Connect with us

Hausa

Mata ta babbaka mijinta a Kano

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Wata mata mai suna Khadija Ahmad ta babbake mijinta Bashir Ahmad da wuta a unguwar Gaida da ke karamar hukumar Kumbotso cikin birinin Kano.

Kano Focus ta ruwaito al’amarin ya faru ne da yammacin ranar Talata bayan da matar ta faki idon mijinta ta cinnan masa wuta a daki.

A cewar shaidar gani da ido Usman Ibrahim Usman matar ta faki idon mijin ne bayan da ya shiga wanka, inda ta hada makamashi a dakinsa ta kuma yayyafa fetur.

Ya ce bayan fitowarsa daga wanka ne kuma ya shiga dakin nasa, inda nan da nan ta kara wani fetir din ta cinna wuta ta kuma jawo Kofar ta rufe.

Sai dai cikin ikon Allah ya yi kokarin balla Kofar duk da wutar da ke cin jikinsa.

Ya kara da cewa bayan ta konashi ne kuma ta fito waje tana ihun neman daukin jama’a.

Hakan ta sanya jama’a suka kai dauki domin kubutar da shi daga wutar da ke cinsa.

Sai dai bayan da aka kaishi asibiti ne kuma ya bayyana cewa ga abinda matar tasa ta yi masa.

Hakan ya sa ta nemi ta gudu sai dai tuni jami’an yan sanda suka kamata domin fadada bincike.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Zakka a yau tana wajaba ne da kimar gwal kawai

Published

on

 

Farfesa Ahmad Murtala

 

Bismillahir Rahmanir Rahim
Allah ya yi Salati ga Annabinmu Muhammad da Alayensa da Sahabbansa baki ɗaya.

Bayan haka, a yammacin yau Juma’a 26 ga Ramadan, 1445 H. wanda ya yi daidai da 05 ga April, 2024 zan ams tambayar da wasu ‘yan uwa suke ta aikowa da bugo waya a kan amfani da nisabin azurfa a wajen fitar d zakka. Wani ma da larabci ya rubuto cewa , “Shin wajen fitar da zakka ya halatta na fitar da kimar takardun kudi ta hanyar azurfa maimakon gwal? Allah ya saka da alheri”.

“هل يجوز أن أقيس الأوراق المالية بالفضة في الزكاة بدل الذهب ؟ جزاكم الله خيرا”
A kan wannan tambaya, aka rubuta wannan bayani. Allah ya bamu sa’a da dacewa.

1-Gwal wanda aka fi sani a cikin littafai da sunan (Dinare) da azurfa wadda aka fi sani da sunan (Dirhami), su ne kudaden da aka yi amfani da su a lokacin Annabi (S.A.W) da lokacin Sahabbai da Tabi’ai har zuwa karni na sha takwas na Miladiyya, a lokacin da kudaden takarda suka fara karfi a hannuwana mutane.

Ayoyi da hadisai duk sun tabbatar da gwal da azurfa a matsayin kudaden da ake amfani da su tun lokacin Annabi (S.A.W) a matsayin kudaden da ake fitar musu da Zakka, ake biyan sadaki da diyya da su, ake yin sauran amfanin yau da gobe da su. Don haka, maganar wasu malamai da suke cewa ba bu gwal a lokacin Annabi (S.A.W) sai dai azurfa, ko kuma su ce ba a sami wani nassi fayyatacce wanda Annabi (S.A.W) ya fadi gwal ba, wannan wata magana ce mara tushe. Domin Allah Madaukaki cewa ya yi, “Wadanda suke taskance gwal da azurfa, ba sa ciyar da su a tafarkin Allah, to ka yi musi bushara da azaba mai radadi”.-(Taubah: 34).

قال الله تعالى: “والذين يكنزون الذهب والفضة ولا ينفقونها في سبيل الله فبشرهم بعذاب أليم”.

A cikin hadisai ma duka biyun bayani a kan su ya zo. Ga kadan daga ciki:

i- Abu Sa’idul Khudri (R.A.) ya ce, “Ɓa bubu sadaka/Zakka a duk abinda yake kasa da ukiyya biyar-(ukiyya daya Dirhami arba’in ce).

عن أبى سعيدٍ الخدريِّ رَضِيَ اللهُ عنه، أنَّ النبيَّ صلَّى الله عليه وسلَّم قال: “ليسَ فيما دونَ خمْسِ أواقٍ مِنَ الوَرِق صَدَقةٌ”.

ii- Daga Aliyu bn Abi Dalib (R.A.) ya ce Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Na yi muku afuwa a fitar da sadaka/zakka a dawakai da bayi. Amma ku kawo sadakar azurfa. Duk Dirhami na azurfa, a bayar da Dirhami ɗaya. Amma ba bi Zakka ga Dirhami dari da casa’in da tara. Suna kaiwa dari biyu, sai a bayar da Dirhami biyar”.

