Connect with us

Hausa

Shin za a iya fitar da zakkar fidda kai da kudi ko taliya?

Published

on

Farfesa Ahmad Murtala

Farfesa Ahmad Murtala

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Annanbinmu Muhammad da Alayensa da Sahabbansa bakidaya.

Bayan haka, a yau zan amsa tambayoyin da a ka dade ana tambaya wato halaccin fitar da kima a zakkar fidda-kai ko rashinsa. 

Tuntuni ban so na shiga amsa wannan tambayar. Sai dai tambayoyi kullum idan an zo karshen azumi, daf da Karamar, suna kara yawaita. A kan wannan tambaya aka rubuta wannan bayani. Allah ya bamu sa’a da dacewa.

1-Ana kiran wannan zakka da sunanye daban-daban. Daga ciki akwai ‘Zakatul Fidri’, wato zakkar da ake yi domin an kamala azumi za a koma cin abinci. Ana kuma kiranta da ‘Zakkatur Rikab’ “زكاة الرقاب”- (Al-Bayanu Wat Tahsil na Ibnu Rushd-Kakan:2/483). Fassarar da zata fi zama daidai da wannan ita ce ‘Zakkar Fidda-Kai’, duk da cewa an yi jam’i wuyaye a kalmomin laracin, amma fassarar Hausar ta fi zama daidai da wannan. Har ila yau, ana kiranta da ‘Zakatul Abdan’ “زكاة الأبدان” – wato zakkar da mutum zai fitarwa da kansa da kansa don ya tsarkaku.

2-Dalilai da yawa suna nuna wajibcin fitar da wannan zakka kamar hadisin Abdullahi bn Umar (R.A.) wanda ya ce, “Annabi (S.A.W.) ya farlanta fitar da zakkar fidda-kai sa’i guda na dabino, ko sa’i guda na sha’ir -(nau’in alkama ne)-, za a fitarwa da bawa da da, namiji da mace, karami da babba cikin Musulmi. Ya yi umarni da a fitar da ita kafin fitar mutane zuwa salla”-(Sahihul Bukhari, L:1503).

Haka nan a cikin hadisin Abu Sa’idil Khudri kuma ya ce, “Mun kasance muna fitar da zakkar fidda-kai sa’i guda na abinci-(an fassara shi da cewa yana nufin alkama)-ko sa’i guda na sha’ir ko sa’i gud.,,..,a na dabino ko sa’i guda na cukwi ko sa’i guda na busasshen inibi”-(Sahihu Muslim, L:2330).

Sa’i guda shi ne mudannabi hudu. Idan an yi la’akari za a ga sa’in zai yi daidai da kwano irin- na bogaji da ake amfani da shi a Kasar Hausa.

Wadannan hadisai, bayan nuni a kan wajibcin zakkar fidda-kai, sun bayyana irin abubbuwa da ake fitarwa da wannan zakka a lokacin Annabi (S.A.W) da Sahabbai. Hadisan sun nuna cewa ana fitarwa ne a kayan abinci guda biyar, wato: alkama, sha’ir, dabino, cukwi, busasshen inibi.

Ba bu wata ingatacciyar ruwaya da ta nuna Annabi yana fitar da kudi ko wani abin daban na kima ba abubuwan da aka ambata ba.

Wannan ya sa yawancin malamai suka tabbatar da cewa za a bayar da abinci ne kurum a wannan zakka. Domin yin hakan shi ne abin da nassin hadisan ya nuna baro-baro.

Aliyu bn abi uwais ya ce an tambayi Imamu Malik game da mutumin da yake wani wuri da ba abinci, shin zai fitarda zakkar fidda-kai da kudi!? Sai ya ce, A a wallahi! Sannan sai ya ce: mutum ya zamo a inda ba abinci, to shi me yake ci kenan!? Sai aka ce da shi ai ya zauna ne a wurin kamar wata daya, wata biyu!? Sai ya ce: idan ya dawo ya fitar da Zakkar fidda-kai din a abinci. Amma ba zai bayar da Wani abu ba abinci ba”-(Al-Amwal na Ibnu Zanjawaih, L:2456).

3-A daya bangaren akwai wani ra’ayin da yake ganin cewa za a iya bada kima ta adadin abin da za a fitarwa da zakkar.

Wani abu da yake da muhimmanci shi ne a san cewa wannan sabanin ra’ayi ba wai a wai zakkar fidda-kai kadai yake ba. Ya shafi har zakkar kudi da kayan noma da dabbobi. Amma akwai abubuwa guda biyu da yawancin masu tattauna wannan mas’ala ko karantata suke mantawa da su. Su ne:

i- Ra’ayin a bada kima ba wai sabon ra’ayi ba ne da aka kirkiroshi tsakanin duhun dare da sanyin safiya. Tsohuwar magana ce tun lokacin Tabi’ai akwaita.

ii- Ba malamin da yake ganin asali shi ne a bada kudi. Duk malaman da suke halatta a bayar da kima sun tabbatar da cewa bada abincin shi ne asali. Sai dai yanayin bukata da zai taso shi ne zai sa a koma ga zancen kima.

