Connect with us

Hausa

Daliban Kano sama da 20,000 ba za su shiga manyan makarantu ba

Published

on

Aminu Abdullahi

Daliban sakandiren fasaha a jihar Kano 10,691 da kuma na bangaren Arabiyya 13,210 ne ba za su samu shiga manyan makarantu a bana ba.

Wannan ya biyo bayan rashin fitar sakamakon jarrabawar kammala sakandire da suka rubuta tun a bara.

Kano Focus ta ruwaito cewa kimanin watanni bakwai kenan da daliban suka rubuta jarabawar, sai dai sun gaza samun sakamakon saboda kin biyan kudin jarrabawar da gwamnati tayi.

Idan za a iya tunawa dai anyi ta kai ruwa rana da gwamnatin jihar Kano kafin ta biya wani ba’ari na kudin jarrabawar dalibai ta NECO.

Wannanne ma ya sanya daliban da suka dauki jarrabawar (NABTEB) da kuma ta (NBAIS) a jihar Kano ke ganin su kam ci gaba da karatu a bana sai dai su ji ana yi.

Yajin aikin malaman jami’o’i baraza ne ga ilimi a arewacin kasar nan-Danmaje

Matasan Arewa ne koma baya a bangaren fasahar sadarwa-Kungiya

Da gan-gan gwamnati ta ki biyan kudin NECO-Iyayen yara

Rilwanu Sulaiman dalibin Arabiyyana ne da ya rubuta jarrabawar, ya ce watanni shida kenan da kammalawa, amma har yanzu ya gaza samun sakamakon sa.

Ya ce da yawa daga cikinsu ba za su samu gurbin karatu a jami’o’in da suka nema ba, sakamakon rashin sakin sakamakon.

“Muma ‘yan jihar Kano ne muna kira ga mai girma gwamna da ya taimaka a sakar mana sakamakonmu ko ma cigaba da karatu”

“Sai da muka biya kudin rijista sannan muka rubuta jarabawar duk da cewa gwamnati na ikirarin ilimi kyauta ne,” inji shi.

Ya ce rike sakamakon nasu tamkar hana su cigaba da karatune, kasancewar da yawansu, iya jarrabawar kawai suka rubuta.

Shima Auwalu Ibrahim dalibin da ya rubuta jarrabawar ta NBAIS ya ce rashin karbar sakamakon na su yasa ya yanke shawarar rubuta jarabawar (WAEC) wadda itama aka ce ba za a yi a wannan shekarar ba.

“Bamu da yadda zamuyi, amma muna fata gwamnati za ta duba halin da muke ciki, tare da sakar mana sakamakon jarabawar mu,” injishi.

To ko me gwamantin jihar Kano ke yi gamme da rashin fitowar sakamakon jarabawar daliban?

Aliyu Yusuf shi ne jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ya ce bashin da hukumomi ke bin gwamnati ne ya sanya aka gaza sakin sakamakon.

Aliyu Yusuf wanda ya yi magana a madadin kwamishinan Ilimi na jihar Kano Muhammad Sunusi Kiru ya ce da zarar gwamnati ta biya kudaden za a saki sakamakon.

Ko da dai Aliyu ya gaza yin cikakken bayani kamar yadda jama’a za su fuskanta, amma dai ya bayyana tsananin bashin da ake bin gwamnati ne yasa aka kasa fanso jarrabawar.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Hausa

Gamayyar Malaman Kano sun nesanta kan su daga tsige Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Gamayyar Malaman Jihar Kano da suka kunshi jagororin darikun Tijjaniyya da Qadiriyya da kuma Salafiyya sun yi watsi da sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai.

Wata sanarwa da KANO FOCUS ta ci karo da ita dauke da sa hannun sakataren gamayyar Malaman, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ranar Talata malaman sun ce ba da yawunsu aka dauki wannan mataki ba, kuma ba sa goyon bayansa.

Malaman da suka sahale a fitar da sanarwar sun hada da Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Ibrahim Sheh Maihula da Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Imam Nasir Muhammad Adam ( Shugaban majalisar Limaman masallatan Juma’a).

Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo da Farfesa Muhammad Babangida da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.

Continue Reading

Trending