Connect with us

Hausa

Siyasar da za a yi a Kano 2021-2023

Published

on

Malam Ibrahim Shekarau da Engr. Rabiu Musa Kwankwaso

Bello Muhammad Sharada

Tun a bara a watan Disamba na sha alwashin zan yi rubutu da  lakabi na sama. Abubuwa da yawa sun faru har suka kawo wannan jinkiri, YAU ga shi zan sauke wannan nauyin cikin yardar Allah.

A Disambar da ta gabata na kudurce magana ne akan yadda za ta kasance a Kano, bayan na yi nazarin yadda aka gudanar da zabukan ciyamomi na APC. Cikin ikon Allah kuma a jiya da daddare Alhaji Murtala Sule Garo, kwamishinan kananan hukumomin na jihar Kano ya sulale bayan kowa ya watse ya jagoranci ciyamomi na kananan hukumomi 44 ya ziyarci gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin yi masa ta’aziyya na mutuwar kaninsa shakiki Muhammad Inuwa.

Domin mu sani wadannan ciyamomi sune wanda Hajiya Gwaggo uwar Kanawa da Alhaji Murtala Sule Garo da Alhaji Abdullahi Abbas suka dora akan mulki watanni 11 da suka shude. Haka kuma sune wakilai da ake zato za su yi wa Kwamanda aiki a takarar gwamnan Kano ta 2022-2023 a bisa tsarin Farfesa Hafsat Ganduje, mai dakin gwamna Ganduje.

Wannan ta’aziyya rokon iri ce. Sharar fage ne. Sake lissafi ne. Ni haka na fassara ta. Abin da na fahimta an tara ‘yan tamore, masu yin siyasa bukata, masu yin siyasar kwadayi. Rakuma da akala.

Sai dai irin wannan yanayin a gurina abin farin ciki ne Kwankwaso ya bada auren ‘yar Shekarau. Abin dadi ne Ganduje ya je har gida ya yi wa Kwankwaso ta’aziyya. Gungun yan Gandujiyya su yi takakkiya gaishe da madugu.

Babban kuma farin ciki shi ne, za a daina fadan siyasa na matasa. Za a sassauta jagaliya a fili da rediyo da New Media. Magoya baya zasu rage tsawo na so da kiyayya. Za a koma kan gundarin siyasar manufa da akida da ‘yanci, a wurgar da tumasancin siyasa da biyan bukata.

A tsawon shekara shida zuwa bakwai na mulkin Baba Ganduje kowa zai ba shi shaidar yana zuwa gaisuwar mutuwa da jana’iza da dubiyar maras lafiya da jaje da shi da matarsa, kuma komai kankantar gudunmawa in ta taso zai bayar.

Ba a taba yin gwamna a Kano da ya samu kuri’ar cin zabe ba irinta Ganduje. Ya samu kuri’ar sama da miliyan daya da rabi a zabensa na 2015. Sannan shi ne kadai da ya yi gwamna karo na biyu tare da goyon bayan kowane tsagin siyasa in banda Kwankwasiyya. Sai da ya shawo kan kowa ya bi shi. Amma ba wani gwamna da ya tara bakin jini da hamayya a Kano kamarsa. A tsawon mulkinsa abu guda biyu ya yi wadanda suka jawo masa son barka. Na farko ya cire Sarkin Kano Halifa Muhammad Sanusi II ya kafa sabbin masarautu guda biyar. Na biyu ya dauki mataki akan Sheikh AbdulJabbar Nasir Kabara.

Sai dai kuma faifan bidiyon da aka yada yana cusa Dala a cikin aljihunsa da dan cikinsa da ya kai shi kara EFCC da shigar matarsa dumu-dumu da karfin ikon da take da shi a kowacce harka ta mulkinsa da sakarwa Murtala Sule Garo da Abdullahi Abbas kowacce sabga ta jam’iyyar APC da dora marasa kwarewa a madafun iko, sannan duk harkar kasuwanci da walwala da tausayi da aikin gwamnati da muwalatin ‘yan siyasa babu wata kulawa. Uwa-uba kuma babu wani mai girma da daraja da dattaku a Kano, kowa banza ne, ga kuma musibar tattalin arziki da tsaro su suka dada dagula shirin gwamna Ganduje.

Kanawa bamu da jiha sama da Kano. Duk balokokon da nake yi da masu irin ra’ayina, muna yi ne, don ta bunkasa, tsarin ya amfani al’umma, kuma dukiyar da aka baiwa Kano a yi amfani da su ta hanya mai kyau.