4- Mazahabin Malikiyya, wanda ake bi a wannan kasa, ya tabbatar da ana fitar da zakkar fidda-kai ne a abinci. Wannan ba wani sabani a kan haka. Sai dai ga wanda ya duba da kyau zai ga akwai rangwame da malaman mazahabin suke yi a cikin mas’alar, ta fuskar za a fitar da ita da wasu abubuwan na abinci ba wanda aka ambata a hadisin ba. Saboda suna da ma’ana daya da wadanda hadisan suka fada.-(Manahijut Tahsili na Arrajraji:2/455; Ikmalu Ikmalil Mu’lim na Ubbi:3/115, Kifayatid Dalibir Rabbani na Assazali:1/386-387). A wasu bayanan har da kudin ma kansu. Ga misalan irin wadannan bayanai daga cikinsu:

i-An tambayi Imamu Ibnul Kasim cewa, “Mutum ne ba shi da alkama a ranar da zai fitar da zakkar fidda-kai, sai yake son ya bawa mabukatan kudi don su saya da kansu, domin a ganin yin haka zai fi sauri? Sai Ibul Kasim ya ce, kada ya yi haka. Domin ba haka Annabi (S.A.W.) ya fada ba”. A wata ruwayar kuma sai Ibnul Kasim ya ce: Idan ya yi haka, ina ganin ba komai”.- Dangane da wannan ruwayar, Imamu Ibnu Rushd –Kakan, ya nuna cewa ba wani sabani tsakanin ruwayoyin guda biyun saboda ai ya basu kudin ne don su sayi alkamar su yi amfani da ita. – (Al-Bayan Wattahsil na Ibnu Rushd-Kakan:2/486-487; Annawadiru Waz Ziyadat na Ibnu Abi Zaid Al-Kairawani:2/303)

قال في العتبية:”وسئل-(ابن القاسم)- عن الرجل لا يكون عنده قمح يوم الفطر، فيريد أن يدفع ثمنه إلى المساكين يشترونه لأنفسهم، ويرى أن ذلك أعجل؛ قال لا يفعل ذلك. وليس كذلك قال رسول الله – صلى الله عليه وسلم. ومن رواية عيسى قال ابن القاسم: ولو فعل لم أر به بأساً.

قال محمد بن رشد الجد:”رواية عيسى هذه عن ابن القاسم، خلاف رواية أبي زيد عنه بعد هذا. وقد قيل إنها ليس بمخالفة لها. وإنما خفف ذلك في رواية عيسى هذه، لقوله يشترونه لأنفسهم، فإنما دفع الثمن إليهم على ذلك – والله أعلم، وبه التوفيق”.

Wannan ya nuna akwai rangwame a mas’alar, ba kaifi daya ba ce!

ii-Imamu Ash’hab yana ganin za a tsaya kurum a fitar da zakkar daga cikin wadannan kayan abinci da wadancan hadisai suka kawo. -(Ikdul Jawahirus Saminah na Ibnu Shash al-Khallal:1/219). Amma kunzumin malaman Mazahabin sun saba masa. Ta fuskar cewa za a fitarwa da abubwa har guda tara ko goma bisa duba da abincin da wasu garuruwa suke ci a lokacin da Imamu Malik ya bada fatawa.-(Mudawwanah: 1/391; Al-Bayan Wattahsil na Ibnu Rushd –Kakan:2/485). Sun kara: gero da dawa da shinkafa da Siltu da Alas. Wannan ya nuna a Malikiyyance ba bu laifi a fadada ma’anar hadisin zuwa ga duk abin da mutane suke ci a matsayin abinci. Wannan ta sa ma Imamu Ibnul Arabi Al-Maliki ya ce, “Ana fitar da zakkar fidda-kai ne daga abincin kowace al’umma. Masu shan nono su fitar a nono, masu cin nama su bayar da nama. Duk abin da suka ci, mabukatansu suna tare da su. Ba za su kallafawa kansu samo wani abin daban da ba su da shi su ba su ba, ba kuma zasu ki ba su abin da suke da shi ba”-(Aridatus Ahwazi na Ibnul Arabi Al-Malik:3/189; Ikdul Jawahirus Saminah na Ibnu Shash al-Khallal:1/219).

Sai dai yana da kyau a san cewa idan an ce abincin mutane gari ba ana nufin a tsahon shekara ba ne. Ana nufin irin abin da mutane suka rika ci a wannan watan na Ramalana kamar yadda Imamus Sawi ya fada.