عن عليٍّ رَضِيَ اللهُ عنه، قال: قال رسولُ اللهِ -صلَّى الله عليه وسلَّم-: “قد عفوتُ لكم عن صدقَةِ الخَيلِ والرَّقيقِ، فهاتوا صدقةَ الرِّقَةِ: مِنْ كلِّ أربعينَ درهمًا درهمًا، وليس في تِسعينَ ومئةٍ شيءٌ، فإذا بلغت مئتينِ ففيها خمسةُ دراهِمَ”.

iii-Anas bn Malik (R.A) yana cewa, “Umar ya dora ni a kan kula da Sadaka da Zakka. Ya umarce ni da na rika karbar rabin Dinare daga Dinare ishirin”-(Muhalla na Ibn Hazam: 6/67).

عن أنس بن مالك -رضي الله عنه- قال: “ولاني عمر على الصدقات، فأمرني أن آخذ من كل عشرين دينارا نصف دينار”.

Malamai masu yawa sun hakaito Ijma’i da haduwar malamai a kan wannan magana. Ga kadan daga ciki:

a-Imamu Malik ya ce, “ Sunnar da ba bu wani sabani a kanta a wurinmu ita ce cewa Zakka tana wajaba ne a Dinare ishirin kamar yadda take wajaba idan take Dirhami dari biyu”-(Muwadda Malik:1/246).

قال الإمام مالك-رحمه الله-: “السنة التي لا اختلاف فيها عندنا أن الزكاة تجب في عشرين دينارا عينا، كنا تجب في مائتي درهم”.

ii-Imamu Shafi’i yana cewa, “Ba bu wani sabani cewa ba bu Zakka a kan gwal sai ya kai Dinare ishirin”.-(Al-Ummu na Shafi’i:2/34).

قال الشافعي-رحمه الله-: “لا أعلم اختلافا في أن ليس في الذهب صدقة حتى تبلغ عشرين”

iii-Imamu Abu Ubaid Alkasim bn Sallam ya ce, “Wannan nisabin ba wani sabani a tsakanin Musulmi a kansa”. Ya kara da cewa, “Asalin Sinare shi ne a daidaidaita guda daya da Dirhami goma”-(Al-Amwal na Abu Ubaid, shi/409 da 519)
قال الإمام أبو عبيد-رحمه الله-: “فهذا لا اختلاف فيه بين المسلمين”. وقال أيضا: “أصل الدنانير أن يعدل الدينار بعشرة دراهم”.

An zo da wannan ne domin a tabbatar da cewa ana fitar da Zakka daga a gwal da Azurfa tun lokacin Annabi (S.A.W).

2-Domin a tabbatar da yadda za a fitar da zakkar da sauran abubuwan da suka rataya da kuɗin, malamai da masana daga baya sun duba nauyin kowanne daga cikinsu an san gwargwadonsa. Gwal dai sai ya kai giram tamanin da biyar (85). Wannan ba ya canzawa a haka tun jahiliyya har zuwan Musulunci sai dai in algush aka yi masa. Ita kuma azurfa ita ce lamari ya yake canzawa. Amma dai yawancin malamai sun tabbatar da cewa a lokacin Annabi (S.A.W.) giram dari biyar da casa’in da biyar (595), shi ne yake daidai da kimar dinare ishirin idan za a yi canji. Malamai sun tabbatar da cewa wannan ne kuma ma’aunjn mutanen Makka tun lokacin Annabi (S.A.W). Domin ya ce, “Ma’aunin nauyi, ana amfani da na mutanen Makka. Ma’aunin yawa kuma, ana amfani da na mutanen Madina”-(Sunanu Abi Dawuda, L:3340)
عن ابن عمر-رضي الله عنهما-قال قال رسول الله-صلى الله عليه وسلم-:” الوزن وزن أهل مكة والمكيال مكيال أهل المدينة”.

Wannan awo da shi ne mutanen kowace kasa zasu kimanta kudin kasarsu da yadda za a sayi gwal ko azurfa masu nauyin da aka ambata. Ana duba gwal ne da yake tsantsar gwal, wanda yake (99%) gwal, ba sirki.
Da zarar mutum ya san kudin gwal ɗaya ta hanyar masu sayar da gwal a garinsu ko ta hanyar duba internet, sai ya ninka kudin sau 85. Duk abinda lissafi ya kama shi ne nisabin zakka. Misali a yau 5 ga April, 2024 ana sayar da gwal mai matsayi na 24k a kan kudi N 93,492.58, sai a ce sau 85. Zai zamo N7,946,869.3. Wannan shi ne kudin zakka lissafin gwal a wannan rana. Zai iya canzawa tsakanin dare da rana ko cikin wasu ‘yan kwanaki. Amma dai ana so a gane yadda ake yin lissafin ne kurum.

