Connect with us

Hausa

Yin sahur da ‘codeine’ na rage mana wahalar azumi- matasa a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

A yayin da aka fara azumin watan Ramadana a yau Talata, wasu matasa a Kano sun ce matukar suna son daukewa kansu wahalar azumi to sai sunyi sahur da codeine.

A cewarsu ta hakan ne za su wuni suna bacci da zai dauke musu duk wata wahala da ake tunin ana sha lokacin azumi.

A wani bincike da Kano Focus ta gudanar ta gano yadda wasu matasa ke  ta’ammali da maganin tari  mai dauke da sinadarin codeine lokacin da aka tashi sahur, duk da sunan rage radadin azumi.

Idan za a iya tunawa dai gwamnati ta haramta sayar da maganin a kasa baki daya, bisa zargin yana gusar da hankalin matasa tare da sanya su aikata muggan laifuka.

Duk da wannan yinkuri amma ana cigaba da sayar da maganin a boye, a farashi mai dan karan tsada, wanda ba kowa ke iya siya ba.

Sai dai a iya cewa lamarin shan maganin ya canza salo a wannan lokaci, ta yadda wasu matasan kan sha fiye da kima yayin sahur don ya gusar musu da hankali tare da hana su jin wahalar Azumi.

Abubakar Sani  mazaunin unguwar Tukuntawa ya shaidawa Kano Focus cewa ya fara shan Kodin yayin sahur shekaru biyu da suka gabata.

Ya ce a kowanne sahur yana shan rabin kwalba, wanda hakan ke bashi damar yin bacci har zuwa gab da lokacin shan ruwa.

“Bana bacci da daddare to duk lokacin da na sha na kanyi bacci sosai da rana, wani lokacin ma sai ana gab da kiran sallar magriba nake tashi.

“Duk kwalba guda ana saida tane a naira 3000 wani lokacin ma tana kaiwa 3500 kuma a haka nake siya,” a cewar sa.

Shima Farouk Gambo da ke unguwar Rijiyar Zaki, ya ce zafin rana da kishirwa suka sanyashi shan Kodin don gudun wahalar azumi.

“Ai ance baccin mai azumi ma ibada ne, to kaga bana tunanin hakan zai zama laifi idan nasha don nayi bacci sosai.

“Kuma kaga ba maye yake sani ba kawai bacci ne irin mai nauyin nan,” a cewar sa.

Ko me malaman Addini suka ce?

Malam addinin musulunci sun ce haramunne shan duk wani abu da zai gusar da hankali don dauke wahalar azumi.

A cewar Malam Abubakar Abdulsalam Baban Gwale manzon Allah S.A.W ya ce duk wani abu da zai gusar da hankali haramun ne.

Ya ce abubuwan da ke gusar da hankali domin neman lafiya ko magani kamar allura ta wata cuta koda anyisu da azumi babu matsala.

“Amma idan mutum yasha ne kawai don ya yi bacci don ya gusar masa da hankali hakan taba Ubangijine.

“Kuma zai rusa masa azumi domin maye yana karya azumi.

“Idan lalura ce za ta sa a sha ko maye ne na lalura da rashin lafiya azumi ma baya kan wanda baya cikin hankalin sa,” a cewar sa.

Ya kara da cewa koda ba Kodin ba haramunne mutum ya samu daki mai sanyi da zai rinka shirga bacci har zuwa magriba.

Ya kuma ce masu irin wannan dabi’a su sani cewa ubangiji baya wajibta yin azumi ne don a sha wahala ba.

Ya ce manzon Allah S.A.W cikin hadisin Salmanul Farisi wanda Ibn Kuzaima da Baihaki suka rawaito ya ce azumi wata ne na hakuri shi kuma hakuri sakamakon sa shi ne aljanna.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Zawarawa ne ke sanya Abaya-Masana

Published

on

Aminu Abdullahi

Batun Abaya ya mamaye kafafen sada zumunta musamman twitter tun bayan shigowar watan Ramadan ta yadda ‘yan mata ke nuna sha’awarsu ta ganin sun sanyata yayin bikin karamar Sallah.