Ina sha’awar jihar Kano ta zama zakara akan sauran jihohi ta fuskokin rayuwa, ina so a rika buga misali da Kano a cikin alheri, ina son Kano ta zama abin koyi da kwatance a cikin sauran takwarorinta. Muna jin labarin jihohi a duniya kamar Selangor a Malaysia da California a America da Taiwan a China da Madina a Saudi Arabia. Haka muke son a ce Kano a Najeriya.

Idan Allah ya nufa nan da watanni takwas za a fitar da wanda zai gajeka a Kano. Cikin watanni masu zuwa hayaniyar siyasa da karbar madafun iko shi ne zai mamaye komai. A shekara 22 da dawowar mulkin farar hula a wannan jamhuriya, da kai aka yi komai. Ka zarce sittin, yanzu ka haura 70, ka doshi 80,  ka san komai kuma ka ga komai. A  cikin shekara 22 ka nuna kwarewar ka a likimo, kai gwani ne.

Bari mu dan yi ratse, mu waiwaya baya. Bayan faduwar PDP a zaben 2015, an rubuta littafai manya da suka shafi siyasar jam’iyyar PDP da mulkin Goodluck Ebele Jonathan. An yi tsokaci kan sababin da ya kawo faduwar PDP bayan shekara goma sha shida a mulki. Na karanta littafai hudu, da suka hada da Against the run of play na Olusegun Adeniyi 2017 da On A Platter of Gold

na Bolaji Abdullah 2018 da My Transition Hours na Goodluck Ebele Jonathan 2018 da Burden of Service na Mohammed Bello Adoke 2019, in ka cire wanda Jonathan ya rubuta da kansa, kaf dinsu sun dangata rawar da mai dakin Jonathan Madam Patience ta taka ya jawo faduwar GEJ/PDP. Matsalar Ganduje bayan ta ‘yan Kwankwasiyya ta Goggo ita ce ta biyu.

 A bana lissafin siyasar Kano sabo ne fil kuma salone da zai zo ba a san irinsa ba a baya. Za a ga abubuwa na siyasa na daban. Idan lokacin ya kara fadada kada a yi mamaki. An samu juyin bukata da yanayi.

Zabi biyu ne da masu lura da sha’anin siyasar gwamnatin tarayya  a Kano suke da shi. Bukatarsu ita ce su samu kuri’a mai kauri daga Kano kowa ye ma zai zama gwamna ruwansu. Zaben shugaban kasa da majalisun tarayya shi za a fara yi.

Zabin kuwa sune ko dai su saka baki bangaren G7 su karbi ragamar Kano su tankade Ganduje can, as-as haihata-haihata, sannan su lallaba su jawo Kwankwaso a hadu guri guda, ko kuma a  watsawa G7 kasa a ido a tabbatar da duk wani tsari da gwamna Ganduje ya zo da shi.

Menene babbar bukatar Kwankwaso? Yana son zama shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ko ministan Abuja. Sannan yana son wanda duk zai zama gwamnan Kano daga Kwankwasiyya zai fito. Mecece bukatar Ganduje da Goggo, su dora gwamna da zai rufa musu asiri da kare mutuncinsu in sun bar gidan gwamnati, daya daga cikin ‘ya’yan Ganduje ya samu zababben kujera, shi kansa ko ya zama mataimakin shugaban kasa ko Sanatan Kano ta arewa, matarsa kuma ta zama Sanata daga Jigawa.

Mecece bukatar ‘yan G7 shin Barau I. Jibrin ko Sha’aban Ibrahim Sharada ko Shehu Dalhatu ya zama gwamna? Shekarau ya koma Sanatan Kano ta Tsakiya? Abduwa da Dederi da Jobe su koma kan kujerunsu?. Wannan ba ita ce manufar da ya kamata mu dora tunani na al’umma a kai ba. Yanzu burin da ya zamar mana wajibi shi ne; ceto Kano ta zama ta mutanen Kano, harkokin siyasar Kano su kasance a doron dimokuradiyya da ‘yanci da ci gaba da mutunci da zaman lafiya. Babban aikin da za a sanya a gaba shi ne bukatar yadda za a farfado da Kano ta koma matsayinta na asali har ta  zarce kowa a kasuwanci da ilimi da sana’a da fasaha da sarauta da addini da al’ada da lumana da zaman lafiya. A rinka alfahari da ita a duniya.

Wannan burin ya fi karfin Kwankwaso da Kwankwasiyyarsa. Ya fi karfin Shekarau da Mundubuwarsa, burine na dindindin domin Kanawa da Najeriya.

