Hausa
Alkalancin wasan Kwallon kafa a Najeriya
Jamilu Uba Adamu
Alkalancin wasan Kwallon kafa abu ne da ya jima yana bawa masu shugabanci na harkokin wasan kwallon kafa matsala a Najeriya.
An jima ana samun korafe-korafe kan zargin masu alkalancin wasan kwallon kafa da karbar na-goro, musamman a gasar ajin kwararru ta kasa, Firemiya lig.
Alkalancin wasan Kwallon kafa abune mai mahimancin gaske, idan akai la’akari akan yadda yake karawa wasan Kwallon kafa armashi idan akayi alkalancin wasan bisa adalci, da kuma akasin hakan idan aka nuna son zuciya.
Sakamakon wasannin da aka yi a makon da ya gabata lokacin da aka fara kakar wasannin 2021/2022 na gasar Firemiya lig ya tabbatar da wannan batu.
Kungiyar Kwallon kafa ta Mountain of Fire dake birnin Ikko ta fafata da Kungiyar Kwallon kafa ta Remo, indai tai rashin nasara. Kungiyar Remo ta bugeta da ci biyu da nema ( 0 : 2 )
Haka kuma Kungiyar Kwallon kafa ta Katsina itama tai rashin nasara a gidanta bayan fafatawar ta da Kungiyar Kwallon kafa ta Enugu Rangers da ci biyu da daya ( 2-1 )
Itama dai Kungiyar Kwallon kafa ta Lobi Stars dake Garin Makurdi tayi kunnen doki a gwabzawarta da Kungiyar Kwallon kafa ta Rivers ta garin Fatakwal, daya da daya ( 1:1 )
Wasan Heartland ta owerri da Nassarawa United na Lafiya, jihar Nasarawa shima kunnen doki akai a tsakani ( 3:3 )
Gombe United itama dai kunnen Doki tai ( 0:0 ) a wasanta da Shooting Stars na Birnin Ibadan.
Abun dubawa anan shine, duk kungiyoyin nan na sama sun fafata a gidane amma basu sami sa’ar cin wasan su a gidan ba.
A yan shekarun baya mafi yawan masu hasashe da bibiyar Kwallon kafa, a kasa Najeriya na ganin cewar abu ne mai wahala wata Kungiyar Kwallon kafa ta samu nasara a wajen gidanta.
Sai dai kuma gashi alamu sun fara nunawa cewar hakan zai iya canjawa bisa la’akari da yadda shugaban kwamitin nada masu alkalancin wasan na Kasa Shariff Rabiu Inuwa Ahlan ya jajirce wajen kokarin ganin ya dakile waccan matsala.
A wata zantawa da na yi dashi, na tambayeshi akan cewar ; wane mataki yake dauka na ganin ya kawo gyara a harkar alkalancin wasan Kwallon kafa?
Cewa ya yi” Kullum kiran da nake yi wa masu alkalancin wasan Kwallon kafa shine, su tsaya akan gaskiya da adalci.”
Yakara da cewar, duk wanda ya samu da rashin gazawa ko son rai ba sani ba sabo kwamitin sa zai hukunta shi, koda kuwa dan gidan su ne.
Wannan mataki da Shariff Rabiu Inuwa Ahlan ya dauka ya fara haifar da da mai ido. A wasan farko da aka fafata an fara ganin ala’amun canji.
Fatan mu dai Allah ya bashi ikon cigaba da tsabtace harkar alkalancin wasan Kwallon kafa a Najeriya.
Jamilu Uba Adamu
Mai Sharhin wasan Kwallon k’afa ne
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Kwankwaso Congratulates Gov. Yusuf on NUT Award for Education Reforms
Former Kano State Governor and National Leader of the New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, has congratulated the current governor, Abba Kabir Yusuf, on receiving the prestigious NUT Golden Award from the Nigeria Union of Teachers (NUT) in recognition of his significant contributions to the education sector.
In a message posted on his verified X (formerly Twitter) handle, Kwankwaso commended Governor Yusuf for his unwavering dedication to revitalizing Kano’s education system.
He described the governor as a “game changer” in the sector and encouraged him to remain steadfast in pursuing his educational reforms.
“Congratulations to His Excellency Abba Kabir Yusuf on the NUT Golden Award for his achievements in the education sector,” Kwankwaso wrote.
He further urged Governor Yusuf to strengthen his commitment toward achieving his broader goals in education reform.
The award was presented during the 2024 World Teachers’ Day celebration, which took place at Eagle Square, Abuja.
Organized by the NUT in collaboration with the Federal Ministry of Education, the event brought together teachers and educational leaders from across Nigeria to recognize and celebrate significant achievements in education reform.
Governor Yusuf was honored with the NUT Golden Award for his transformative efforts in rescuing Kano’s education system, which had suffered from years of neglect.
His administration has been lauded for implementing policies aimed at improving school infrastructure, increasing access to quality education, and ensuring the professional development of teachers in Kano.
This recognition comes as part of a broader acknowledgment of his leadership and commitment to enhancing educational opportunities for all in the state.
The event, which marked the 2024 edition of World Teachers’ Day, highlighted the importance of teachers and their role in national development, with the NUT acknowledging the critical support of political leaders like Governor Yusuf, who are spearheading reform efforts.
The governor’s administration has undertaken various initiatives to address the challenges in Kano’s education system, including rebuilding dilapidated schools, recruiting more teachers, and prioritizing student enrollment, especially for girls.
Governor Yusuf’s receipt of the NUT Golden Award serves as a milestone in his administration’s ongoing efforts to reposition Kano as a leading state in education, setting an example for others across the country. His reforms have drawn praise.