Connect with us

Hausa

Buhari zai baiwa Kano tallafin bilyan 18

Published

on

Muhammadu Buhari

Mukhtar Yahya Usman

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a bawai jihar Kano tallafin N biliyan N18 domin cike gibi da aka samu cikin kasafin kudi.

Haka zalika shugaban kasar ya amince a baiwa sauran jihohin kasar 35 wadannan kudade, jumlatan  N bilyan 656.

KANO FOCUS ta ruwaito wannan na cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osibajo ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce kowacce jiha za ta samu naira biliyan 18.225, wanda za ta biya cikin shekara 30 kan kuɗin ruwa kashi 9 cikin 100.

Ramadan:Rahma Sadau ta tallafawa mabukata sama da 2000

Danzago ne Shugaban Jam’iyyar APC a Kano – Shekarau

‘Yan Film basu tallafawa Ashiru Nagoma ba-Abokanansa

A cewar fadar shugaban ƙasa, an ɗauki matakin ne saboda a tallafa wa jihohi cimma muradansu na harkokin kuɗi musamman kasafin kuɗaɗensu na shekara.

Za a raba kuɗin ne a mataki shida cikin wata shida kuma ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN) za a rarraba wa jihohin.

Tun a watan Yuli ne Ministar Kuɗi Zainab Ahmad ta faɗa wa majalisar cewa za a fara zarar kuɗi daga asusun jihohin domin fara biyan bashin tallafin farko da aka ba su.

sai dai jihohin sun nuna turjiya tare da neman wani agajin, abin da ya sa aka ɓullo da agajin kasafin kuɗin kenan.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Rikicin APC :Ba za mu karbi hukuncin kotu ba-Ganduje

Published

on

Ganduje

Mukhtar Yahya Usman

Gwamatin Kano ta ce ba za ta amince da hukuncin da wata kotu a Abuja ta yi ba da ya rushe zaben shugabancin jam’iyyar APC da tsagin gwamnati ya gudanar.

KANO FOCUS ta ruwaito kwamishinan shari’a na jihar Kano Barisster Musa Abdullahi Lawal ne ya sanar da hakan ga manema labarai ranar Talata.

Kwamishinan ya ce lauyoyin gwamnati sun fara nazaratar hukuncin tare da daukar matakin da ya da ce.

Ya ce sunyi mamakin hukuncin kuma ba za su karbe shi ba, a cewarsa lokacin da aka gudanar da zabukan a matakan mazabu babu wadanda suka yi nasu daban.

A don haka ya ce basu ga dalilin da yasa aka rushe shugabanci Abdullahi Abbas ba.

Barista Lawan yace za su duba yadda aka yi masu karar suka sami sakamakon zabukan da aka gudanar har suka gabatarwa kotu, da ta amince dasu.

Continue Reading

Hausa

Yanzu-yanzu-Kotu ta rushe shugabancin Abdullahi Abbas

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Wata kotun tarayya dake Abuja ta rushe zaben shugabancin jam’iyya APC da tsagin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya gudanar.

KANO FOCUS ta ruwaito mai shari’a Hamza Mua’zu ne ne ya rushe zaben a zaman kotu na yau  Talata.

Haka kuma mai shari’ar ya tabbatar da zaben da tsagin tshohon gwamnan Kano Ibrahim shekarau ya gudanar.

A cewar mai shari’ar zaben na bangaren Shekarau ya samu sanya hannun mutum 7 daga cikin wadanda uwar jam’iyyar ta turo jihar Kano domin gudanar da zaben.

Cikin abinda tsagin Shekarau ya gabatar, gaban kotun shi ne tsagin na gwamna Ganduje bai gudanar da zaben matakin kanan nan hukumomi da mazabu ba.

Idan za a iya tunawa a watan da ya gabata ne aka gudanar da zaben shugabancin jam’iyya APC a jihohin kasar nan ciki har da nan Kano.

Sai dai a nan Kano an samu rashin hadin kai tsakanin mambobin jam’iyyar.

Hakan ta sanya gwamna Ganduje ya gudanar da zaben tare da wadanda ke goya masa baya a wani wuri daban.

Yayin da Malam Ibrahim shekarau ya gudanar da nasa zaben da a wani wurin daban

Haka zalika tsagin na gwaman Ganduje ya zabi Abdullahi Abbas  a matsayin shugaba, ya yin da tsagin Ibrahim Shekarau ya zabi Ahmad Haruna Zago a matsayin shugaba.

Continue Reading

Hausa

Yanzu-yanzu: Sarkin tsaftar Kano ya rasu

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Allah ya yiwa Sarkin Tsaftar Kano Alhaji Ja’afaru Ahmed Gwarzo rasuwa.

KANO FOCUS ta ruwaito Sarkin Tsaftar ya rasu ne ranar Laraba a kasar Saudiyya.

Daya daga cikin ‘yan uwan marigayin Alhaji Nasiru Sani Gwarzo ne ya tabbatar da rasuwar tasa ga manema labarai.

Sarkin tsatar ya rasu ne bayan ‘yar gajeriyar rashin lafiya a kasa mai tsarki da ya tafi domin aikin umara.

Kafin rasuwarsa, Sarkin shi ne mataimaki na musamman ga gwamnan Kano Abdullahi Ganduje kan rigakafin cutar shan Inna.

Continue Reading

Trending