفِرُونَ }

[سُورَةُ التَّوۡبَةِ: ٣٢]

Allah Shi ne shaida a kan fafatawar da muka rinka yi a dandaloli na Interfaith Dialogue musamman a tsakanin Abuja da Kaduna da Jos da sauran wurare wajen muhawara da kiristoci a kan Shari’ah, musamman Hisbah da dai sauransu.

Idan wannan shi ne kafirci kamar yadda akasarin masu wa’azi suke fada, to ina kiransu da su fadada tinani, su zurfafa bincike a kan ma’anar Interfaith Dialogue da kuma abubuwan da ta kunsa.

Hakika abun da ya wajaba akan mu Musulmai shi ne mu yi ta’asilin manufofinmu, da ka’idodinmu, da matakanmu, da fuskoki da fajjojinmu na yin muhawara da kafirai a bisa koyarwar Al-Qur’ani da Sunnah kamar yanda Professor Mansur da Professor Dogarawa suka yi kokarin tabbatarwa a bayanansu da rubuce-rubcensu. Sa’annan kuma mu tsaya mu yi kyakkyawan tsari wajen tabbatar da cewa ba kowane Musulmi ne zai je ya shiga Interfaith Dialogue ba sai wanda yake da Ilimin Musulunci mai zurfi. Akalla a tabbatar yana da ahliyya ta zazzago nassoshin Qur’ani da Sunnah ba tare da lahani ko rudani ba. Kuskure ne namu gaba daya da muka bar mutanen da suke “wala yakadu yubin” a Qur’ani suna zuwa suna wakiltarmu a fagagen Interfaith Dialogue.

Wallahi, a Kasa irin Nigeria inda ake da al’ummai mabanbanta addinai, akidu da kabilu, da al’adu ba karamin kuskure bane a ce wai kada Musulmai su yi muhawara ta addini da kafirai.

Misalai na yadda muhawara tsakanin Musulmai da kafirai suka tabbatar ma Musulmai nasarori a kan addini da rayuwa suna da yawa. Daga ciki akwai canja suturar mata Nurses Musulmai. Duk dan shekara 50 ya san yadda Nurses Musulmai suke fita tsirara. Amma muhawara da karfn hujjar Musulmai suka sa yau gashi nurses dinmu Musulmai suna sanya Hijabi. Wannan ya taimaka wajen kwadaitar da iyaye su rika barin ‘ya’ yansu Musulmai su karanci fanning Nursing.

Ni dai na lura da yawa daga cikin wadanda suka yi kuskuren cakuda Interfaith Dialogue (Hiwarul Adyan) da kuma Unification of Religions (Wahdatul Adyan) basu yi mura’atin ayar nan ta Suratul Isra’i ba:

{ وَلَا تَقۡفُ مَا لَیۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۚ إِنَّ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡبَصَرَ وَٱلۡفُؤَادَ كُلُّ أُو۟لَـٰۤىِٕكَ كَانَ عَنۡهُ مَسۡـُٔولࣰا }

[سُورَةُ الإِسۡرَاءِ: ٣٦]

Kuma sunki su yi aiki da ayar Suratun Nahli:

{ وَمَاۤ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ إِلَّا رِجَالࣰا نُّوحِیۤ إِلَیۡهِمۡۖ فَسۡـَٔلُوۤا۟ أَهۡلَ ٱلذِّكۡرِ إِن كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ }

[سُورَةُ النَّحۡلِ: ٤٣]ss

Professor Salisu Shehu,
Shi ne tsohon Shugaban ‘Centre for Islamic Civilisation and Inter-faith Dialogue’ na Jami’ar Bayero, Kano.

 

Continue Reading

Trending