Ya kara da cewa: Wannan shi ne zahirin abin da malamai irinsu Al-Haddab suka rinjayar. –(Hashiyatu Sawi Alas Sharhi Assagir:1/505)

 قال الصاوي-رحمه الله-:”والمنظور له غالب قوتهم في رمضان، على ما يظهر من الحطاب ترجيحه، لا في العام كله، ولا في يوم الوجوب”.

iii-Dangane da wadanda zasu fitar da kamar nono da nama da irinsu, sai malaman Malikiyya irinsu Imamu Abu Muhammad Abdullahi Asshabibi suka ce, “Sai a kaddara gwargwadon yadda sa’i guda zai ciyar, sai a bayar da kwatankwacinsa”. Duk da cewa akwai malaman da basu gamsu da wannan magana ba irinsu Al-Burzuli, amma wasu manyan malaman Malikiyyar irinsu Imamu Al-Haddab suna nuna wannan magana tana da karfi. Haka nan Al-Khirshi.-(Mawahibul Jalil na Al-Haddab: ; Sharhul Mukhtasar na Al-Khirshi:1/229; Sharhul-Izziyyah na Azzurkani: sh/482).

iii-Imamu Malik yana ganin baure-التين-ba abinci ba ne don haka ba za a bayr da zakka ta kayan abinci ko zakkar fidda-kai da shi ba. Amma sai Malaman Mazahabin tun daga kan Ibnul Kasim da Abdulmalik bn Habib da Abubakar Al-Abhari, da malaman Bagdada irinsu Isma’ilu Alkadi, da malaman Andalus (Spain) irinsu Al-Baji da Ibnu Abdilbarri suna ganin za a iya bayarwa ga wadanda bauren abinci ne a wurinsu. Imamul Baji ya ce, “Abin da yake mafi daidai a wurina shi ne baure nau’i ne na abinci. Don haka za a fitar masa da zakka, riba kuma zata iya shiga cinikayyar da shi, wadanda suke cinsa za su iya fitar masa da zakkar fidda-kai”- .-(Al-Muntaka na Baji:2/171; Al-Kafir na Ibnu Abdilbarri: sh/100; da Al-Jami’u Li Ahkamil Kur’an na Kurdubi: 7/103).

قال الإمام الباجي:”والصواب عندي أنه من الأقوات وأن تجزئ فيه الزكاة والربا ويخرجه في زكاة الفطر من يتقوته”.

A zamanin yanzu zamu dauki wannan ruhusar a kan kayan abinci da suka shafi taliya da macaroni da indomine da sauransu, cewa a kimanta abin da zai iya isa kwano daya a bayar.

vi- Duk da an ruwaito cewa shi Imamu Malik ba ya ganin za a fitar da zakkar fidda-kai a gari, amma wasu daga cikin malaman Mazahabin Malikiyyar kamar irin su Ibnu Habib da Asbag da sauransu suna ganin za a iya fitar da gari wanda zai daidai da sa’i guda.-(Ikdul Jawahirus Saminah na Ibnu Shash al-Khallal:1/219). Ma’anar wannan maganar tasu shi ne wanda yake da garin samovita da ko garin fulawa da sauran irinsu zai iya fitar da su a matsayin fidda-kai.

v-Imamus Sawi, daya daga cikin hamshakan malaman Mazahabin Malikiyya na daga baya, ya duba wannan mas’ala da idon basira sai ya yi bayanai da suke dada tabbatar da halascin a karbi kima. A daidai inda ake cewa sai wadannan kayan abinci guda tara ko goma ne kurum za a fitarwa da zakka, sai ya ce, “Amma magana mafi bayyana ita ce idan an bayar da kudi zakkar ta yi. Saboda ana samun toshe bukatar mabukaci a wannan rana da kudin”. -(Bulgatus Saliki na Assawi:1/438)

قال الصاوي:”فالأظهر الإجزاء لأنه يسهل بالعين سدّ خلته في ذلك اليوم”

5- Wadansu hadisai sun bayyana hikimar shar’anta wannan zakka ta fidda-kai shi ne tausasawa mabukata da wadatasu ga barin yin roko a wannan rana. Abdullahi bn Abbas ya ruwaito cewa Manzon Allah ya farlanta fitar da zakkar fidda-kai don tsarkake mai azumi daga siriri da maganganun batsa. Sannan kuma don ciyarwa ga maiskinai (mabukata).

Wanda ya bayar da ita kafin sallar idi, to an karba. Wanda kuwa ya bayar da ita bayan sallar idi, to ta zamo sadaka kurum kamar sauran sadkoki”-(Abu Dawud, L:408)

Wannan hadisin ya bayyana alfanu guda biyu da za a samu ta hanyar yin zakkar fidda-kai. Shi mai azumi a tsakakeshi. Su kuma mabukata a yalwata musu a wannan lokaci. Don haka ciyar da mabukatan wata babbar manufa ce.

Annabi (S.A.W) ya nuna a bayar da abinci shi ne asali. A zahiri kuma idan ciyarwar zata zamo sai dai a basu kudin su nemi abinci su saya, shi ma ya yi.

Idan an yi la’akari, akwai kasashe irin na Turai da za a ga samun zallar kayan abinci irinsu alkama da gero da dawa da sauransu yana da wahala ga mazauna birane, irin wadannan ba laifi suma su bayar da kudade ko wata kima.

6- Bayar da kima ko canza wani abu da wani abu da zai fi alfanu a irin wadannan hidimomi na al’umma ba wai wani sabon abu ba ne. Domin ga ruwayar da Mu’azu bn Jabal ya je Yaman karbar zakka ko jiziya -kamar yadda Dawus bn Kaisana ya ruwaito daga wurinsa, yana cewa da mutane Yaman, “Ku bani yadi ko gwado a maimakon sha’iri da gero. Wannan zai fiye muku saukin bayarwa. Sannan kuma sahabban Annabi (S.A.W.) a Madina zasu fi son haka”-(Bukhari ya kawo shi a Ta’aliki. Dawus bai hadu da Mu’azu ba. Duba Fat’hul Bari:3/311).

