Connect with us

Hausa

Babu abin mamaki a rikicin Ganduje da Shekarau-Kwankwaso

Published

on

Rabiu Kwankwaso

Aminu Abdullahi

Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ko kaɗan bai yi mamakin rashin jituwar da ta dabaibaye jam’iyyar APC a jihar Kano ba.

Kano Focus ta ruwaito Kwankwason na wadannan kalamai ne ya yin zantawarsa da sashen Hausa na BBC ranar Juma’a.

A cewar Kwankwaso tuntuni ya san haka za ta faru, batu ne kawai na lokaci da zai bayyana komai.

Sanata Kwankwaso, ya ce ba bu abun da ya yi tasiri a rikicin jam’iyyar ta APC a Kano face tsagwaron son rai da son zuciya, da kuma rashin haƙuri.

”Duk wanda yake ba zai iya rike wanda ya masa alheri shekara da shekaru ba, wanda shi ma da kansa yana fada cewa na masa, amma shi randa ya samu dama rana daya tak ya kasa iya rike Kwankwaso da ‘yan Kwankwasiyya, to kaga ai ba zaman lafiya”.

”Ni abun ya ma sake tabbatar min da abun da nake zato ne kawai” inji shi.

Ya kara da cewa dama Hausawa kan ce ƙarya fure kawai take ba ta ‘ƴa’ƴa, don haka ga shi lokacin da ake jira ya zo.

Kwankwaso ya ce ya ji dadin kalaman da tsohon gwamnan Jihar Malam Ibrahim Shekarau ya yi na yabonsa, yana cewa duk wanda aka yi wa irin wannan yabo dole zai ji dadi.

”Na samu labarin maganar da ya yi a kaina, amma kawai sai na godewa Allah, ka ga da kamar bai gane bane sai yanzu Allah ya nusar da shi, duk mai hankali zai ji dadi.

Sannan a matsayinsa ma ace ya saki jiki ya yi wannan magana to na san maganar ta kama jikinsa da gaske yake yi”

”Don siyasa ta sake hadamu sai a tafi, idan ma bata hada ba sai a godewa Allah, tun da an samu ci gaba a tunaninsa ga shi yana fadar yadda al’amarin yake.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Anyi jana’izar Sarkin Bai a garin Danbatta

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

 

An gudanar da jana’izar Sarkin Bai Alhaji Muktar Adnan wanda ya ya rasu cikin daren juma’a.

KANO FOCUS ta ruwaito an gudanar da jana’izar ne da misalin 2:30 jim kadan bayan Kammala sallar juma’a a Kofar fada da ke garin Danbatta.

Babban limamin Danbatta Malam Nasir Abubakar ne ya sallace shi.

Cikin wadanda suka halarci jana’izar akwai mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero, sai kuma Sarkin Kazaure Ahaji Najib Hussain Adamu.

Haka kuma cikin mahalartan akwai tsohon gwamnan Kano sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da kuma Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Jim kadan bayan kammala sallar ne aka binne shi kusa da Mahaifinsa a daya daga gidajen ‘ya’yansa.

Wanene Sarkin Bai?

An Mukhtar Adnan a shekarar 1926 a garin Danbatta, ya fara karatun sa na Elementari a makarantar Danbatta a shekarar 1935 daga bisani kuma ya shiga makarantar Midle ta Kano 1939 zuwa 1944.

Mahaifinsa shi ne Mohammed Adnan wanda ya rike mukamin Danmaje a Babura, sannan ya dawo garin Danbatta a matsayin  Sarkin Bai tsakanin 1942.

Ya kuma halarci makarantar harkokin mulki ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Ya fara aiki da  hukumar N A, daga 1948 zuwa 1950 inda ya rike manyan mukamai a wancen lokacin ya kuma samu lambobin girma da dama.

A shekarar 1954 ne kuma mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi I ya nadashi sarkin Ban Kano kuma dan majalisar sarki.

Haka kuma a shekarar 1968 gwamnan Kano Audu Bako ya nadashi a matsayin kwamishinan Ilimi na farko a jihar Kano.