Ta wannan hanyar ne yawancin Musulmi a kasashe daban suke fitar da lissafin Zakka. Masu Riyal ko Junaih ko Dollars ko Yen da sauransu, duk da wannan zasu lissafa zakkarau.
Ita kuwa azurfa, idan aka ce za a yi la’akari da wancan giram na lokaci Annabi (S.A.W), kudin giram dinta a yau (05th April, 2024) shi ne N 1,104. Sai a ce sau 595. Shi zai bada N 656,880
Abin la’akari a nan shi ne an sami nisabi biyu kenan. Na azurfa daban, na kuma gwal daban, wanda ba haka abin yake ba a lokacin Annabi (S.A.W.). Saboda haka akwai matsala s lissafi !

3- Tambayar da wadansu suke kawo wa a yanzu ita ce saboda mai ba za a koma kan azurfa a rika fitar da nisabin Zakka bisa awonta na giram 595 ba?!

Musamman ga gwal ya yi tsada sosai don haka ne ma nisabin zakkar ya tafi sama da miliyan bakwai har takwas da sauransu!

Wannan tunani ne mai kyau kuma kokari ne na samo wa al’ummar Musulmi mafita a cikin tsarin addinin Musulunci, ba daga wani wuri can a wajen sa ba.

Masu wannan ra’ayi zasu iya karfafa ra’ayin nasu da kasancewarsa mai sauki. Kuma kusan wadanda zasu fitar da Zakka zasu yawaita fiye da idan an yi la’akari da lissafin Gwal, wanda sai hamshakai ne mutum zasu fitar da ita!
Sai dai wannan ra’ayi a yadda yake din nan yana cike da dinbin kusakurai. A gaskiya a yanzu ba zai yiwu a yi aiki da shi ba. Saboda ra’ayin bai zauna daidai ba. Akwai sauran sinadaran ilimi da ake da bukatarsu kafin a yi la’akari da shi.

4- Yana da kyau a tuna da cewa Allah ya wajabtawa mai kudi da ya fitar da Zakka ya bawa talaka kamar yadda Annabi (S.A.W) ya fada cewa, “Ka fada musu cewa Allah ya wajabta musu fitar da sadaka/zakka daga dukiyoyinsu. Ana karbar ta ne daga masu kuɗin cikinsu, sai a mayar da ita ga talakawan su”.-(Bukhari, L:1425; Muslim).

عن ابن عباس-رضي الله عنهما-قال قال رسول الله-صلى الله عليه وسلم-: “فأخبرهم أن الله قد فرض عليهم صدقة تؤخذ من أغنيائهم فترد على فقرائهم”.

Wannan hadisin ya tabbatar da cewa masu kuɗi ne suke fitar da Zakka su bawa talakawa. Don haka wanda ya mallaki nisabi shi ne mai kuɗi. Wanda bai mallaki nisabi ba, ya fada cikin masu rufin asiri da talakawa!
Zakkar kuɗi da dabbobi da kayan abinci an ɗorawa mai kuɗi ne kawai, shi ne zai bayar da ita. Ba a ɗorawa talaka ya bayar da ita ba. Mai kudi da talaka sun hadu a bayar da zakkar Fidda-kai ne Kurum. Shi ya sa ma Annabi (S.A.W) da yake fadar hukumomin fitar da zakkar Fidda-kai ya ce, “Manzon Allah (S.A.W) ya wajabta zakkar Fidda-kai don tsarkakewa ga mai yin azumin daga sirri da batsa, da Ciyarwa ga miskinai. Wanda ya bayar da ita kafin sallar ido, ta zamo karba biyar zakka. Wanda kuma ya bayar da ita bayan an yi sallar Isha, to zamo sadaka kurim kamar sauran safakoki”.-(Sunanu Abi Dawuda, L: 1609)
عن ابن عباس -رضي الله عنه- قال “فرضَ رسولُ اللَّهِ -صلَّى اللَّهُ عليهِ وسلَّمَ- زكاةَ الفطرِ طُهرةً للصَّائمِ؛ منَ اللَّغوِ والرَّفثِ وطُعمَةً للمساكينِ، من أدَّاها قبلَ الصَّلاةِ فهيَ زكَاةٌ مقبولةٌ ومن أدَّاها بعدَ الصَّلاةِ فهيَ صدَقةٌ منَ الصّدقات”.

A nan an yi haka ne saboda miskini kasa yake da Fakiri shi ma Fikirin zai iya taimakawa da abinda yake da shi ga wani.