Imamul Bukhari da wasu malaman suna kafa hujja da wannan ruwaya a kan halascin a duba masalaha wajen fitar da asali kayan abinci ko kuma kima.-(Al-Majmu’u na Nawawi:5/429; Fat’hul Bari na Ibnu Hajar:3/312).

Ibnu Habib daga cikin manyan malaman Malikiyya na farko ya bada fatawa irin wannan dangane da wanda zai bada zakkar kudi, sai ya ga abinci ya fiyewa mutanen da za a bawa. Ya ce sai ya basu abinci a maimakon kudin. Ya kara da cewa, “Ya fitar a kayan abinci domin saukakawa mabukata a lokacin da mutane suke da bukatar abincin. Idan ya zamo yana wahala, ba a samunsa da sauki-(Al-Bayan Wat Tahsil na Ibnu Rushd-kakan:2/512)

قال ابن حبيب:”…أن يجب عليه عين فيخرج حبا-إرادة الرفق بالمساكين عند حاجة الناس إلى الطعام، إذا كان عزيزا غير موجود”.

7-A cikin hadisin da Sayyadin Abubakar ya bayyana yadda nisabin zakka yake na kudi da na kayan noma da ya zo na dabbobi sai ya ce, “Wanda zakkarsa take ya bayar da rakuma ‘yar shekara biyu amma ba shi da ita, sai dai yana da ‘yar shekara uku, to za a karba. Sai kuma mai sa’i (wakilin gwamnati a karbar zakkar) ya bashi dirhami ishirin ko akuyoyi guda biyu”.-(Bukhari:3/311-312-Fat’hul Bari).

Idan an yi la’akari za a ga an halatta bada kima a nan. Shi ya sa wasu hamshakan malamai irinsu Abu Ubaid suka ce ba laifi idan bukatar bada kima ya taso a bayar koda kuwa a ainihin zakka ne ma baki daya. –(Al-Amwal na Abu Ubaid:sh/458).

Idan an bayar a babbar zakka, to ina ga zakkar fidda-kai!

8-Manyan malaman Mazahabin Malikiyya irisnu Ibnu Abi Hazim da Muhammaad bn Dinar da Ibnu Wahad da Asbag suna ganin da mutum zai yi gaban kansa ya fitar da zakka maimakon ya bayar da kayan abinci ko dabbobi (a babbar zakka fa kenan), sai ya bayar da kudi, suka ce ya isar masa. Duk da dai ba a so ya yi hakan ba tun farko. Ibnu Rushd-Kakan ya karfafi wannan magana da cewa it ace magana mafi bayyana.-(Hashiyatud Dasuki:1/499 da 502; Hashiyatur Rahuni Ala Sharhil Mukhtasar:2/324-330; Ikdul Jauharil Samin na Ibnu Shad: sh/85).

9- Idan muka duba sauran malamai masu wannan ra’ayi na fitar da kima da kudi a zakkar fidda-kai zamu ga akwai Manyan Tabi’ai irinsu Hasanul Basari da Umar bn Abdul’aziz da Abu Is’haka Assabi’i da sauransu da suke da ra’ayin. Ga kadan daga cikin bayanansu:

i-Daga Hasanul Basari ya ce, “Idan mutum ya bayar da kudi (dirhami) a zakkar fidda-kai, ya isar masa”-(Al-Amwal na Humaidu bn Zanjawaih, L:2454)

عن الحسن قال:”إذا أعطى الدرهم من زكاة الفطر أجزأ عنه”

ii-Abu Is’haka Assabi’i ya ce, “Na riskesu (yana nufin Sahabbai da Tabi’ai) suna bayar da kudi a kimar abinci a zakkar fidda-kai”-(Musannafu Ibnu Asi Shaibah:3/174).

10-A Mazahabin Abu Hanifa da Imamu Sauri da Is’haka bn Rahawaihi da sauransu duk suna halatta bada kima. Ba wai a zakkar fidda-kai kawai ba. A duk abin da ya shafi kaffara da bakance da sauransu.-(Al-Mabsud na Assarkhasi:3/113-114; Umdatul Kari na Al-Aini:9/8)

 A dunkule, fitar da abinci shi ne asali. Kuma mutum ya yi kokari ya duba mutane da suke da bukatar abincin ya basu. Amma idan kuma ya yi la’akari da bukatar bada kima da kudi sai ya bayar a inda ake da matsananciyar bukatar hakan. Shehul Islam Ibnu Taimaiyya ya yi bayani irin wannan hali da cewa, “Ya halatta a fitar da kima a zakka a inda ba za a iya kaucewa bukata da masalahar yin hakan ba. Kamar a ce ya sayar da kayan gonarsa, a irin wannan hali sai ya bayar da dirhami goma ya isheshi. Ba sai an dora masa nauyin sai ya sayo kayan noman ko alkamar ba domin ya riga ya tallafawa mabukacin da kansa. Imamu Ahmad bn Hanbal ma ya fada halascin yin hakan baro-baro. Wani misalin kuma a ce akuya zai bayar a zakkar shanu, amma ba shi da akuya. A nan fitar da kimar ya wadatar da shi, ba sai an kallafa masa ya tafi sayo akuyar ba. Ko kuma su wadanda suka cancaci a basu zakkar su nemi a basu kimar su da kansu saboda ta fiye musu. Wannan ma ya halatta”-(Majmu’ul Fatawa na Ibnu Taimiyyah:25/82-83; Al-Ikhtiyaratul Fikihiyya na Ibnul Lahham: sh/103)

Allah ya bamu sa’a da dacewa a duniya da Lahira.

