Connect with us

Hausa

Dalilai 4 da ya hana Teloli samun dinki a bana

Published

on

Zulaiha Danjma

Teloli a jihar Kano sun koka kan karancin dinkin sallah da jama’a ke kawo musu, biyo bayan matsin rayuwa da ake ciki.

Kano Focus ta rawaito cewa Telolin sun bayanna dalilai hudu da ke kara ta’azzara rashin samun aikin.

Cikin kuwa har da karin kudin kayan dinki, Rashin kudi a hannun jama’a, dawurwuran tsayar da zabi, da kuma rashin samun albashi.

Karin kudin kayan dinki

A cewar wani tela Abdussalam Kabir da ke dinki a unugwar Rijiyar Zaki, kudaden da tela yake siyan kayan dinki sun yi tashin gwauron zabo.

“A gaskiya komai ya canza, saboda tsadar kayan dinkin, samun dinki ya ragu”

“Wasu abubuwan da ake siya  ada N600 yanzu ya koma N800

“Me dinka set 4 ada da wuya yanzu ya dinka kala daya” Acewarsa.

Shi ma wani tela Kabiru Abubakar da ke Tudun Maliki  ya ce kudaden siyan kayan aiki a bana sun nunka.

“Kudin siyan kayayyakin dinki sun karu gaskiya, wasu sun ninka kudinsu akan yadda aka sansu”

“Kananan kamar zare wani dan N40 ya dawo N50, kuma quality na kayan ma duk  sun ragu.

“Shi komai da komai yadda aka sanshi ya ragu a quality ga kuma kudin sa ya karu” Acewar sa.

Rashin kudi 

Telolin sun cigaba da cewa rashin kudi na hana abokan huldarsu  kawo dinki.

Kabiru Muhammad ya ce, masu kawo dinki sun sauya daga yadda suka saba kawowa ba kamar a baya ba.

“Idan kostoma ada na kawo kaya kala 3, yanzunma zai iya kawo ukun amma za kaga darajar kanyan sun ragu.

“Alalmisali ace  bara sun kawo maka shadda me tsada wanda duk yadi zai iya kaiwa 2,500 zuwa 3,000 yanzu sai an rage kudin.

“sai ka gama mutum yaje ya siyo yadi, irin su Lana ko Kashmir ko irin su dan Aba dan ya samu rarar kudi.

“Wannan ragowar canjin da aka samu zai iya biyan kudin dikin dasu”

Haka zalika, Abdulsalam Muhammad ya ce “yara ma da iyayensu ke dinka musu kala 4 ko 3 yanzu da wuya a yi musu kala 2 saboda ba kudin”

“Kusan dai duk wanda ya kawo dinkin yaransa ba sama da guda biyu-biyu” Acewar sa

Rashin takamai-mai

Haka zalika Telolin sun bayyana cewa mafi akasari magidanta na shiga halin dawurwura da rashin takamai-mai wajen zabin mai za su dinka da iyalansu.

Wasu na tuna ni biyu, tsakanin dinkin da wasu al’amuran na gida wanne ne ya fi amfami.

“Mafi akasari ta abinci ake bata sutura ba, wani gani yake mai zai yi, shin dinkin ya kamata ya yi, ko abincin yara yakamata ya siya, ko kudin makarantar yara zai biya.

“Irin wannan matsololin da suke faruwa shi ne yake sa muke fuskanta karancin kawo dinki”

“Amma duk da hakan mutane na yin iya bakin kokarinsu wajen ganin sun yi ma kansu da iyalen su sutura” Acewarsa, a cewar Kabiru tela.

Rashin Albashi 

Telolin sun bayyana cewa  rashin biyan albashi na sanya jama’a kasa kai musu dinky, tunda galibin al’umma yan albashi ne.

“Gaskiya wannan lokacin ana samun karancin samun kayan dinki musamman ma wasu ba a biya albashi ba.

“Wani yana jiran sai an biya, inda zai iya kasancewa sai karshe-karshen azumi za a biya, kuma lokacin wani ma zai tunanin dinkin”

Shi ma Kabiru tela yace “Wasu rashin albashi ne da wuri, wani za kaga gwamnatin ta ba da albashin amma ta cire wani baa’ari daga ciki.