Muhimmin abu dai a nan shi ne ma’aunin talauci da arziki suna canzawa da canzuwar yanayi da mutane da lokaci da karfin hada-hadar kasuwanci da karfin da kudade suke da shi na sayan abubuwa. Wanda wani lokaci za a dauka cikakken mai kuɗi ne shi, sai zamani ya canza ko a wani wurin ya zamo shi ne talakan da za a bawa Zakka. Hakika a da can a shekaru masu yawa da suka wuce wanda yake da N 656,880, mutum ne mai tarin kudi, amma a yanzu talaka ne shi. Shi ma yana jira masu kudi su tallafe shi!
Za a gane haka bisa la’akari da tashin gwauron zabo da kayan masarufi suka yi ta yadda komai kudinsa ya ninka sau iya abinda mutum zai ji in ya je saya, zamu dada tabbatar da cewa wanda shekara ta kewayo masa ya zamo yana mallake da iya dubu dari biyar da saba’in, a gaskiya wañnan talaka ne da yake bukatar taimako, amma ba wanda zai fitar da Zakka ba. Masu ganin zai bayar da Zakka ba su tuna wannan ba. Su abinda suke kallon azurfa da kuma canjin ta a kasuwa. Amma ba su duba yadda kimar canji da yadda kudi suke a hannun mutane a yau suka canza ba. Daman kuma tarihi ya nuna cewa ana samun wannan juyin a azurfa.

5-Nisabin Zakka guda daya ne a lokacin Annabi (S.A.W) ba biyu ba. Domin Dirhami goma shi ne canjin Dinare daya. Don haka wanda yake da wannan, yana da kudi daidai da wanda yake da wancan. Haka abin yake har a lokacin Sahabbai da Halifofi. Sai daga baya aka fara samun juyawar abubuwa. Kimar azurfa ta fara hawa da sauka sosai. Wannan yana nufin wadanda suke so a dauki nisabin zakka a azurfa a yau kamar yadda ake daukar na gwal, za a sami nisabi biyu a kan maganarsu. Yin haka kuma ya sabawa abinda aka sani a tsarin Musulunci. Ba a taba bada nisabi kala biyu ba.

6-A yadda bayanai suka zo, kimar gwal bata cika canzawa sosai ba a tsawon tarihi. Malamai masana tattalin arziki a Musulunci sun tabbatar da haka. Ga guda biyu daga cikinsu:

A-Shaikh Abu Zahra yana cewa, “Idan ya zamo cewa Sinare sihirin shi ne gwargwadon abinda za a cutarwa da Zakka, bisa yadda Sahabbai suka ƙaddara akan yadda Annabi (S.A.W) ya a gwada a Dirhami, don haka zai yiwu a dauki dinare ishirin din su ne ma’auni na dindindin a kowane zamani. Saboda ita azurfa, kudi ne irin na ma’adani. Wato haka ce mutum da ake samun arha da tsada suna kaiwa da komowa a kanta. Amma gwal kuwa shi ne kudin duk duniya wanda ba a canzawa. Domin da shi ne ake ƙiyasta kimar komai har da ita azurfar. Don haka ne ba ma la’akari da wani abu. A matsayin ma’auni in ba gwal ba”.-(Attakafulul Ijtima’i Fil Islam, shi:71)
قال الشيخ أبوزهرة-رحمه الله-:”وإذا كانت عشرون دينارا هي مقدار الزكاة بتقدير الصحابة المبني على تقدير النبي -صلى الله عليه وسلم- في الدراهم، فإنه يسوغ أن تعتبر العشرين دينارا هي التقدير الدائم في كل العصور. ذلك، لأن الفضة نقد معادن، وهي سلعة يجري عليها الرخص والغلاء. وأما الذهب فهو العملة العالمية لا تتغير، وبها تقاس قيم الاشياء، ومنها الفضة. لذلك لا نعتبر مقياسا سواه”.

ii-Shaikh Muhammad Diya’uddini Rais shi ma ya ce, “Daga cikin tabbatattun abubuwa wadanda aka fada a baya zai bayyana gare mu cewa gwal shi ne tushen duk wani ma’aunin nauyi na kudi. Sauran abubuwan duka ana kimanta su ne a kansa. Saboda shi yana da sigar tabbatuwa ba tare da ya canza ba a zamani daban-daban”-(Al-Kharaju Wan Nuzumul Maliyyah Lid Daulal Islamiyyah: sh/373)
قال الشيخ الدكتور ضياء الدين الريس: “ومن الحقائق التي ذكرت سابقا تبين أن المثقال هو أساس الأوزان. فالوحدات الأخرى تقدر بالنسبة إليه. وذلك لما اختص به من صفة الثبوت في مختلف الأزمنة”.