Farfesa Ahmad Murtala, shi ne shugaban Sashen Nazarin Ilimin Addinin Musulunci na Jami’ar Bayero dake Kano.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Gaskiya Kwankwaso ya nunawa Ganduje halasci – Bello Sharada

Published

on

Na saurari jawaban da Sanata Rabi’u Musa  Kwankwaso ya yi a gaban ‘yan jaridar Aso Rock jiya. Magana ta gaskiya a duniyance, Kwankwaso ya nuna wa Dr Abdullah Ganduje halasci na rayuwa da zamantakewa. Amma siyasa ta lalata al’amura a tsakaninsu. Daga abin da na rairaiyo a shekara 24 tun daga 1999 zuwa 2023  na rayuwa a tsakanin Kwankwaso da Ganduje, Kwankwaso da zuciya guda yake tafiya da Ganduje, shi kuma Ganduje likimo ya yi wa Kwankwaso.

Sabanin da ke tsakaninsu kuma, tsarin Kwankwasiyya ne haka. Kwankwasiyya da Kwankwaso Danjuma ne da Danjummai.  Da gangan Ganduje ya ki ragawa Kwankwaso, haka zalika ta hannun Abba K Yusuf, Kwankwaso ba zai ragawa Ganduje ba. Dole sai ya biya farashi mai tsada. Maganar gaskiya a mulkin shekara takwas 2015-2023 na Ganduje zai yi wahala ya kubuta a hannun mutanen Kano da hannun ‘yan Kwankwasiyya. Kuma ba shakka Ganduje zai samu karancin tausayawa. Mutane da yawa za su sha wahala a sakamakon yadda Ganduje ya yi mulki, Abba K Yusuf yake son ya yi nasa mulkin.

Cikin shekaru 24 na mulkin farar hula da muke ciki, an ga mulkin Kwankwaso da Shekarau da Ganduje, zamu ga mulkin Abba K Yusuf in Allah ya nufa da rai da lafiya. Lallai gwamna Kwankwaso na Abba ya bi sannu-sannu. Kwankwaso ya sani nasarar cin zabe ba shi ne  lasisi na Kwankwasiyya tayi duk abin da ta ga dama a Kano ba. Cikin mutanen da suka yi rajistar zabe su, miliyan biyar da dubu dari tara  (5, 921,370) da kuma mutanen Kano gaba daya su kusan miliyan 15 zuwa 20, wanda suka zabi Kwankwasiyya mutum  miliyan daya NE kacal da dubu 19 (1,019,602 ). Akwai mutane dubu dari tara da hamsin da bakwai da basu zabi Kwankwasiyya ba (957,408)  A tsakanin Kwankwasiyya da sauran mutanen da suka je zabe bambancin kuri’a dubu 68 ce.

Duk aikin da za a yi kada a kalli Ganduje da Goggo da ‘ya’yanta da Dan Sarki masu APC, a kalli mutanen Kanon da wajen Kanon da Najeriya.

Bello Muhammad Sharada,
Mai sharhi ne kan al’amuran yau da kullum

Continue Reading

Hausa

Shugabannin Fulani sun goyi bayan takarar Tinubu

Published

on

Aminu Abdullahi

 

 

Shugabannin Fulani wato (Ardo) daga sassa daban-daban na Najeriya sun jaddada goyon bayansu ga dan takarar jam’iyyar APC Sanata Bola Ahmed Tinubu a wani taro da suka gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar lahadi.

A taron da suka yi tare da hadin gwiwar Kungiyar Sabuwar Arewa wato “Arewa New Agenda” shugabannin sun yi alkawarin yin amfani da ‘yan kungiyar 33,661 wajen tattaro sauran ‘yan uwansu Fulani domin su zabi Sanata Bola Tinubu.

A lokacin da yake nasa jawabin bayan an kammala al’adar Fulani ta rabon goro ga mahalarta taron, shugaban Kungiyar Aliyu Liman Bobboi ya ce raba goron da aka yi yana nufin shugabannin za su koma gida su isar da sakon shawarar da aka yanke a wajen taron zuwa ga mabiyansu.

Ya kara da cewa taron an gudanar da shi ne domin su nuna wa duniya goyon bayansu ga Tinubu saboda sun yarda, sun kuma yi amanna da cancantarsa, suna kuma masu adduar samun nasara a zabe mai zuwa.