Bello Muhammad Sharada

Shi ne Sakataren dake kula da walwalar ‘Yan Jam’iyyar APC (State Welfare Secretary) na Jiha tsagen Ahmadu Haruna Zago.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.

Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .

Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.

“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.

Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun  da basu samu damar biya ba a baya.”

Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A  bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari,  gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.

“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen  ciyar da al’umma.” Dangote.

 

Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.

“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da  neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”

Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada  rade-radi da jita-jita.

Continue Reading

Hausa

A kwanaki 100, VON ta farfaɗo, ci gaba ya bayyana da kuma fatan fin haka nan gaba – Ndace

Published

on

Jibrin Baba Ndace

 

A zafin ranar 29 ga watan Oktoba, 2023 ne aka samu wani canji na alheri da ya lulluɓe harabar Voice of Nigeria (VON) mai cike da sa’ida, sakamakon naɗin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi mini a matsayin Darakta-Janar na gidan rediyon na ƙasa, inda hakan ya zamto wani ɗamba na sauyin zamani a kafar yaɗa labaran ta ƙasa.

Bikin karɓar aiki daga hannun wanda na gada, Osita Okechukwu ya wuce a ce biki ne na sallamar ma’aikaci. Da ga karɓar shugabancin, guguwar sauyi ta fara kaɗa wa bayan na halarci taron AFRICAST 2023 a Legas. Sai na yi amfani da wannan damar na ziyarci cibiyoyin watsa shirye-shiryen tashar ta mu da ke Ikoyi da Ikorodu, inda hakan ya bani kwarin gwiwar cewa akwai dama mai ƙarfi da zan samu na kawo gagarumin ci gaba a gidan rediyon.

Dawowa ta shelkwatar VON da ke Abuja kuma, sai na fuskanci akwai aiki ja a gaba na. A yanayin lalacewar gine-gine da kayan aiki da na gani a cibiyar mu ta Ikko, sai na ji cewa ya zama wajibi na tashi tsaye na kawo gyara cikin gaggawa.

Duk da cewa kusan hakan yanayin ya ke a cibiyar watsa shirye-shiryen mu ta Lugbe a Abuja, akwai abinda ya bani ƙarfin gwiwa, shi ne wutar sola da na tarar. Sai na fahimci cewa wato akwai ɗumbin nasarori a VON, amma ana buƙatar jajirtaccen shugaba da zai farfaɗo da ita.

Bayan gine-gine da kayan aiki, ma’aikata su ne ƙashin bayan VON, sai dai kuma kash! akwai ƙarancin karsashi a tare da su ma’aikatan gidan rediyon a duka tashoshin namu na Abuja da Legas sakamakon rashin biyan su alawus-alawus na su da kuma kuɗaɗensu na ƙarin matsayi. Wannan ƙalubale ne da ya ke buƙatar kawo ɗauki cikin gaggawa domin samun gaba mai kyau.

Tun asali, kamata ya yi a samu wani kundi na tsare-tsare. Zaburar da ma’aikata na buƙatar ƙirƙiro da dabarun inganta walwalar su da kuma ƙara musu matsayi akai-akai lokacin da ya dace da kuma basu lambobin yabo bisa ƙwazon su a aiki. Kada kuma a manta da cewa haɗin kai tsakanin shugabanni da ma’aikata shi ne babban sinadarin kawo sauyi Na ci gaba a ma’aikata.

Halastar mu zuwa babban taron UNESCO na duniya, karo na 42 da aka yi a birnin Paris da kuma taron ranar rediyo na duniya a Dubai, ba wai mun je yawon buɗe-ido ba ne, sai dai wata babbar dama ce ta samun damammaki daga ƙasashen duniya. Waɗannan tarukan wata babbar dama ce ta nuna wa duniya irin ƙwazon VON na watsa shirye-shirye daidai da yadda ya ke a duniya da kuma ƙulla alaƙa, duk a ƙoƙarin ta na zama a aji ɗaya da manyan kafafen yaɗa labarai na duniya.

Ganawar farko ta shugabannin VON da ta gudana a ranar 19 ga watan Disamba, 2023, ba wai an yi zaman hira ne kawai ba, sai dai zaman ya kasance wata ɗamba ce aka kafa wajen samar da haɗin gwiwa domin fitar da dabarun aiki da za su ƙara taimaka wa gidan rediyon ya cimma muradun sa.

Aiyuka na bi-da-bi me ya haifar da nasarar da mu ka samu ta ganawa da kwamitin majalisar dattawa kan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma, kare kasafin kudin da mu ka yi wa kwamitocin majalisar dattawa da na majalisar wakilai da kuma ziyarar aiki da mu ka kaiwa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris. Waɗannan aiyukan sun kasance tubalin mu na gina alaƙa, wacce za ta samar mana da taimako da kuma fahimtar juna.