An samu lokuta mabanbanta da yawa a tarihi wanda kimar azurfa take canzawa sosai, saboda amfani da ita a matsayin ma’aunin kudi ya ragu. Don haka, in ana so nisabin ya samu ta hanyarta, sai an yi ciko a kan yadda take. Wato sai ta fi giram 595 ta zamo daidai da kimar gwal, sannan ne za a fitar mata da Zakka.

Duka malaman Musulunci marubuta a kan Kuɗi da yanayin sa da kala-kalarsa da hawa da sauka na kima irin su Balazuri, da Makrizi, da Ibnu Khaldun da saurasu duk sun tabbatar da yadda azurfa take hawa take sauka, amma kimar gwal ba ta canzawa.-(Futuhul Buldan na Balazuri: shi/651-659; Al-Majmu’u na Nawawi: 5/500-503; Annukudul Kadimah na Al-Makrizi: shi/2-16; Al-Mukaddimah na Ibnu Khaldun: shi/322-326; Al-Khidadut Taufikiyyah na Aliyu Mubarak Basha: 20/42-48; Al-Kharaju Wan Nuzumul Maliyyah na Diya’uddini Rais: Shi/384)
Misali a karshe-karshen mulkin Umawiyyah sai da kimar azurfa ta sauka. Ya zamo sai an bada Dirhami goma sha biyu (12) ne zai yi daidai da dinare daya. Da tafiya ta yi tafiya a lokacin Abbasiyya, sai a ka samu a wani lokaci kimar ta koma Dirhami sha biyar (15) ga Dinare ɗaya. A shekara ta 399 H. lokacin Daular Fadimiyyah a Misra, abin ya lula da yawa, ya zamo sai an bayar da Dirhami talatin da huɗu zuwa da biyar (34-35) a canjin Dinare ɗaya. Daga baya aka ɗan sami sauki ta yadda Dirhami sha takwas (18) shi ne yake daidai da Dinare daya. –(Annukudul Kadimah Wal Islamiyyah na Al-Makrizi, shi/14).

A wancan zamani ana samun bangarori da sassan daular Musulunci da suke amfani da gwal fiye da azurfa kamar Kasar Misra da Sham. Can bangaren su Iraki da Farisa kuma sun fi amfani da azurfa fiye da gwal. Wannan ya sa inda suke fi amfani da gwal, sai aka riƙa samun kimar azurfa tana yin kasa a wurinsu. Kamar yadda ya faru a Misra a misalin da aka faɗa a sama kaɗan.
Ali Mubarak Basha ya kawo bayanai dalla-dalla yadda kimar gwal da azurfa suke canzawa tun farkon tarihin Musulunci har zuwa 1793M. Azurfa ita ce ta fi canzawa sosai daga gari zuwa gari, da zamani zuwa zamani da kuma mulkin sarakuna daban-daban. Ana samun wagegen bambanci a tsakaninsu. Abinda ya dada tabbatar da cewa kimar da aka rika dauka daga gwal/Dinare ita ce ta fi tabbas a tashon tarihin Musulunci.-(Al-Khidadul Taufikiyyah na Ali Mubarak Basha: 20/53-131).

A yau kuma, a wannan zamanin kimar azurfa ta sauka sosai a duniya. Bambancin da yake tsakanin kimar gwal sa ta azurfa ya ninku wajen sau goma sha biyar ko kasa da haka kadan ko sama da haka. Wannan kadai ya isa ya nuna bambancinsu da na lokacin Annabi (S.A.W).

Sannan wannan gibin ba wai a iya Nigeria ba ne kaɗai duk duniya ne. Za a samu kimar gwal ta zarta ta azurfa sosai. A ko’ina kuma wanda yake mallake da azurfar ba a daukarsa a mai kudi ko mai arziki, amma wanda yake da kimar gwal wannan a ko’ina mai kudi ne.

