Connect with us

Hausa

Yadda lemon Jolly Jus ya hallaka mutane biyu, da jikkata 19 a Kano

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Akalla mutane biyu ne suka hallaka, kimanin 21 suka kamu da wata cuta da ba a kai ga ganota ba, sakamakon zargin shan lemon Jolly Jus da wa’adin amfani da shi ya kare.

Kano Focus ta ruwaito al’amarin ya farune a unguwannin Warure, Dandago da kuma Sabon Sara a cikin Birnin Kano.

A cewar shaidun gani da ido, shan ruwan lemon ya kwantar da mutane 13 ‘yan gida daya a unguwar Warure Makasa, yayin da ya kwantar da wasu shida a makota.

Ya yin da sauran suka kamu a unguwannin Dandago da Sabon Sara.

Haka zalika sunce shan lemon ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu, daya a Unguwar Garangamawa, yayin da guda kuma ya mutu a unguwar Sabon Sara.

Siyama Rabi’u ita ce wadda ta hada lemon ta baiwa kowa ya sha a gidan ta ce da farko sun za ci ruwa ne da suka siya daga wurin ‘yan garuwa, sai dai daga baya suka fahinci sun sha lemon jolly Jus ne da wa’adinsa ya kare.

“A ranar Asabar din da ta gabata ne na girka abinci, na kuma hada lemo mukaci muka sha da ‘yan gidamu.

“Jim kadan bayan cin abincinne ni da ‘ya ta da kuma kanina muka fara amai, sai kuma daga baya muka fara fitsarin jini.

“Abu kamar wasa sai duk ‘yan gidanmu suka fara, aka garzaya da mu asibitin Dr. Shamsu da ke unguwar Garangamawa, aka dan yi mana magani muka koma gida.

“Sai dai muna komawa gidanne kuma al’amarin ya kara ta’azzara, sai aka garzaya da mu asibitin Imamu Wali, daga nan kuma aka mayar damu Aminu Kano.

Ba ruwan yan garuwa ne matsalaba.

Siyama Rabi’u ta ce ba ruwan ‘yan garuwa ne ya haifar musu da ciwon ba kamar yadda ta fada tun da fari.

Ta ce a iya tunaninta ruwan da suka sha ne tun da fari, amma daga baya ta tabbatar ba ruwan ba ne.

“Na za ta ruwan da muka sha ne ya bamu wannan matsalar sai da bincike ya nutsa muka gano ashe lemon Jolly Jus da muka sha.

“Mun duba takardar lemon sai muka ga ashe wa’adin amfani da shi ya kare tun Oktoba 2020.

Tuni dai hukumar kare hakkin masu siyan kayayyaki ta Kano Consumer Protection Council ta shiga bincike kan al’amarin.

Haka zalika hukumar ta kama lemukan da dama da wa’adin amfani da su ya kare.

Hukumar ta ce za ta tsananta bincike domin gano lemukan masu matsala.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Mahaya dawaki sun kashe mutune 2 a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wasu magidanta biyu ‘yan gida daya sun rasu sakamakon banke su da mahaya Dawaki su ka yi yayin da suka bisa babur a titin  Sokoto Road da ke Kano.

Kano Focus ta ruwaito cewa ranar Asabar ne mahaya Dawakin suka kashe Inuwa Sani da Abdulrahaman Sani ‘yan unguwar Yakasai a Birnin Kano.

Mahaifiyar su, Rukayya Ali ta ce an kashe ‘ya’yan na ta ne akan hanyar su ta zuwa gaishe ta.

Ta ce kowanne daga cikin marigayan  ya mutu ya bar mata daya  daya ‘yaya shida.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta Abdullahi Haruna Kiyawa.

Ya ce suna zargin wani matashi Sadiq Adamu, 22, da abokansa bakwai ne suka shirya hawan Dawakin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen.

Ya ce sun kama biyu daga cikin wadanda ake zargi kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su gaban kotu.

Masarautar Kano dai ta haramta hawan Dawaki a cikin birinin Kano sakamakon jikkatawa ko hallaka jama’a da mahayan ke yi.

Continue Reading

Hausa

Kishi: Mata a Kano ta hana a yiwa mijinta jana’iza a gidansa

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Tsananin kishi ya sanya wata mata Jamila Muhammad hana shigar da gawar mijinta cikin gidansa domin yimasa jana’iza bayan rasuwarsa.