Ya kara da cewa Ardo a matsayinsu na shugabanni suna da ta cewa sosai akan wanda mutanensu zasu zaba, kuma suna da yakinin cewa magoya bayan nasu za su yi ma su biyayya.

Liman ya yi nuni da makusanta shakikai dake tareda Tinubu kamar Gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje, Abubakar Badaru na jigawa, tsohon shugaban EFCC Malam Nuhu Ribadu, da sauran manyan Fulani yace wannan na nuni ga yadda Tinubu ya dauki kabilar ta Fulani da muhimmanci.

Kungiyar ta shuwagabannin Fulani ta kuma bawa Tinubu sarautar Barkindo.

Gwamnan jahar kano Abdullahi Umar Ganduje da yake bayani ya yi tsokaci akan irin bajinta da kwarewa da kuma cancantar Tinubu da ya shugabanci Najeriya. Ya kuma kara da cewa Fulani a matsayinsu na kabila dake fuskantar barazana a sassa daban-daban, suna bukatar zabar shugaban da zai iya basu kariya.

Ganduje ya kara da cewa suna nan kan kokarin samarwa Fulani da wani tsari wanda zai bunkasa hanyoyin kiwo a duk fadin kasar nan.

A nasa bayani dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Sanata Tinubu ya yi tsokaci akan irin kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da mahaifiyarsa a bangare daya da kuma Fulani a dayan bangaren. Ya nuna cewa alakarsa da Fulani amana ce ta dindindin.

Ya kara jaddada niyyarsa ta samarwa Fulani hanyoyin kiwo na zamani da za su kawo cigaba da kuma yalwa ba tare da tsangwama ba.

Tinubu ya kara da cewa bai taba tsammanin zai hadu da bafulatanin da ya fi shi jin yaren yarbanci ba sai gashi yau ba zato ba tsammani ya hadu dasu. Ya ce wannan abun a yaba ne.

“Wannan itace irin Najeriyarda muke bukata, kasa daya al,umma daya.  Ina mai tabbatar maku idan da zamu kasance anan tsawon sa,o,I biyar iyakacindai zancenda zakucigaba da ji daga gareni kenan.  Ina mai matukar mika godiya da gareku.

“Tabbas makiyayan Najeriya na fama da matsaloli dabban dabban amma ina mai tabbatar maku da cewa munada tsari na musamman da zai magance wudannan matsalolin,’ a cewar Tinubu.

A nasa jawabin Malam Nuhu Ribadu ya bayyana Tinubu a matsayin mutumin da ya cancanta, ya dace wanda kuma zai iya kawo ci gaba mai dorewa ga kabilar ta Fulani.

Ya kuma yi godiya ga goyon bayan da suka bashi tareda alkawarin ba zai ba su kunya ba.

Continue Reading

Hausa

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, Baƙon Shehu Maghili

Published

on

Magaji Galadima

 

 

A ranar Litinin 12 ga watan Disamba 2022 gwamnatin ƙasar Aljeriya ta aiko da wani jirgi na musamman domin ya ɗauki mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zuwa ƙasar ta Aljeriya domin halartar taron duniya na musamman don tunawa da rayuwa da kuma aiyukan shahararren malamin addinin Musulunci sharifi kuma masanin falsafa  wato Shehun malami Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na goma sha biyar. 

Jigin ya tashi daga Kano da karfe 9:45 na safe. A cikin waɗanda suka samu alfarmar raka Sarki wannan tafiya akwai Sarkin Dawakin Tsakar-gidan Kano Alhaji Ahmad Ado Bayero hakimin Kumbotso da Ambasada Ahmad Umar Ɗanmalikin Kano da Dakta Ibrahim Ɗahiru Bauchi wanda ya wakilci Sheikh Ɗahiru Bauchi da Malam Isa Sanusi Bayero da Dakta Lawi Atiku Sanka da kuma ni Magaji Galadima Kachallan Kano, sannan sai wasu malamai da sharifai na Kano da kuma fadawa hadiman Sarki.

Jirgin ya ɗan yada zango a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar inda ya ɗauki Sultan na Agadas da Sarkin Sharifan ƙasar Nijar da sauran malamai da muƙaddamai da malaman jami’a. Sarkin Kano da ‘yan tawagarsa sun sauka a Aljiyas babban birnin Aljeriya da misalin karfe 5:00 na yamma inda manyan ministoci da jami’an gwamnati dana diflomasiyya da kuma manyan malamai suka taryi mai martaba Sarki da tawagarsa. Daga nan akayi jerin-gwano aka raka Sarki masaukinsa.

A rana ta biyu wato Talata Sarki da ‘yan tawagarsa suka fita zuwa wajen taron ƙasa da ƙasa da aka shirya domin tunawa da shahararren malamin addinin musulunci masanin falsafa kuma sharifi wato Shehu Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na sha biyar kuma har ya zo Kano zamanin Sarki Muhammadu Rumfa.

Al-Maghili ya zauna a Kano tsawon lokaci kuma ya bijiro da sababbin tsare-tsare ma su muhimmanci a fadar Kano, kana kuma ya yi rubuce-rubuce akan ibada da hukunci, sannan ya rubuta wani kundi da ya zama daftari na jagorar duk wani sarki na Kano da ma nahiyar yammacin Sudan.