Hakazalika, alaƙar da mu ka ƙulla da ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu, da suka hada da Thunderbird, Image Marchants Promotions Limited, SEMEDAN, GOTNI, NIPR, Ciyaman na NUJ a Minna da kuma wakilci da ga Dangote Group da Jaiz Bank, ba wai ziyara ba ce kaɗai, sai dai sun zamto tattaunawa da za su buɗe kofa, su gina mana gadoji da kuma alaƙa da za su taimaka wa VON ta kai gaci.

Sannan, ziyarorin da muka kai wa Media Trust, National Orientation Agency, News Agency of Nigeria, Nigerian Diaspora Commission da NTA da kuma manyan shugabannin sojoji ya nuna ƙwazon mu na kawo gyara mai inganci a VON tare da bata suffar da ta ke buƙata.

A kwanaki 100 na farko a matsayin Darakta-Janar, na bada umarnin cewa duk wani ɗan hidimar ƙasa (NYSC) da masu koyon aiki a VON, dole a basu horo na musamman, da nufin su ji a ransu kamar su ma ma’aikata ne a tsawon lokacin da za su yi a gidan rediyon. Daɗin daɗawa kuma mun ƙulla alaƙa da Guards Polo Club da ƙungiyar shugabannin ma’aikatu ta Afirka domin jawo hankalin al’umma ga irin aikace-aikacen VON.

Bayan duk wadannan, irin bayanan sam-barka da ke fitowa daga bakunan ma’aikatan VON masu albarka, ya ƙara mana ƙaimi da ƙwarin gwiwa. Maida hankali da mu ka yi wajen gyara lalatattun kayan aikin mu da neman tallafin gwamnati wajen farfaɗo da tashar mu ta Lugbe ya nuna yadda shugabancin mu ke da zuciyar kawo gyara da kuma ɗaukaka VON.

A yayin da muka cika kwanaki 100 da karɓar ragamar shugabancin VON, magana a ke yi ta fara ganin guguwar sauyi ta fara kaɗa wa. Kalubalen da mu ka taras ya zamto wani ginshiƙi na gyara mai inganci. Sannan, dabarun da mu ke ɓullo da su sau ɗau saiti na fito dartabar VON ba wai a matsayin shahararren gidan rediyo ba, har ma ta zamto a bar koyi a fannin watsa shirye-shirye a faɗin duniya. Yayin da ake ci gaba da samar da hanyoyin gyara, lokaci kaɗai mu ke jira da zai fito da VON da har karan ta zai kai tsaiko a idon duniya.

Mallam Jibrin Ndace shi ne Darakta-Janar na VOICE of Nigeria, VON. Tashar watsa labarai na duk duniya ta Nijeriya.

Continue Reading

Hausa

Gwamna Abba Kabir Yusuf: Kano na Bukatar Sabuwar Alkibla!

Published

on

Farfesa Faruk Sarkinfada

 

Bayan nasarar da Allah Madaukakin Sarki ya baiwa Gwamnan jihar Kano Eng Abba Kabir Yusuf a kotun koli ta Nigeria bisa tabbatar da zaben sa, jihar Kano na bukatar sabuwar alkiblar jagoranci da ta gaza samu tun dawowar mulkin demokradiyya a shekarar 1999.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na bukatar assasawa da gudanar da jagorancin da zai tabbatar da zaman lafiya da ci gaba da bunkasar arzikin jihar kano ta hanyar dinke baraka ta bangarori da dama, musamman na siyasa, malamai da masarautu, don samun nasarar gudanar da mulkin adalci ga jama’ar jihar Kano. Mai girma Gwamna ya na da kyakyawan abin koyi daga rayuwar fiyayyen halitta, Annabin mu Muhammadu tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi, dangane da kalubalen da ya fuskanta a karon farko, da kuma gada bisani yayin da budi da nasarar Ubangiji Allah su ka saukar masa.

