Connect with us

Hausa

Illoli 10 na shafukan sada zumunta

Published

on

Zulaiha Danjuma

Shafukan sada zumunta wani dandali ne da al’umma ta runguma a wannan zamani da ta kai galibin al’umma a yanzu basa iya rayuwa sai da su.

Irin wadannan shafuka sun hadar da Facebook, Twitter, Whats app, da sauran su.

Sai dai masana sun ce yin amfani da dandalin na da nasa  muhimancin da kuma barnar da ke tattare da shi.

A zantawar jaridar Kano Focus da shugaban sashin nazarin kafafen yada labarai na zamani da ke jami’ar Bayero a nan Kano Dr Nura Ibarahim ya bayyana illoli goma da ke tattare da amfani da kafafen.

Illolin sun hadar da yaduwar hotuna da fina-fina batsa, cin mutuncin masu mutunci, yada labarun karya, yaduwar maganganun batanci, Damuwa, zalunci, Yada shaye-shaye da neman maza, Buri mara nanufa, Lalacewar ilimi da tarbiyya da Bangar siyaya

Yaduwar hotuna da Fina-finan batsa

Dakta Nura ya ce illa ta farko da ke tattare da shafukan na sada zumunta shi ne yadda al’umma suka dauki shafukan wurin zuwa domin kallon fina-finan batsa.

Ya ce shafin twitter wuri ne na samun bayanai na musamman akan abubuwa da dama amma mafi yawan mutane na zuwa kan twitter don kallon finifinan batsa

“Mutane sun dauki facebook da twitter a matsayin wurin yada hotunansu na Allah wadai da kallon Fina-finan shashanci”

“Ada da zaran ka hau wadannan  shafuku kana karuwi, dan zaka ga mutanen da za su yi maka hanya da zai iya anfanar da kai.

Cin mutuncin masu mutunci

Daktan ya kara da cewa yadda matasa suka fidda tsoro da kunya a idamuwansu wajen cin mutuncin wadanda ke gaba da su a shafukan sada zumunta abune me cin rai

“Yadda aka san mu yan Afrika da yan Arewa da girmama na gaba da mu amma yanzu za a ga wani yaro me karancin shekaru na zagin sa’an mahaifinsa ba tare da jin nauyin hakan ba”

Yada Labaran karya

Malamin ya kara da cewa yada labaran da basu da tushe ballantana makama na daya daga cikin matsalolin da ke raba kawuwan ‘yan kasa

“Wani kawai na cikin dakin sa zai fito da labari na raba kan al’umma ta bangaren siyasa, Al’ada da sauran su”

“Sau dayawa mutane na bude shafukan a yanar gizo domin damfarar jama’a.

“Sai suce mutane su bi wani link don samun wani tallafi ko aiki amma ko kadan hakan ba gaskiya ba ne.”

Maganganun Batanci

Dakta Nura ya ce maganganun cin mutuncin juna da yawan tafka muhawara a dandalin sada zumunta na daga cikin al’amuran da ke fito da illarta.

“Duk mun san irin hatsarin dake tattare da irin wadannan kalaman, kwanaki wani dan siyasa ya yi maganar batanci da hakan ya kai shi gidan yari na tsahon shekara guda”

“Mutane na tunanin cewa internet wuri ne da mutum zai iya yin duk abinda ransa ke so.

“Wannan shi ne abun da ke kara yawaita maganganun batanci”

Damuwa

Daktan ya ce kafar sada zamunta na sa wa wasu damuwa ta yadda suke ganin yadda wasu ke wallafa abubbuwan nasararsu da suka cimma.

Da yawan  mutane na ganin cewa suna samun koma baya idan suka kalli yadda wasu ke nuna irin rayuwarsu ta jin dadi.

“Mutane sun dauki rayuwar social media tamkar gaske, sun ki su fahimci cewa duk wanda ya wallafa abu a kan yanar gizo yayi hakkan ne dan ya burge.