Taron an shirya shi ne a babban ɗakin taro na ƙasar dake birnin Aljiyes.  A ranar buɗe taron Sarkin Kano da tawagarsa sun isa wajen da misalin karfe 9;00 na safe amma sai aka kaishi wani ɗaki ya zauna a kauwame har sai da ɗakin taron yayi cikar kwari sannan aka shigar dashi.

Toh dama an ɗauki makwanni ana ta yaɗawa a kafafen labarai cewa ƙasar ta Aljeriya zata karɓi bakuncin wani ƙasaitaccen Sarki mai alfarma da daraja daga garin Kano a Nijeriya, don haka mutanen ƙasar duk sun zaku suga wannan ƙasaitaccen Sarki. Saboda da haka yana shiga ɗakin taron sai duk aka tashi tsaye waje ya kaure da sowa da tafi, mata kuma na rabka guɗa, su kuma ‘yan badujala suka goce da wani irin take na musamman da ake kaɗawa mashahuran mutane in sun shigo wajen taro.

An ɗauki tsawon lokaci kafin a samu natsuwa lamurra su koma daidai sannan mai martaba Sarkin Kano figinai suka yi sayi ya zauna aka gyara aka kimtsa sannan aka fara gudanar da taro.

Daganan ne kuma sai aka fara jawabai, babban ministan harkokin addini na ƙasar shine ya wakilci shugaban ƙasa kuma yayi jawabin maraba ga mahalarta taron kana yayi godiya ta musamman ga Sarki Aminu Bayero a madadin shugaban ƙasa da al’ummar ƙasar baki ɗaya. Shima Sarkin na Kano  yayi jawabi inda ya nuna farin ciki da godiya ga gwamnati da jama’ar ƙasar baki ɗaya saboda kyakkawar taryar da aka yi masa, ya kuma isar da gaisuwar jama’ar masarautar Kano da Nijeriya baki ɗaya a garesu.

Sarkin ya yaba da hangen nesan waɗanda suka assasa wannan taro na tunawa da Shehu Maghili wanda yace yafi cancanta a kira shi da Bakano maimakon dan Aljeriya saboda da dalilai da dama. Ya baiyanawa mahalarta taron cewa a yanzu haka a cikin birnin Kano akwai unguwar Sharifai waɗanda asali jama’ar da suka zo Kano tare da Shehu Maghili sune ke zaune a wannan unguwa tun lokacin har zuwa yanzu, kuma shugabansu Sidi Fari shine Sarkin Sharifan Kano kuma yana da gurbin zama a majalisar Sarkin Kano.

A ƙarshen jawabin Sarki yayi godiya ga Allah wanda Ya ƙudura cewa a zamaninsa ne akayi wannan babbar hobbasa ta sake dawo da wannan tsohuwar alaƙa tsakanin Kano da Nijeriya da kuma ƙasar Aljeriya kamar yadda su Shehu Maghili suka shimfiɗa.

Daga nan kuma sai aka buɗe fage inda malamai da masana suka yita ƙwami akan tarihin rayuwa da rubuce-rubucen Shehu Maghili.

Bayan an tashi daga taron wannan rana ta farko, sai mutane suka yanyame Sarkin Kano, malamai da jami’an gwamnati da baƙi daga sauran ƙasashe kowa burinsa shine ya samu ya ɗauki hoto da Sarkin Kano.

Bayan an fito waje ma haka har zuwa inda ya shiga mota. Mu ma ‘yan kwarakar Sarki da kyar muka yakice ‘yan jarida masu son jin kwakwaf domin yawansu babu lokaci da zamu warware musu zare da abawa. Koda muka isa masauki sai muka tarar ashe tuni wasu jama’ar sun yi kwamba suna jiran isowar Sarki domin su samu su gaisa kuma su ɗauki hoto da shi.

 

Bayan ya shiga ɗaki kuma sai manyan malaman ƙasar su kuma suka yi layin shiga suna yiwa sarki addu’a har saida rana tayi gora sannan jami’an tsaro suka tare mutane suka hana su shiga don a kyale Sarki ya huta.

A rana ta biyu mai martaba Sarki da tawagarsa ya sake komawa wajen taron inda malamai suka ci gaba da gabatar da takardu.

Bayan anyi hutun zango na farko sai mai martaba Sarki ya fita domin kai ziyara ofishin jakadancin Nijeriya dake kasar ta Aljeriya.

Jakadiyar Nijeriya Hajiya Aisha Muhammad Garba ta taryi Sarki da tawagarsa kuma anyi jawabai masu muhimmanci.

Da maraice kuma har ila yau sai Jakadiyar ta shiryawa mai martaba sarki wata liyafar alfarma a gidanta inda aka gaiyaci ‘yan Nijeriya mazauna ƙasar Aljeriya da kuma wasu malamai daga Nijeriya.

A rana ta uku kuwa mai martaba Sarki ya halarci bikin rufe taron kuma abin ya ƙayatar ƙwarai musamman yadda Sarkin Kanon ya zama tauraro a wajen taron domin dai hankalin kowa na kansa tun daga farko har i zuwa lokacin da aka ja labulen rufe taron.

