Connect with us

Hausa

Ranar Hausa: Ya Ɗabi’un Bahaushen asali suke?

Published

on

Mukhtar Sipikin

Ya zam al’ada a irin wannan rana ta Hausa, jama’a sui ta zayyano karin maganar Hausa da kuma gagara gwari don ai nishaɗi a ƙarawa kuma jama’a ilimi. Sai da ana tuya ne ana mantawa da albasa, don ba a faɗo ɗabi’u da halaye na Bahaushen asali, don mu faɗaku, mu fahimci Bahaushe in ya yi wata halayya da wasu ba su gane ba.

Wato shi Bahaushe mutum ne da ba shi da ƙabilanci, ko ya nunawa wanda ba jinsin sa ba tsangwama ko kyara. Wannan halayya ta sa shi ya ke ba da auren ƴaƴansa da jinsin da ba na sa, sannan ya auro jinsin da ba na shi ba, shi isa ma za ka ga ya cakuɗu da jinsin kala-kala.

Duk da ba shi da kyara, amma in har ya ga wani mutum ya yi rashin kan gado, ko rashin fasaha sai ya murmusa ya ce “wane ba shi da Hausa” domin shi Bahaushe kalmar Hausa ta na da ma’anoni daban-daban. Hausa na nufin harshe, Hausa na nufin fikira, Hausa na nufin wayewa da basira, Hausa a taƙaice na nufin rayuwar Bahaushe da halayyarsa da komai nasa.

Bahaushe mutum ne mai son zaman lafiya, shi isa za ka ji yana cewa “zaman lafiya ya fi zama Ɗan Sarki” don ko a tarihinsa ya sha gwagwarmaya, ya san bala’in yaƙi da zaman ɗar-ɗar. Shi isa za ka ga duk inda Bahaushe ya ke, ka ganshi cikin kyakyawar mu’amulla da ƙabilun wajen, har ta kai ya zam ɗan gari, misali: Hausawan Ghana, Kamaru, Chadi da wani sashi na C. Africa, K

Bahaushe mutum ne mai sanyin hali, bashi da riƙo ga sauran yafiya, in wata ƙabila ta yi mai wani abu mammuna, sai ya yafe, sannan ba zai faɗawa ƴaƴansa abun da akai masa ba, don kar su taso su ce za su ɗau fansa. Shi yafiyarsa kamar mantuwarsa ta ke, in yafe sai ya manta, sai dai in an fama ciwon.

Bahaushe mutum ne mai girmama shugabanni, shi dai kawai abun da ya ke so, shi ne ai masa adalci. In shugaba ya yi masa adalci ɗaya, ya zalunce shi sau ɗari, to sai ya yi mai uziri da adalcin nan ɗaya da ya yi mai.

Bahaushe yana da tsari da a sana’o’insa, ko wani gida da sana’arsu, wasu jima, wasu saƙa, wasu su, wasu farauta, wasu wanzanci, wasu fawa dss.  Noma da fatauci kuwa na kowa ne.

Bahaushe mutum ne mai girmama mata, matan kuma masu girmama maza. Shekaru aru-aru a ƙasar Hausa in ka duba tarihi sai ka ga har sarakuna mata aka yi.

Bahaushe mutum ne da ya fi fifita hankali fiye da wayo. Ba wai ba shi da wayo ba ne, amma ya fi alfahari da hankali, shi isa ɗaya daga cikin abun da ya fi yi wa Bahaushe ciwo, shi ne ka kira shi da mahaukaci.

Bahaushe bai ɗauki duniya a bakin komai ba, shi isa ma ya ke kiranta da “rumfar kara” ko “budurwa wawa” sannan bai ɗauki abun cikinta wata tsiya ba, shi isa in aka samu mai maƙo, sai ka ji ana cewa “wane ya fiya son abun duniya”

Wannan halaye ne masu kyau na Bahaushe, sai dai zamani ya canza, wasu halayen masu kyau yanzu in yana aikata su, sai a dunga kallonsa wawa wanda bai san ciwon kansa ba, shi kuma yana ganin ai halayensa na gari ne, wanda kowacce ƙabila yakamata ta koyi da su.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

EFCC arraigns one for N108 million fertiliser fraud in Kano

Published

on

Sanusi Hashim

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

The Kano Zonal Directorate of the Economic and Financial Crimes Commission, EFCC, has arraigned one Sanusi Hashim for allegedly misappropriating and converting to his personal use, the sum of 108 million Naira. 

 

KANO FOCUS reports that Hashim was arraigned before Justice Kabiru Dabo of the Kaduna State High Court sitting in Zaria on a one -count charge of misappropriation contrary to Section 293 and punishable under section 294 of the Penal Code.

 

He was alleged to have collected a total sum of 108 million Naira from one Ahmad Mohammad Liman and Basiru Mohammad for the supply of fertilizer but instead misappropriated and diverted the money for his personal use.

 

The lone-count charge reads ‘’That you Sanusi Hashim sometime in April 2020 under the jurisdiction of the Kaduna State High Court dishonestly misappropriated and converted to your own use, the sum One Hundred and Eight Million Naira (N108,000,000) property of one Ahmad Mohammad Liman and Basiru Mohammad for the supply of fertilizer from Indorama Eleme Fertilizer and Chemicals and you thereby committed an offence under Section 293 and punishable under Section 294 of the Penal Code’’.

 

The defendant pleaded not guilty when the charge was read to him.

 

Counsel to the prosecution, Bright C. Ogbonna prayed the court for a trial date in view of the defendant’s plea.

 

Consequently, Justice Dabo remanded the defendant in a Correctional Centre and adjourned the matter to February 10, 2025 for hearing of bail application.

Continue Reading

Hausa

Gov. Yusuf Directs Reassigned Commissioners to Handover and Assume Duties by Tuesday, 17th December

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

The Governor of Kano State, Alhaji Abba Kabir Yusuf, has directed all reassigned commissioners to ensure a smooth handover and assumption of duties by Tuesday, 17th December 2024.

Speaking through his spokesperson, Mr. Sanusi Bature Dawakin Tofa, the Governor stated that the cabinet changes will take full effect during the next council meeting on Wednesday, 18th December 2024.

He emphasized the need for the completion of all transition processes before then.

“All commissioners affected by the changes are directed to hand over their responsibilities between Monday, 16th and Tuesday, 17th December 2024,” the statement reads.

The Governor further urged members of the state executive council to redouble their efforts and uphold a strong spirit of teamwork, dedication, and commitment to supporting his administration in serving the good people of Kano State.

Continue Reading

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Trending