“Wani lokacin ma ba a biya albashin akan lokaci ba ko dai wasu abubuwa makaman cin haka” Acwarsa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Hotuna: Sarkin Kano ya halarci taron Maulidi

Published

on

Aminu Ado Bayero

Nasiru Yusuf

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya halarci taron Maulidi da aka yi Gidan Rumfa (Gidan Sarki) ranar Litinin.

KANO FOCUS ta ruwaito cewa Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara ne ya gabatar da karatu a lokacin Maulidin.

Maulidin ya samu halartar manyan Hakimai da malamai da sauran jama’a.

Ga sauran hotunan taron Maulidin.

Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara

 

Continue Reading

Hausa

Yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil wasan yara ne – Prof. Alkafawy

Published

on

Malam Ibrahim Khalil

Nasiru Yusuf

Majalisar Malamai ta Kasa ta bayyana yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano da cewa wasan yara ne.

A wata sanarwa da KANO FOCUS ta samu Mai dauke da SA hannun Sakataren Kungiyar Farfesa Muhammad Sadik Alkafawy ya sanyawa hannu ranar Alhamis ta ce abun da aka yi ba ya bisa doka.

Ga cikakkiyar sanarwar:

“Majalisar  Malamai ta Kasa ta sami labarin yunkurin wata jama’a da ke kiran kanta Malamai, amma ta bari wasu wadanda ba su nufin alheri su yi amfani da su a kawo baraka tsakanin jama’ar Musulmi. Wannan abin takaici ne.

“Tun daga ranar da a ka assasa Majalisa zuwa yau ba a taba samun tabargaza irin wannan ba. Don haka Majalisa ta Kasa na yin kira ga wadannan mutane su tsoraci Allah su kauce ma son zuciya.

“Hakika Majalisar Malamai reshen jihar Kano ta yi daidai da tace wadanda su ka shiga wannan bankaura ba ‘ya’yanta ba ne tun daga jiha balle na Kasa. Yaya za a yi wanda ba ya cikin Majalisa ya ce ya kori wanda a ka kafa Majalisa da shi?.

“A wurin Majalisa ta Kasa abinda a ka yi ba ya bisa doka, kuma wasan yara ne. Hasali ma fata mu ke Allah ya ba shi shugabancinta na Kasa baki daya, amin.

“A karshe, Majalisar kasa ta yi mawafaka da duk abinda Majalisar Kano ta tsaya a Kai. Alhamdu Lillah.”

Continue Reading

Hausa

Tijjanawa ba sa goyon bayan nadin Pakistan shugaban Majalisar Malamai – Alkarmawi

Published

on

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

 

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم 

وصلي الله علي النبي الكريم 

Majalisar Malamai ta jihar Kano tana da mahimmanci ga Musulmin Arewacin Nigeria gaba daya ba Kano ba kawai, don ko ba komai Al’ummar Musulmi suna kara samun hadin kai da magana da murya daya sanadiyar wannan majalisar kuma babban abun bukata shine hadin kan Musulmi.

Amma sabon shugabanci da akai jiya (Litinin) da aka nada Malam Abdallah Saleh Pakistan (Shugaban Izala na jahar kano) zai iya rusa majalisar ma gaba daya, Saboda Shugabancin yana bukatar malamin da yake Zaune lafiya da duk akidun Musulunci da suke Kano, wanda Pakistan kuwa yana da matsala da wasu bangarorin.

Shawarata kowa a nan shine Asami malamin da yaki da kyakkywar alaka da kowa ya jagoranci Alumma Sai asami kai wa ga gaci.

Don haka a madadin Tijjanawa, gaskiya gabadayanmu musamman na jihar Kano muna sanar da cewa ba ma tare da Shugabacin Malam Abdallah Saleh Pakistan.

Khalifa Abdulmajid Alkarmawi

Shugaban Khuddamur Rasul SAW na Afrika

Continue Reading

Trending