Da yammaci kuma sai shugaban ƙasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya gaiyaci Sarki Aminu zuwa fadarsa inda suka zauna suka yi zantuka na girma. Shugaban ƙasar yace yayi murna matuƙa da karɓar baƙuncin Sarkin, ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar tasu tana sane da tarihin masarautar Kano da rawar da Shehu Maghili ya taka wajen bunƙasa al’adu da addinin Musulunci a birnin Kano.

Shugaba Tebboune yace Sarkin Kano a wannan ziyara shi baƙon Shehu Maghili ne, duk da yayi wafati fiye da shekaru 600, wannan ziyara ta Sarki lallai Shehu Maghili shine sila.

Shi kuma a lokacin da yake maishe da jawabi Sarki Aminu yayi godiya ga Allah da Ya bashi ikon amsa gaiyatar shugaban ƙasar da kawo wannan ziyara, ya yabawa gwamnatin ƙasar Aljeriya saboda ɗawainiyar ɗaukar nauyin wannan taro mai muhimmanci.

Daga nan kuma sai yayi kira ga shugaban na Aljeriya da su haɗu su farfaɗo da hulɗar cinikayya da kasuwanci tsakanin Kano da Aljeriya wanda yace zai taimaka wajen ƙara yauƙaƙa danƙon zumunci tsakanin nahiyoyin biyu. Baya ga wannan kuma da yake ance lokacin iska ake cin ɗan jinjimi sarkin ya bukaci gwamnatin ƙasar ta Aljeriya da ta bawa ɗaliban jihar Kano tallafi na guraben ƙara ilmi a fannoni dabam-daban a jami’oin ƙasar inda shugaban ƙasar nan take yayi wuf yace ya amince da wannan shawara kuma yana jira in Sarki ya koma gida,  ya tsaro jadawalin yadda duk yake so ayi , su kuma in Allah Yaso zasu aiwatar. a nan dai akayi muwafuƙa duk shawarar tasu tazo daidai.

Daga nan suka yi bankwana cikin farin ciki da girmama juna.

A rana ta hudu mai martaba Sarkin Kano tare da wasu daga cikin ‘yan tawagarsa sun ziyarci garin Ain-Madhi wato ainihin garin da aka haifi Maulana Shehi Ahmadu Tijjani (RA) wanda ya kafa ɗarikar Tijjaniyya.

Sarkin ya ziyarci muhimman wuraren tarihi a garin sannan ya gana da manyan malamai da sharifai zuriyar Shehin inda suka yiwa Sarkin da Kano da Nijeriya  addu’oi na musamman.

A rana ta biyar Sarki ya kammala ziyarar kamar yadda aka tsara, don haka sai ya karyo linzami zuwa gida. Manyan jami’an gwamnati da malamai da kusoshin diflomasiyya da kuma jakadiyar Nijeriya sune suka raka mai martaba Sarki zuwa filin jirgin sama, akayi ban kwana kowa na cike da farin ciki.

Ko shakka babu wannan ziyara da mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayero ya kai jamhuriyyar dimokuraɗiyyar ƙasar Aljeriya ta buɗe wani sabon babi na dangantaka mai ƙarfi tsakanin ƙasar da kuma Nijeriya. Wannan tagomashi da Sarkin Kano yake samu a duk inda yaje lallai abin godiya ga Allah ne ga duk mai ƙaunar ci gaban jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Ɗadin daɗawa gashi har mai martaba Sarki yayi hobbasa har shugaban ƙasar na Aljeriya yayi alkawarin baiwa ɗaliban jihar Kano guraben ƙaro ilmin jami’a kyauta da shiryawa malamai da limamai kwasa-kwasai na ƙara sanin makamar aiki, sannan a waje ɗaya kuma shugaban na Aljeriya ya bada umarni cewa ayi duk abinda za ayi don ganin kwance duk wani daurin Gwarmai don sassauta hulɗar kasuwanci ga ‘yan kasuwar Nijeriya masu sha’awar zuwa Aljeriya.

Mai martaba Sarki ya samo nasarar da ba a taɓa samowa ba a bigiren dangantakar  siyasa ko diflomasiyya, don haka babu abin yi da ya wuce mu yiwa Allah godiya da muka samu Sarki wanda addu’ar magabata da kyakkawar mu’amala  da nagartaccen lamiri suke haskaka masa turbar tafiyarsa, ba kuskunda ba jalla-kujalle.

Fatanmu shine Allah Mabuwayi Ya kara wa Sarki lafiya da jimiri da jinkiri, yadda yake fafutukar samawa al’ummar Kano tudun dafawa, shima Allah Ka dafa masa.

Yadda Sarki ya ɗauko saitin gwadabe tun ba a je ko’ina ba a tafiyar yayi nuni da cewa nan da ɗan lokaci zai ginawa Kanawa rijiya gaba dubu wacce ko da an shekara saran  ruwa toh sai tamfatse.

A laaaafiya baƙon Shehu Maghili !!!

Magaji Galadima
Kachallan Kano
Disamba 25, 2022.

 

Continue Reading

Trending