A karon farko, yayin halin tsanani da jarrrabawa na tsawon shekaru goma sha uku a garin Makka, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya rayu cikin kyawawan dabi’u, kamar dogaro ga Allah, juriya, rashin tsoro, hakuri, da su ka bayyana yayin halin gwagwarmaya wadanda ba za a iya fahimtarsu ba a cikin halin yalwa da iko. Ya kuma ci gaba da isar da sako ba tare da gajiyawa ba duk da rashin yawan mabiya da kuma tsangwama da ya yi ta fuskanta. Wannan juriya da tsaiwa tsayin daka akan kira ga Allah ya ja hankulan da yawa daga cikin wadanda ba su bada gaskiya ba suka musulunta. A kashi na biyu na rayuwarsa, wato lokacin da nasara ta samu, iko da mulki suka samu Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya bayyana kyawawan halaye kamar su hangen nesa, yafiya, kauna, saukin kai, da jajircewa, wadanda su ka kara jawo hankulan mutane da dama ya zuwa musulunci. Ya yafe wa wadanda suka nuna masa tsana da kiyayya, ya bada cikakken tsaro da kariya ga wadanda suka fitar da shi daga mahaifarsa (Makka), ya ba da dukiya mai yawa ga matalautan su. Wadannan kyawawan dabi’u ya sa ko da wadanda ke adawa su ka karbi kiran Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma duk tsirarun makiyansa suke zama masu kaunarsa daga bisani.

Hakika mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf na da kyakyawan darussa daga rayuwar Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata gare shi a halin tsanani da ya shiga tun zaben 2019, sanda bai sami nasarar zama gwamnan Kano ba, da kuma halin nasarar sa a yanzu da ya yi nasara a zaben 2023 kuma kotun koli ta Nigeria ta tabbatar masa da wannan Nasara. Gwamna Abba Kabir Yusuf na bukatar dinke baraka a wannan lokaci, ta hanyar yafiya, musamman ga wadanda su ka tsangwame shi a baya da kuma kyakyawan hangen nesa, nuna kauna, saukkin kai, da jajircewa, da kare hakkin duk wani mai hakki ba tare da nuna bambanci ta kowannen bangare ba.

Jinina ga mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf don kafa majalisar dattawan Kano (KEC), wadda za ta zama mai ba da shawara ga gwamnati, kuma ta hada da muhimman jagorori ‘yan asalin jihar Kano, da kuma tshofaffin gwamnonin ta, Dr Rabiu Musa Kwankwaso, Mallam Ibrahim Shekarau da Kuma Dr Abdullahi Umar Ganduje. Har way au mu na kira da babban murya musamman ga wadannan shuwagabanni uku da su ka mulki jama’ar Kano tun daga 1999 zuwa yanzu, su kau da banbance-banbancen da ke tsakanin su wajen tallafa wa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf don samar wa jihar Kano sabuwar alkiblar shugabanci na gari. Hakika a tsawon shekaru kusan 24, kowanne daga cikikin wadannan shuwagabanni ya ba da gudunmawa, gwargwadon ikon su, wajen samar da ayyukan ci gaba ta bangarori da dama a jihar Kano. A yanzu ne mutanen Kano su ka fi bukatara gudunmawarku wajen wanzar da abubuwan alkhairai da ku ka dasa, da kuma cike gurabun da ku ka bari, don bunkasar jihar Kano a Nigeria da duniya gaba daya. Hakika za su zamanto ababen alfahari a gare mu in har wannan tsari ya tabbata.

Shi fa kyakyawan shugabanci mai dorewa, ya na samuwa ne lokacin da aka samu jagororin da su ka cancanta daga cikin al’uma, kuma ma su zartar da kudurorin da su ka dace a lokutan da su ka dace, domin tunkara da warware matsalolin da ke addabar al’umar su a wannan lokaci. Lallai Kanawa na matukar kishirwar ingantaccen shugabanci tare da hadin guiwar dukkanin masu ruwa da tsaki daga shuwagabannin siyasa, malamai, sarakuna, ‘yan kasuwa, ma’aikata, ma su manya da kananan sana’o’i da matasa da dukkanin jama’a. Don haka dole ne a rage, ko a kawar da banbance-banbancen siyasa da kiyayya a tsakanin shuwagabanni da mabiya a wannan jiha tamu, domin mu tunkari manyan matsalolin mu na cin hanci da rashawa, magudin zabe, matsanancin talauci, tabarbarewar ilimi, lafiya da tattalin arziki da kuma siyasar rashin kishin talaka ta hanyar yawan ketarawar daga jam’iyya zuwa wata jam’iyyar don maslahar kawunan su.

Kano na bukatar sabuwar alkibla don wanzar da matsayin ta na cibiyar kasuwanci da al’adu da siyasar Arewacin Nigeria. Allah Madaukakin Sarki ya shiryar da shuwagabannin mu, Ya ba mu lafiya da zaman lafiya da yalwar arziki mai amfani.

Ameen.

Farfesa Faruk Sarkinfada
fsarkinfada@yahoo.co.uk

Continue Reading

Trending