Batun ya janyo barkewar muhawara tsakanin ‘yan mata da samari, inda wasu matan ke da ra’ayin yin Abaya koma ta wane hali ya yin da wasu kuma suka bayyana rashin gamsuwarsu na yin Abayar saboda wasu dalilai da suka bayyana.

Sai dai wani masanin zamantakewar  Dan Adam da ke jami’ar Bayero a nan Kano Aminu Sabo Dambazau ya ce sanya Abaya alamu ne da ke nuna cewa mace Bazawara ce.

Ya ce a zamanin baya mata na sanya ta ne domin su rufe jikinsu sabanin yanzu da ta canza manufa.

Ya ce anyiwa Abayar fassara, cewar idan mace ta sakata hakan na nufin ta taba yin aure ta fito ne, kuma tana neman wani mijin.

“Idan kaga mace tasa Abaya ta fito titi to bazawara ce da take neman  mijin aure,  wata kuma ta saka ne kawai don ta ja magana,” a cewar sa.

Ya ce dabi’a ce ta dan Adam san birgewa musamman mata wanda hakan ne yasa suke gasa don ganin sun kere sa’a ba tare da sanin

To sai sai Kano Focus ta yi nazari kan yadda batun Abaya a kafafen sada zumunta ya dauki sabon salo na izgili da zargi a tsakanin matasa.

Me ya ja hankalin mata son kwaliyyar Abaya da sallah.

Abaya ba bakuwar sutura ba ce, mata sun jima suna sanyata tun lokacin da ba ta zama gama gari ba, kuma ainihi shigar ta samo asali ne daga larabawa.

Sai dai  batun a bayar ya zama abin da a kafi tattaunashi a shafin twitter da ya bazu zuwa sauran shafukan sada zumunta.

Hakan yasa da yawan ‘yan mata ke da burin ganin  sun mallaketa don ganin cewa suma ba a barsu a baya ba.

Wannan dai ya sanya samari tofa albarkacin bakinsu a kan lamarin wanda hakan yasa batun Abayar ke neman canza salo.

Wasu samarin sun wallafa rubuce rubuce daban daban da ke tattare da zargi da kuma rashin tabbas ga wadanda ke da burin sanya Abaya da sallah.

Ya yinda wasu samarin ke ganin batun Abayar ka iya zama wata hanya ta rabasu da masoyan su ko kuma haddasa fitina tsakanin mijin da bashi da halin yin Abayar da matar sa.

Ya yin da wasu kuma ke ganin cewa akwai matan da za su iya bin hanyar banza don cika burin su na samunta.

Ra’ayoyin mata

Kano Focus ta jiyi ra’ayoyin wasu mata kan batun yin a baya da karamar sallah.

Sadiya Ibrahim Mai shekaru 25 a unguwar Kofar Famfo cewa tayi za tayi yayin Abaya kamar yadda taga da yawan mata ita za su yi.

Ta ce a cikin kayan da za ta saka da sallah saida ta fadawa mahaifin ta ya hado mata da a baya.

“Ni dama ina sakawa to kuma naga yanzu wannan sallar ita za ayi ya yi shiyasa nima na fadawa mahaifina ya siyamin,” a cewar ta.

Ummukulsum Abubakar mai shekaru 20 ta ce tanaso tayi Abaya da sallah amma ba ta da hali.

“Inaso na saka amma irin wacce ake cewa za a yi yayin ta gaskiya tayi tsada sosai don suna maganar kudin ta ya kai dubu 20.

“Ni kuma ba za a iya siyamin riga kawai ta dubu ashirin ba amma idan saurayi na ya bani zan karba tun da shi yayi niya,” Inji ta.

Ta kara da cewa tana rage kudin makarantar ta koda an siya mata mara tsadar to za ta yi ciko don a canza mata.

Kadija Ahmad Sanusi da ke unguwar koki mai shekaru 26 cewa tayi “Maganar gaskiya bani da ra’ayin Abaya, tana burgeni amma ni indai abu ya zama gama gari to bazan yi shiba.

“Sabida mafi yawanci Abayoyin yanzu robane asaka dan gyalen ta ayi rolling a fita haka kuma nasan akwai illar da take tattare da ita shiyasa shaidan yake kawata wa mutane ita a idanuwan su,” a cewar Kadija.