“Kuma ba wanda zai sa hotun da zai bayyana shi a masayin mai shan wahala sai dai me jin dadi”

“Wani yaga kayan jikin wani batare da sanin kayan nasa ne ko ba nasaba,

“Shima sai yasa irin ta, kuma in bai samu ba ko baida hali ya shiga damuwa ke nan”

Hassada da bakin ciki

Daktan ya ce jama’a na zaluntar junasu  a shafukan sada zumunta ta hanyar hassada, rashin fahinta ko bakin ciki da babbancin ra’ayi

“Wani  ganin yadda kake rayuwa a social media ba tare da sanin ka ba, sai kawai ya yi ta yi maka hassasa da bakin ciki.

“Idan ka wallafa hoto sai a samu abin ci maka mutunci ko dariya koda hoton bai cancanci a yi masa hakan ba.

Sheye-shaye da neman maza

Yadda matasa suka mayar da shafukan sada zumunta wurin tallata yadda suke shaye-shayensu abin a yi alla wadai ne a cewar malamin.

“Yanzu matasa na shan shisha su dauki video da hotonsu su yada duniya ta gani, a ganin su hakan burgewa ne”

“Sheye-shaye da neman maza ya mamaye social media, kuma matasa da sun ga hakan sai su dauka wayewa ne”

Buri mara manufa

Malamin yace buri abune me kyau da dan adam ke dashi, amma buri mara manufa na iya zamowa matsala a rayuwar dan Adam

“Burin cewa zaaka sayi  waya sama da kudin da kake samu a wata ko cikin sana’ar ka ba karamin shashenci ba ne.

Dan kaga wani na rike da irin ta, bayan baka biya kudin hayar gidan ka ba ko yi wa iyayenka ko iyalanka abinda ya da ce”

“Wata za ta yi aure wani ya mata lefe 12 ko 14 sai kice ba zaki yi aure ba sai wanda zaki aura yayi miki irin na wance da kika gani a social media

Lalacewar ilimi da tarbiya

Dokta yace ilimi da tarbiyar yara na iya samun matsala sanadiyyar irin abubuwan da suke kalla a shafukan sada zumunta da kuma kwaikoyon irin ababuwan da suke gani

“Idan anbar yaro yana kallon shirye-shiryen da bai kamata ba saboda rashin karfin tunaninsa hakan ka iya sauya masa tunani.

Hakan na sawa ya fara canza halayyarsa na kwarai  zuwa na banza dan yaga anyi acikin wani fim da ya kalla”

Bangar siyasa

Malamin ya cigaba da cewa yanzu matasa sun rude da harkokin siyasa, inda wani ma bai damu da rasa ransa ba akan wani da bai sanshiba

“Matasanmu sai dai suje shafukan sada zumunta suna zage-zage da cin mutunci, saboda wani nasu da sukeso.

“Sunki mayar da hankali akan abubuwan daya shafi rayuwar su sai dai dabanci da bangar siyasa”

Hanyoyin magance illolin

Dakta Nura ya kuma bada wasu hanyoyi da ake ganin za abi domin magance wadannan matsaloli.

Ya ce dolene gwamnati sa doka akan masu yada kalaman karya da batanci.

Haka zalika dole iyaye su baiwa yayansu tarbiyya, kan yadda za su yi amfani da shafukan sada zumunta.

Ya ce malaman addini suma sai sun bayar da gudunmawa wajen ilimantar da samari illar da ke tattare da kafafene yada labarai na zamani

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Hausa

Gamayyar Malaman Kano sun nesanta kan su daga tsige Malam Ibrahim Khalil

Published

on

Sheikh Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Gamayyar Malaman Jihar Kano da suka kunshi jagororin darikun Tijjaniyya da Qadiriyya da kuma Salafiyya sun yi watsi da sanarwar tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin majalisar malamai.

Wata sanarwa da KANO FOCUS ta ci karo da ita dauke da sa hannun sakataren gamayyar Malaman, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ranar Talata malaman sun ce ba da yawunsu aka dauki wannan mataki ba, kuma ba sa goyon bayansa.

Malaman da suka sahale a fitar da sanarwar sun hada da Shugaban Darikar Kadiriyya na Afrika ta Yamma Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Ibrahim Sheh Maihula da Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Imam Nasir Muhammad Adam ( Shugaban majalisar Limaman masallatan Juma’a).

Sauran sun hada da Farfesa Musa Muhammad Borodo da Farfesa Muhammad Babangida da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.

Continue Reading

Trending