KANO FOCUS ta ruwaito al’amarin ya faru ne ranar Litinin a unguwar Gwazaye da ke yankin Dorayi a karamar hukumar Gwale, da ke nan Kano.

Abdullahi Mustapha guda ne daga cikin wadanda suka sheda al’amarin ya shaidawa shirin ‘yan zazu na gidan rediyon Dala cewar tsananin kishi ne ya hana matar amincewa a ajiye shi a gidanta.

Ya ce matar na zaune ne a gidan mijin bayan da kotu ta raba aurensu ta kuma umarceshi da ya bata dama ta ci gaba da zama a gidan saboda yara.

Ya kara da cewa matar ta nemi su rabu da mijin ne don kawai ya auri wata matar.

Sai dai bayan auren sabuwar matar ne kuma auren ya rabu, haka kuma gidan ya koma hannunta.

Mustapha ya ce bacin rai da takaicin matar ne ya haifarwa mijin ciwon zuciya har ya mutu.

Bayan mutuwar tasa ne kuma aka daukoshi daga asibiti aka kuma kaishi gidan da matar take amma fafur ta ce ba za a yi masa sutura a gidan ba.

A cewar Mustapha ba irin bakin da ba a baiwa Jamila ba, amma ta ce sai dai a kaishin gun amarya a yi masa jana’iza.

Hakan ta sanya wani dattijo a unguwar ya bada damar a shigar dashi gidansa domin yi masa jana’iza.

Tuni dai yan uwan Jamila suka dauke ta zuwa garinsu da ke Gezawa domin gudun abinda zai faru.

Continue Reading

Hausa

Hisbah ta nemi taimakon Saudiyya kan dakarunta

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta nemi taimakon kasar Sadiyya da ta tallafa mata wajen horar da jami’anta akan sha’anin aikinsu.

Kano Focus ta ruwaito babban Kwamandan Hisbah, Muhammad Harun Sani Ibn Sina ne ya yi rokon a ofishinsa ranar Lahadi.

Wanan na zuwa ne bayan da hukumar ta karbi bakuncin daya daga cikin limaman Masallacin Harami na Makkah Farfesa Alhassan Bin Abdulhameed Albukhary tare da ayarinsa.

Ayarin Limanin sun ziyarci Kano ne bisa gayyatar Jami’ar Bayero don horarwa ta musamman ga alkalai da daliban ilimi wanda wannan ita ce horarwa irinta ta hudu da suka yi a kasar nan.

Hisbah ta kama matar da ta yi safarar jariri daga Delta zuwa Kano

Ramadan:Hisbah ta kama Gandaye 11 a Kano

Shigar mata: Hisba ta kama wani saurayi da ya rikide zuwa Amina a Kano

“Babban kalubalenmu shi ne rashin wurin da za mu horar da jami’anmu domin su kara samun horo a kan ayyukansu.

“Zai yi kyau idan har za mu samu tallafi daga Hukumar Kasar Saudiyya mai albarka wajen samar mana da wuri ko kuma makarantun da jami’anmu za su dinga samun horo ko da kuwa a kasar Saudiyya din ne.” cewar Ibn Sina

A nasa Jawabin Imam Albukhariy ya yaba wa hukumar Hisbah akan ayyukan da take gudanarwa a fadin jihar nan, inda ya nemi su rubanya kokarinsu akan ayyukansu.

“Shi aikin umarni da aikin alheri da hani da mummuna abu ne babba a harkar zamantakewar al’umma.

“Wasu malamai suna cewa da za a kara wani abu a kan rukunan Musulunci to da abin da za a kara ba zai wuce umarni da aikin alheri da hani da mummuna ba saboda muhimmancinsa a Musulunci.

“Don haka ’yan Hisbah ku sani aikin Allah kuke yi.”

Farfesa Albukhari wanda shi ne Shugaban Sashen Larabci na Jami’ar UmmulQura da ke garin Makkah ya bayyana cewa, Hukumar Kasar Saudiyya za ta taimakawa hukumar Hisbah da duk irin abin da take bukata, matukar dai bai ci karo da tsarin mulkin kasar ta Saudiyya ba.

Continue Reading

Trending