Ta kara da cewa wasu ba siya suke yiba, basu akeyi wasu kuma koda basu da hali suna sanyawa kansu ne cewa dole sai sunyi.

Sadiya Bello Abdullahi da ke Hotoro ta ce tun kafin a fara batun a baya tana sakawa.

Ta ce ita ba ta daga cikin mutanen da ke da ra’ayin sanyawa da Sallah.

“Ba wai kudin ne bamu da shiba, kawai dai bamu da ra’ayi ne, wasu ma samarinsu za su roka su basu kuma a sanadiyyar haka sai a samu sabani a tsakani.

“Ga kuma wadanda suka ce za su yi bai kamata su takura kansu akai ba, akwai gumama da na gwanjo,” a cewarta

Continue Reading

Hausa

‘Yan Sanda a Kano sun kama dan Vigilante na kwacen waya

Published

on

Aminu Abdullahi

Rundunar ‘yan sandan Kano ta kama jami’in Vigilante da wasu mutane uku bisa zargin kwacen waya a cikin baburin Adai-daita sahu.

Kano Focus ta ruwaito cewa mai magana da yawun rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Laraba.

Ya ce wadanda aka kama sun hada da Musa Sa’id dan shekara 21 da Umar Mukhtar mai shekaru 19 da kuma Yusuf Kadda’u dan shekara 18 sai Walid Abdulsalam mai shekaru 19.

Ya kara da cewa sun kama su ne da Adai-daita Sahu guda daya da wukake guda uku, ya yin da suka fito yin kwacen waya.

Kiyawa ya ce kwamishinan ‘yan sanda Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bada umarnin maida su baban sashen binciken manyan laifuka na rundunar, wanda da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.

“Duk lokacin da aka ga irin wadannan mutanen to a gaggauta sanar da mu don daukar mataki.

“Kuma duk lokacin da wayar mutum ta fadi ko aka sace  to ya kai korafi ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

“Kuma idan layin da ke jikin wayar da mutum ke amfani da ita ya bata to ya gaggauta zuwa bankin sa ko kuma ya kira lambar karta kwana,” a cewar sa.

‘Yan sanda sun kama yan fashi uku a Jogana

‘Yan sanda a Kano sun kama makocin da ya jagoranci yiwa makocinsa fashi

Cin zarafi: Kotu ta umarci ‘yan sanda su binciki Baffa Babba Dan Agundi

Ya kara da cewa yawancin masu kwace a baburin Adai-daita Sahu suna da kama, wanda hakan yasa kwamishinan ‘yan sanda ya kara fadada sintiri na jami’an tsaro don magance matsalar.

A nasa bangaren daya daga cikin wadanda aka kamda ya ce shi dan Vigilante ne ya ce rashin kudi ne yasa suka hada kai tare da fitowa kwacen waya.

Ya ce ya dauki makami guda daya ne a ofishin ‘yan Vigilante yayin da kuma suka karbo ragowar makaman a gurin wasu.

“A ofishin Vigilante na dauko, ni dan Vigilante ne kuma wannan shine karo na farko dana taba yin haka.

“Mun zo nan wajen Ja’oji sai ‘yan sanda suka kama mu,” a cewar sa.

Continue Reading

Hausa

Zargin neman matar aure: Hisbah ta kori Uba Rimo

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kori daya daga cikin jami’anta Muhammad Sani Uba Rimo biyo bayan kamashi da matar aure a hotal.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Lawah Hamis Fagge ne ya shaidawa Kano Focus ranar Talata.

Ya ce korar ta biyo bayan sakamakon binciken da kwamitin da aka kafa ya bincike Rimo ya fitar.

Idan za a iya tunawa a watan Maris din da ya gabata ne aka zargi Sani Uba Rimo da neman matar aure a wani dakin Hotal a unguwar Sabongari da ke nan Kano.

Sai dai bayan kamashi ne ya ce ya je kama matar ne domin sasantata da mijinta bayan ta gudu daga gida.

Uba Rimo shi ne shugaban sashen da ke kula da kama karuwai a hukumar ta Hisbah.

Continue Reading

Trending