Connect with us

Hausa

Sheikh Abduljabbar ya kuma korar lauyoyin da suke kare shi a Kotu

Published

on

Nasiru Yusuf

A karo na biyu Sheikh Abduljabbar ya kuma korar lauyoyin da suke kare shi a Kotu, inda yake ake tuhumarsa da yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

A zaman kotun na ranar Alhamis, Sheikh Abduljabbar ya fadawa Kotu cewa lauyoyinsa sun gaza kare shi, don haka shi ne zai cigaba da kare kan sa.

Malamin ya ce ya yarda da duk shawarar da Alkali ya ba shi na kada ya cire lauyoyinsa daga cikin shari’ar,

Abduljabbar ya ce tun asali lauyoyinsa ne suka hana shi ya yi magana har aka kai shi Asibitin duba kwakwalwa, kuma suka rika tsorata shi da cewar za a yanke masa hukuncin kisa domin angama komai da su lokaci kawai ake jira.

A cewar Malamin wannan ne yasa har ya kawo yanzu yana gidan kaso.

Malamin ya kuma zargi lauyoyinsa na baya da keta alfarmar iyalinsa, wanda ya ce bai ji dadin hakan ba.

“Amma nasan duk lauyoyin nan ba za su iya kare ni ba. Idan kuma na kyale su, to zan iya zubar da mutuncina, ko ba komai. Don haka ni abun da nake so in ce, wannan rigima duk akan auren Nana Safiyya ne da kuma maganganun da ake cewa na ce, duk ina da abun da zan fada, domin haka, ko mun zauna da lauyoyina ko bamu zauna da su ba, ba za su iya baiyana wadannan hujjojin nawa ba. Domin ba lauyan da yake Jin Arabiyya a cikin su.

“Don haka magana ta gaskiya ni sharia  ta da ake tuhumata ba ta ‘law’ ba ce ta Hadisai ce.  Kuma ni ne nasan Hadisan su lauyoyi ba su san su ba. Domin lauyana na baya da ya kafe na ba shi hujjojin, amma bai iya bayar da su ba a gaban kotu. Sai ya ce in bashi duk hujjojin, don ya cuda su a cikin ‘law’ amma bai iya yin hakan ba.

“A karshe sai suka ce shi shaida na farko jahiline.  Shi ne na ce, ta ya ya za a yi jahili ya haddace Alqur’ani da hadisi littafi ashirin, fa fiqihu goma, ku ce masa jahili?  Kuma nace musu ga bayanina a mp3 su danna kowa ya ji. Sai suka ce shi shaida bai danna komai ba,” A cewar Sheikh Abduljabbar.

Sheikh Abduljabbar ya ce ya ba wa lauyoyinsa samina akan ga yanda za su yi, amma sun kasa kare shi, don haka ya yanke shawarar shi zai iya kare kansa.

Sannan ya shaidawa Kotu daga yanzu ya cire duk lauyoyin da suke kare shi a cikin wannan shari’a da ake yi.

Malamin ya gabatarwa da Kotu bukatar ta ba shi dama ya yi wa shaida duk tambayar da ya tsara.

Sai dai lauyan gwamnati ya ki amincewa da abun da Sheikh Abduljabbar ya nema, inda yace a doka ba a yin irin wannan shari’a babu lauya domin idan fa abinda ake tuhumar malamin da aikatawa ya tabbata to hukuncin kisa ne akan shi.

Don haka ya ce bai yarda Sheikh Abduljabbar ya cire lauyoyinsa ba, amma zai iya yi wa shaida duk tambayoyin da yake so.

Sannan ya roki kotu ta ba wa Sheikh Abduljabbar dama ya je ya yi nazari, su ma lauyoyinsa su yi nazari, kuma su ma lauyoyin gwamnati su yi nazari sannan a cigaba da shari’a.

Daga bisani Kotu ta gamsu da wannan rokon na lauyan gwamnati dan gudun yin kuskure a cikin sharia.

Alkali ya waiwayi Sheikh Abduljabbar ko ka yarda a daga sharia zuwa wani lokaci, ya ce ya yarda.

Da Alkali ya tuntu6i lauyoyin Sheikh Abduljabbar, sai lauya Umar Faruk ya ce, sun san halin da Sheikh Abduljabbar yake ciki, don haka suka ba shi dama ya yi magana da kan sa.