7-Malamai masana Fikihun zamani da tarihi kudi da hada-hadar da ake yi da su na zamani suna tabbatar da cewa yanzu ba za a yi amfani da azurfa/Dirhami ba a matsayin ma’aumin fitar da zakka. Saboda wadancan dalilai da aka kawo a sama. Ga kadan daga cikin bayanansu:
i-Irin wannan mas’alar da wasu suke kokarin sun kawo a yau, ta taba faruwa kusan sama da shekara dari da suka wuce a Kasar Misra. Shaikh Diya’uddini Rais ya yi bayanin yadda wani littafi Mai suna “Al-Fikhu Alal-Mazahibil Arba’ah” da aka buga a can Misra a 1939M. ya kawo hargitsi ta fuskar samar da nisabi kala biyu daban-daban; daya da awon gwal, shi ne mafi yawa. Dayan kuma bai kai wancan yawa ba saboda an yi shi da awon azurfa. Sai malamin ya ja kunne sosai tare da tabbatar da kuskuren wannan lissafin. Ya kara da cewa, “Ma’anar wannan kenan akwai nisabi guda biyu ga Zakka. Amma fa sun saba sosai. Daya daga cikinsu bai kai rabin dayan ba ma. Wannan kuwa ba shi ne makasudin hadisan Manzon Allah (S.A.W,) ba. Ba kuma shi ne makasudin Shari’abs Ai nisabi daya tak ake da shi. Shi ne wanda hadissan suka ba da gwargwadon sa ta hanyoyi guda biyu na daidaita. Su ne Dinare ishirin da kuma Dirhami dari biyu. Duk biyun abu daya, kudi daya ne. Domin ƙaddara nisabin zakka wajibi ne ya zamo gwal ko azurfa ko wani abin da an ba su ba amma mWanda ya yi daidai da su. Kima daya ce duk yadda kudaden suka bambanta. Kasancewar gwal a lokacin Annabi (S.AW), haka nan a wurin mutanwn Makka shi ne tushwn kudade, muna gain shi Gwale ko abinda zai zauna mazauninsu, ya yi aiki irin nasa, shi ya kamata a rike a matsayin ma’aunin kaddara kima”.-(Al-Kharaju Wan Nuzumul Maliyyah Lid Daulal Islamiyyah: sh/381)
قال الشيخ ضياء الدين الريس: “معنى ذلك أن هناك نصابين للزكاة، وهما متفاوتان كثيرا. أحدهما أقل من نصف الآخر. وليس هذا هو المقصود من أحاديث الرسول عليه السلام، ولا المقصود من التشريع. وإنما هناك نصاب واحد، قدرته الأحاديث بمبلغين متعادلين. وهما عشرون دينارا، أو مائتا درهم. وكانا شيئا وسعرها واحدا. فتقدير نصاب الزكاة يجب أن يكون واحدا من الذهب أو بالفضة أو من غيرهما -على حد سواء-. القيمة واحدة مهما اختلفت العملة. ونرى-بما أن المثقال بزمن النبي-صلى الله عليه وسلم-، وعند أهل مكة هو أساس العملة- نرى أن العملة الذهبية، أو ما يقوم مقامها ويؤدي وظيفتها هي التي ينبغي أن تتخذ أساسا للتقدير”.

ii-Shaikh Yusuf Qaradawi shi ma ya bincika wannan mas’alar ya tabbatar da cewa, “Abinda ya fi dacewa shi ne a takaita a kan ƙaddara nisabi a wannan zamanin da gwal. Duk da cewa kddarawa da azurfa zai fi amfani ga talakawa da wadanda suka cancanci a basu, amma akwai matar lamba ga sosai ga masu dukiyar a wajen fitar da zakkar, wadanda ba ‘yan jari hujja ba ne, ko wasu manyan masu kuɗi, su ne ma kunzumin al’ummar”.-(Fik’huz Zakka:1/288. Yana da kyau kuma a duba 1/276)
قال الشيخ القرضاوي-رحمه الله-: “كان الأولى أن يقتصر على تقدير النصاب في هذا العصر بالذهب. وإذا كان التقدير بالفضة أنفع للفقراء، والمستحقين، فهو إجحاف بأرباب الأموال. وأرباب الأموال في الزكاة، ليسوا هم الرأسماليين وكبار الموسرين، بل هم جمهور الأمة”.

iii-Shaikh Ali Qaradagi, daya daga cikin manyan masana tsarintsarin kin arziki na Musulunci a duniyar mu ta yau, yana cewa, “Azurfa yanzu ba ta zamo ita ce maaunin zakka a wannan zamanin namu ba. Saboda yanzu ba ta da kuma kamar yadda take da kima a zamanin baya. Saboda shi nisabi ai shi ne karamin ma’auni na wadata. Wannan yana tabbatar da cewa nisabin azurfa (wanda yake kamar dala dari biyu 200 Dollars, ba shi ne ma’aunin wadata/arziki ba”.
قال الشيخ على القدره داغي: “إن الفضة لم تعد معيارا في عصرنا الحالي، لأنها لم تعد ذات قيمة كما كانت في سابق العصور، لأن النصاب يعني الحد الأدنى من الغنى، مؤكدا أن نصاب الفضة (حوالي 200 دولار) لم يعد مقياسا للثراء”.

8-Idan ma so ake a duba manufofin Shari’ah wajen taimakawa talaka, sai a matsa duka wadanda suka isa fitar da Zakka bisa kimar gwal su fitar da ita yadda ya kamata. A lokacin za a ga yadda dukiyar zata kewaye kowa ya sami rabon sa. Amma wanda yake da ‘yan kwabbasa na N 656,880 yana fafutukar yadda zai cigana da rike kansa, sai kuma aka ce zakka ta hau kansa wannan an sa shi a damuwa sosai. Domin shi yake da bukatar tallafi ! Abin nufi da’awar aiki da Makasid ba shi ne da baka Makasid a aikace ba.