Ya nada sarakuna har hudu a Kano da suka hadar da Malam Muhammadu Inuwa a watan Afrilun 1963, sai kuma Alhaji Ado Bayero a shekarar 1963, sai Muhammadu Sanusi II a shekarar 2014, sai kuma Sarkin Kano na yanzu Alhaji Aminu Ado Bayero.

Ya rasu ranar Juma’a 03 ga Disambar shekarar 2021, yana da shekara 95.

Shi ne hakimi mafi dadewa a masarautar Kano da ya shafe shekara 65 yana hakimci.

Gwamnatin Kano ta nuna alhininta

Duk da cewa ba a ga fusakun jami’an gwamnatin Kano a wurin jana’izar ba, sai dai gwamnatin ta fitar da sanarwar nuna alhininta.

Cikin wata sanarwa da sakataren yada labara gwamnan Kano  Abba Anwar ya fitar ta ce jihar Kano ta rasa babban bango.

Sanarwar ta ce Sarkin Bai ya rasu a lokacin da jihar Kano ke tsananin bukatar irinsu.

Haka kuma gwamnan ya ce jihar Kano ba za ta taba mantawa da irin rawar da ya taka wajen inganta ilimi ba.

A don hakan ne ma ya mika sakon ta’aziyyarsa ga yan uwan mamacin da ma al’ummar jihar Kano baki daya.

Buhari na alhinin rasuwarsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masarautar Kano bisa rasuwar ta Sarkin bai.

Cikin wata sanrwa da jami’in yada labaransa Garba Shehu ya fitar ta ce rasuwarsa ba wai asarace ga jihar Kano ba har  ma da kasa baki daya.

A cewarsa tsahon shekara 63 da ya kwashe yana sarauta a Kano da kuma kasancewarsa bulalaliyar Majalisa a baya ya tabbatar da matsayinsa na wanda ya taka rawa wajen gina kasa.

Continue Reading

Hausa

Yadda Abdullahi Abbas ya sa aka kona ofishin mu-Barau Jibril

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Sanatan Kano ta Arewa Barau I Jibrin ya zargi shugaban jam’iyyar APC tsagin gwamnan Kano Abdullahi Abbas da kona masa ofishi.

Haka kuma sanatan ya zargi  shugaban karamar hukumar Gwale, Khalid Ilyasu Diso da kuma mataimaki na musamman ga gwamnan Kano kan al’amuran na musamman Murtala Gwarmai  da hannun a ciki.

Mai magana da yawun Sanata Barau, Shitu Madaki Kunci ne ya bayyana hakan ya yin da yake zantawa da KANO FOCUS ranar Alhamis.

Madaki ya ce basa kokwanto kan zargin da suke yi a kan mutanen uku, acewarsa ba za su bar abin ya tafi hakaba, ba tare da daukar mataki ba.

“Abdullahi Abbasa da Honorable Khalid Diso, da Gwarmai  S A sun jagoranci gungun wasu matasa yan bata gari zuwa wannan ofis inda suka faffasa kuma saka sa wuta a wannan waje”

Ya ce tuni suka fara hada bayanai kuma da zarar sun kammala za su shigar da kara a kotu.

Yadda al’amarin ya faru.

Da safiyar yau ne wasu matasa dauke da muggan makamai suka farwa ofishin jam’iyyar APC na jihar Kano tsagin Malam Ibrahim shekarau, wanda mallakin Sanata Baraune.

Matasan sun cinna wuta a wurare da dama na ofishin tare da farfasa gilasansa da kuma sace wasu muhimman abubuwa da ke cikinsa.

Muhammad Shehu shaidar gani da ido ne ya ce matasa sun fito ne daga harabar Sakatariyar Audu Bako, suka kuma bi kan titin Sokoto suka bullan kan titi Maiduguri.

da ga nan ne kuma suka isa inda ofishin ya ke suka kuma sa duka tare da cinna wutar.

“Matasa ne aka turosu da makamai da galan galan na fetur zuwa ofishin nan na Barau, kawai sun sa duka sun faffasa wajen sun saci kujeru.