Lauya Umar Faruk ya ce, duk da malamin ya ce, ya ciremu to mun yarda da abun da Kotu ta fada na a daga sharia kuma muna cikin wannan shari’ar daga nan har ta kare domin muna tausayamasa halin da yake ciki amma shi bai san abun da mu muka sani ba shi yasa. Yana cikin gaggawa ne. Kuma a fagen irin na sharia ba fagen a bude littafi a koyar da karatu ba ne.  Fage ne na ilimin sharia, don haka muna yi masa uzuri.

Alkali ya kara Jan hankalin lauyoyin Sheikh Abduljabbar da suyi hakuri akan kalaman malamin kuma kada su janye su cigaba da hakuri da tattaunawa.

Daga nan Alkali ya daga cigaba da zaman shari’ar zuwa ranar Alhamis 11 ga watan Nuwamba, 2021.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Rikicin APC :Ba za mu karbi hukuncin kotu ba-Ganduje

Published

on

Ganduje

Mukhtar Yahya Usman

Gwamatin Kano ta ce ba za ta amince da hukuncin da wata kotu a Abuja ta yi ba da ya rushe zaben shugabancin jam’iyyar APC da tsagin gwamnati ya gudanar.

KANO FOCUS ta ruwaito kwamishinan shari’a na jihar Kano Barisster Musa Abdullahi Lawal ne ya sanar da hakan ga manema labarai ranar Talata.

Kwamishinan ya ce lauyoyin gwamnati sun fara nazaratar hukuncin tare da daukar matakin da ya da ce.

Ya ce sunyi mamakin hukuncin kuma ba za su karbe shi ba, a cewarsa lokacin da aka gudanar da zabukan a matakan mazabu babu wadanda suka yi nasu daban.

A don haka ya ce basu ga dalilin da yasa aka rushe shugabanci Abdullahi Abbas ba.

Barista Lawan yace za su duba yadda aka yi masu karar suka sami sakamakon zabukan da aka gudanar har suka gabatarwa kotu, da ta amince dasu.

Continue Reading

Hausa

Yanzu-yanzu-Kotu ta rushe shugabancin Abdullahi Abbas

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Wata kotun tarayya dake Abuja ta rushe zaben shugabancin jam’iyya APC da tsagin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya gudanar.

KANO FOCUS ta ruwaito mai shari’a Hamza Mua’zu ne ne ya rushe zaben a zaman kotu na yau  Talata.

Haka kuma mai shari’ar ya tabbatar da zaben da tsagin tshohon gwamnan Kano Ibrahim shekarau ya gudanar.

A cewar mai shari’ar zaben na bangaren Shekarau ya samu sanya hannun mutum 7 daga cikin wadanda uwar jam’iyyar ta turo jihar Kano domin gudanar da zaben.

Cikin abinda tsagin Shekarau ya gabatar, gaban kotun shi ne tsagin na gwamna Ganduje bai gudanar da zaben matakin kanan nan hukumomi da mazabu ba.

Idan za a iya tunawa a watan da ya gabata ne aka gudanar da zaben shugabancin jam’iyya APC a jihohin kasar nan ciki har da nan Kano.

Sai dai a nan Kano an samu rashin hadin kai tsakanin mambobin jam’iyyar.

Hakan ta sanya gwamna Ganduje ya gudanar da zaben tare da wadanda ke goya masa baya a wani wuri daban.

Yayin da Malam Ibrahim shekarau ya gudanar da nasa zaben da a wani wurin daban

Haka zalika tsagin na gwaman Ganduje ya zabi Abdullahi Abbas  a matsayin shugaba, ya yin da tsagin Ibrahim Shekarau ya zabi Ahmad Haruna Zago a matsayin shugaba.

Continue Reading

Hausa

Yanzu-yanzu: Sarkin tsaftar Kano ya rasu

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Allah ya yiwa Sarkin Tsaftar Kano Alhaji Ja’afaru Ahmed Gwarzo rasuwa.

KANO FOCUS ta ruwaito Sarkin Tsaftar ya rasu ne ranar Laraba a kasar Saudiyya.

Daya daga cikin ‘yan uwan marigayin Alhaji Nasiru Sani Gwarzo ne ya tabbatar da rasuwar tasa ga manema labarai.

Sarkin tsatar ya rasu ne bayan ‘yar gajeriyar rashin lafiya a kasa mai tsarki da ya tafi domin aikin umara.

Kafin rasuwarsa, Sarkin shi ne mataimaki na musamman ga gwamnan Kano Abdullahi Ganduje kan rigakafin cutar shan Inna.

Continue Reading

Trending