A dunkule, an kawo wannan ne duka don tabbatar da cewa kimar azurfa a yanzu bata kai kimarta a lokacin Annabi (S.A.W) ba. Don haka ba za a dauki giram 595 dinta a matsayin ma’aunin fitar da Zakka ba. Bayanai sun nuna mana cewa ita da kanta azurfar take samun hawa da sauka tun bayan wucewar manyan Khalifofi, ba wai turawan mulkin mallaka ne suka kawo daina amfani da ita azurfar ko daina amfani da shi kansa gwal din ba.

An yi wasu dauloli a tarihin Musulunci da suka jingine amfani da gwal da azurfar ma baki ɗaya, suka yi amfani da wasu abubuwan daban da ake kira da (Al-Fulus) da sauransu, amma duk da haka sun auna wadannan kudaden nasu da gwal, sun kuma fitar da zakka. Irin hakan shi ne abinda ya wajaba ga al’ummatai. Kowanne su auna kudadensu a kan kimar gwal, su fitar da Zakka. Muna rokon Allah ya karba!
Bisa bayanan da aka yi za a fahimci cewa mas’alar ba ta cikin tsarin irin mas’alolin nan da za a ce akwai rangwame duk wanda mutum ya dauka na fitarwa a kimar gwal ko a kimar azurfa, a ce duk daidai ba ce. Saboda kuskuren fahimta ne tun farko da mutane da yawa suka fada ciki. Daga cikinsu kuwa har da masu sa nisabin gwal da na azurfa a tare a matsayin sanarwa da al’umma duk wanda mutum ya dauka shikenan. Wannan kuskure ne a zahiri. Mutum ya fahimci yadda tsarin abu a yadda yake shi ne aiki da ilimi!

Allah ne Masani.

Allah ya karbi ibadu, ya bamu sa’a da dacewa a duniya da Lahira.

Farfesa Ahmad Murtala, Shehin Malami ne a sashen Nazarin Shariah da Ilimin addinin Musulunci a Jamia’r Bayero dake Kano. 

Continue Reading

Hausa

Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.

Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .

Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.

“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.

Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun  da basu samu damar biya ba a baya.”

Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A  bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari,  gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.

“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen  ciyar da al’umma.” Dangote.

 

Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.

“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da  neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”

Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada  rade-radi da jita-jita.

Continue Reading

Hausa

A kwanaki 100, VON ta farfaɗo, ci gaba ya bayyana da kuma fatan fin haka nan gaba – Ndace

Published

on

Jibrin Baba Ndace

 

A zafin ranar 29 ga watan Oktoba, 2023 ne aka samu wani canji na alheri da ya lulluɓe harabar Voice of Nigeria (VON) mai cike da sa’ida, sakamakon naɗin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi mini a matsayin Darakta-Janar na gidan rediyon na ƙasa, inda hakan ya zamto wani ɗamba na sauyin zamani a kafar yaɗa labaran ta ƙasa.

Bikin karɓar aiki daga hannun wanda na gada, Osita Okechukwu ya wuce a ce biki ne na sallamar ma’aikaci. Da ga karɓar shugabancin, guguwar sauyi ta fara kaɗa wa bayan na halarci taron AFRICAST 2023 a Legas. Sai na yi amfani da wannan damar na ziyarci cibiyoyin watsa shirye-shiryen tashar ta mu da ke Ikoyi da Ikorodu, inda hakan ya bani kwarin gwiwar cewa akwai dama mai ƙarfi da zan samu na kawo gagarumin ci gaba a gidan rediyon.

Dawowa ta shelkwatar VON da ke Abuja kuma, sai na fuskanci akwai aiki ja a gaba na. A yanayin lalacewar gine-gine da kayan aiki da na gani a cibiyar mu ta Ikko, sai na ji cewa ya zama wajibi na tashi tsaye na kawo gyara cikin gaggawa.

Duk da cewa kusan hakan yanayin ya ke a cibiyar watsa shirye-shiryen mu ta Lugbe a Abuja, akwai abinda ya bani ƙarfin gwiwa, shi ne wutar sola da na tarar. Sai na fahimci cewa wato akwai ɗumbin nasarori a VON, amma ana buƙatar jajirtaccen shugaba da zai farfaɗo da ita.

Bayan gine-gine da kayan aiki, ma’aikata su ne ƙashin bayan VON, sai dai kuma kash! akwai ƙarancin karsashi a tare da su ma’aikatan gidan rediyon a duka tashoshin namu na Abuja da Legas sakamakon rashin biyan su alawus-alawus na su da kuma kuɗaɗensu na ƙarin matsayi. Wannan ƙalubale ne da ya ke buƙatar kawo ɗauki cikin gaggawa domin samun gaba mai kyau.