“Abinda zai baka haushi wai motar ‘yan sanda na binsu a baya daya gaba daya a baya, akwai ma ‘yan sandan da na sansu da idona.

“Jami’an gwamnati muke zargi da turosu, su ne nan suka sakasu yin wannan aikin.

Shi ma Ibrahim Jamilu ya ce a gabansa matasan suka isa ofishin dauke da makamai masu tarin yawa, suka kuma sa duka kan mai uwa da wabi.

“Harga Allah a gabana suka zo sun kai su kunsan dubu da adduna da wukake suka fara kona wurin.

“Nan take muka fara waya muna kiran mutanenmu, muna gaya musu su zo za a kona ofishin Barau.

“Suna ganin mun fara yawa ne kuma sai suka fara guduwa daga wurin. Acewarsa.

Yadda na sha da kyar

Isma’il Muhammad da ke gadin ofishin ya ce ba dan ya buya a bandaki ba da tuni matasan sun kashe shi.

Ya ce Allah ne kadai ya kubutar da rayuwarsa, ya sa ya kewaya bayan ofishin, basu same shi a ciki ba.

“Na gansu dauke da makamai masu tayar da hankali da suka kidimanin rayuwa.

“Sun shigo da fetur ne a galan, ai idan aka ce maka adadinsu ya kai dubu bazan musaba, sai da na gudu fah, karshe a bandaki na buya.

“Ta kan titin Maiduguri suka bullo babban tititin da ko shaidan ne ya biyo sai an ganshi, sai daga baya kuma yan sanda suka zo.

Abdullahi Abbas yaki magantuwa

A kokarin jin ta bakin Abdullahi Abbas kan zargin da ake yi masa mun ziyarci gidansa, inda aka ce bai sakko ba.

Bayan mun jira ne kuma ya fita zuwa filin jirgin sama domin zuwa Abuja.

Mun kuma bishi har filin jirgin saman sai dai hakanmu bai cimma ruwa ba domin yaki cewa komai.

An kama mutum 13

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce ta kama mutane 13 cikin masu tada husumar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar da tsakar ranar Alhamis.

Ya ce an kamasu da nau’in makamai iri-iri, da suka hadar da wukake, da gorori, gariyo da barandami.

Kiyawa ya ce tuni kwamishinan ‘yan sandan Kano Shu’aibu Sama’ila Dikko ya bayar da umarnin a fadada bincke kan al’amarin.

Sakatariyar Audu Bako ce matattarar ‘yan daban

An dai ga matasan sun fito daga sakatariyar Audu Bako dauke da makaman, inda suka bi kan titin Sokoto, zuwa Cinimar  Marhaba suka bulla kan titin Maiduguri.

Haka zalika bayan kammala aikinsu an gansu sun koma cikin sakatariyar suna sauya kaya, daga nan suka tafi gida.

Haka zalika an ga yadda suka dinga fada da junansu bayan fitowa daga Sakatariyar harma aka jikkata wani matashi da aka yasar bakin hanya.

Matashin dai ya sha suka da wuka a wuyansa da kansa, inda jini ke kwarara, amma aka ransa wanda zai kai masa dauki.

Continue Reading

Hausa

Daya daga cikin malaman da suka jagorancin mukabalar Abduljabbar Kabara ya rasu

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Daya daga cikin malaman da suka jagorancin mukabala da malam Abduljabbar Kabara Malam Mas’ud Mas’ud Hotoro ya rasu.

Kano Focus ta ruwaito Malam Mas’ud ya rasu ne a daren ranar Labaran sakamakon hadarin mota a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Idan za a iya tunawa malamin na cikin mutum hudu, da sukayi Muƙabala da Sheikh Abduljabbar Kabara a kwanakin baya.

Malamin shi ne wanda ya wakilci bangaren Kadiriyya ya yin zaman mulabalar.

Rahotannin sun bayyana cewa za a yi wa Malamin jana’aiza a yau Alhamis a gidansa da ke Hotoro da karfe 2:00 na rana.

Continue Reading

Trending