Tun asali, kamata ya yi a samu wani kundi na tsare-tsare. Zaburar da ma’aikata na buƙatar ƙirƙiro da dabarun inganta walwalar su da kuma ƙara musu matsayi akai-akai lokacin da ya dace da kuma basu lambobin yabo bisa ƙwazon su a aiki. Kada kuma a manta da cewa haɗin kai tsakanin shugabanni da ma’aikata shi ne babban sinadarin kawo sauyi Na ci gaba a ma’aikata.

Halastar mu zuwa babban taron UNESCO na duniya, karo na 42 da aka yi a birnin Paris da kuma taron ranar rediyo na duniya a Dubai, ba wai mun je yawon buɗe-ido ba ne, sai dai wata babbar dama ce ta samun damammaki daga ƙasashen duniya. Waɗannan tarukan wata babbar dama ce ta nuna wa duniya irin ƙwazon VON na watsa shirye-shirye daidai da yadda ya ke a duniya da kuma ƙulla alaƙa, duk a ƙoƙarin ta na zama a aji ɗaya da manyan kafafen yaɗa labarai na duniya.

Ganawar farko ta shugabannin VON da ta gudana a ranar 19 ga watan Disamba, 2023, ba wai an yi zaman hira ne kawai ba, sai dai zaman ya kasance wata ɗamba ce aka kafa wajen samar da haɗin gwiwa domin fitar da dabarun aiki da za su ƙara taimaka wa gidan rediyon ya cimma muradun sa.

Aiyuka na bi-da-bi me ya haifar da nasarar da mu ka samu ta ganawa da kwamitin majalisar dattawa kan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma, kare kasafin kudin da mu ka yi wa kwamitocin majalisar dattawa da na majalisar wakilai da kuma ziyarar aiki da mu ka kaiwa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris. Waɗannan aiyukan sun kasance tubalin mu na gina alaƙa, wacce za ta samar mana da taimako da kuma fahimtar juna.

Hakazalika, alaƙar da mu ka ƙulla da ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu, da suka hada da Thunderbird, Image Marchants Promotions Limited, SEMEDAN, GOTNI, NIPR, Ciyaman na NUJ a Minna da kuma wakilci da ga Dangote Group da Jaiz Bank, ba wai ziyara ba ce kaɗai, sai dai sun zamto tattaunawa da za su buɗe kofa, su gina mana gadoji da kuma alaƙa da za su taimaka wa VON ta kai gaci.

Sannan, ziyarorin da muka kai wa Media Trust, National Orientation Agency, News Agency of Nigeria, Nigerian Diaspora Commission da NTA da kuma manyan shugabannin sojoji ya nuna ƙwazon mu na kawo gyara mai inganci a VON tare da bata suffar da ta ke buƙata.

A kwanaki 100 na farko a matsayin Darakta-Janar, na bada umarnin cewa duk wani ɗan hidimar ƙasa (NYSC) da masu koyon aiki a VON, dole a basu horo na musamman, da nufin su ji a ransu kamar su ma ma’aikata ne a tsawon lokacin da za su yi a gidan rediyon. Daɗin daɗawa kuma mun ƙulla alaƙa da Guards Polo Club da ƙungiyar shugabannin ma’aikatu ta Afirka domin jawo hankalin al’umma ga irin aikace-aikacen VON.

Bayan duk wadannan, irin bayanan sam-barka da ke fitowa daga bakunan ma’aikatan VON masu albarka, ya ƙara mana ƙaimi da ƙwarin gwiwa. Maida hankali da mu ka yi wajen gyara lalatattun kayan aikin mu da neman tallafin gwamnati wajen farfaɗo da tashar mu ta Lugbe ya nuna yadda shugabancin mu ke da zuciyar kawo gyara da kuma ɗaukaka VON.

A yayin da muka cika kwanaki 100 da karɓar ragamar shugabancin VON, magana a ke yi ta fara ganin guguwar sauyi ta fara kaɗa wa. Kalubalen da mu ka taras ya zamto wani ginshiƙi na gyara mai inganci. Sannan, dabarun da mu ke ɓullo da su sau ɗau saiti na fito dartabar VON ba wai a matsayin shahararren gidan rediyo ba, har ma ta zamto a bar koyi a fannin watsa shirye-shirye a faɗin duniya. Yayin da ake ci gaba da samar da hanyoyin gyara, lokaci kaɗai mu ke jira da zai fito da VON da har karan ta zai kai tsaiko a idon duniya.

Mallam Jibrin Ndace shi ne Darakta-Janar na VOICE of Nigeria, VON. Tashar watsa labarai na duk duniya ta Nijeriya.

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending