Connect with us

Hausa

Marigayi Alhaji Bashir Usman Tofa: Mutum Mai Kyawawan Halaye Da Dabi’u Nagari

Published

on

Daga Imam Murtadha Gusau

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun! Lallai daga Allah muke, kuma zuwa gare shi makomar mu take!!

Allahu Akbar! Yau litinin, 03/01/2022, mun wayi gari da wani mummunan labari mai sosa rai. Labari mai cike da bakin ciki marar iyaka. Labarin da ya girgiza arewacin Najeriya, da Najeriya baki daya. Labarin da yasa miliyoyan ‘yan Najeriya zubar da hawaye, domin tausayi da jimami, wato labarin rasuwar daya daga cikin dattawan arewa, masu kishin addini, masu kishi da tausayin talaka, masu kishin kasar su Najeriya da son ci gaban ta, kuma masu kishin yankin arewa; sauran ‘yan mazan jiya, baya-goya-marayu, wato Alhaji Bashir Usman Tofa.

Bashir Tofa ya rasu da asubahin yau litinin, bayan jinya da yayi na wasu kwanaki, kuma anyi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, a gidan sa dake Gandun Albasa, a cikin Birnin Kano. Jana’izar da dimbin al’ummah suka halarta.

Ina addu’a da rokon Allah ya jikan sa, ya gafarta zunuban sa, da kura-kuren sa, da kasawar sa. Allah yayi masa sakamako da Aljannah Firdausi. Allah ya albarkaci zuri’ar da ya bari, kuma Allah ya ba iyalan sa, ‘yan uwa, abokan arziki da al’ummar Musulmi baki daya, hakurin jure wannan babban rashi, amin.

Ya ku jama’ah! Lallai kyawawan dabi’u da halaye nagari na daga cikin muhimman abubuwan da addinin Musulunci ya ba fifiko, wanda ta hanyar mallakar su ne dan Adam zai iya samun tsira tun a nan duniya da kuma gobe kiyama. Kyawawan dabi’u da halaye nagari babbar alama ce da ke nuna nagartar mutum da kuma mutuncinsa. Ana gane mutumin kirki ta hanyarsu, kuma mafiya alherin Musulmi su ne wadanda suke da kyawawan halaye da dabi’u na gari. Kuma muminai masu cikakken imani wadanda Allah da ManzonSa suka fi so, kuma al’ummah suke kauna, sune masu kyawawan halaye da dabi’u na kwarai. Sannan kuma Musulmin kwarai shine wanda ya samu kyakkyawar tarbiyyah daga iyayensa, kuma ya mallaki wasu irin nagartattun dabi’u da halaye nagari abin koyi.

Allah Madaukaki ya yabi kyakkyawan hali da dabi’un Annabi (SAW) kuma Ya sanya shi ya zamo abin koyi ga dukkan Musulmi. Allah Madaukaki Yace:

“Kuma lallai, hakika kana a kan halayen kirki manya.” (Al-kur’an, 68:4)

Kuma lallai babbar manufar aiko Annabi (SAW) ita ce, ya dasa kyawawan halaye da dabi’u nagari tsakanin Musulmi, a cikin kowane fanni na rayuwarsu. Abu Hurairah (RA) ya ruwaito cewa:

“Manzon Allah (SAW) yace: “Hakika an aiko ni ne, domin in cika kyawawan halaye.” (Musnad na Imamu Ahmad)

A wata ruwayar Annabi (SAW) yace:

“Iyaka an aiko ni ne domin in cika kyawawan halaye.” (Muwadda Imamu Malik)

A wata ruwayar Annabi (SAW) yace:

“Hakika Allah Ya aiko ni ne domin in cika kyawawan dabi’u kuma in cika ayyuka na kwarai.” (Mujma’a al-Awsat)

’Yan uwa masu daraja! Kyakkyawar dabi’a a wurin Allah na nufin kayi riko da akida mai kyau da yin ayyukan Ibadah kamar yadda Manzon sa (SAW) ya koyar. A wurin mutane kuma, kyakkyawar dabi’a ko hali nagari, yana nufin ka zamo mai adalci, ka zamo mai tausayi, mai yafiya mai kirki, mai kyauta kuma mai hakuri a wurin mu’amala da su.

Kasancewar kyakkyawar dabi’a ko kyawon hali yana da matukar muhimmanci, sai riko da hali nagari ya zama wajibi a cikin addinin Musulunci. Manzon tsira, Annabi Muhammad (SAW) ya umarci Musulmi da su rika nuna halaye na gari a cikin kowane al’amari. Abu Zarril Ghifari (RA) ya ruwaito cewa:

“Annabi (SAW) yace: “Ka yi mu’amala da mutane da kyakkyawar mu’amala.” (Sunanut-Tirmizi)

Imam Ibn Al-kayyim yace:

“Addini gaba dayansa kyawawan halaye ne, don haka duk wanda yafi ka kyawon hali toh yafi ka a cikin addini.” (Madarij as-Salikin)

Kuma ya sake cewa:

“Kyakkyawan hali shine addini gaba daya.” (Madarij as-Salikin)

Abdullahi Ibn Amir ya ruwaito cewa, Manzon Allah (SAW) yace:

“Mafi alherinku shine mafi kyawun halinku.” (Buhari)

A wata ruwayar Annabi (SAW) yace:

“Mafiya cikar imani a cikin Musulmi, sune wadanda suka fi kyawon hali, kuma mafiya alherin cikinku sune wadanda suka fi kyautata wa matansu.” (Sunanut-Tirmizi).

Kuma a wata ruwayar Annabi (SAW) yace:

“Hakika, cikakkun muminai sune mafiya kyawun hali da kuma wadanda suka fi kyautata wa iyalansu.” (Sunanut-Tirmizi)

Abdullahi Ibn Amru yace:

“Manzon Allah (SAW) yace: “Shin in gaya maku mutumin da nafi so kuma yafi kusa da ni a ranar kiyama? Sune wadanda suke da kyakkyawan hali.” (Musnad Imamu Ahmad)

A wata ruwayar Annabi (SAW) yace:

“Hakika mafi soyuwa da kusanci da ni a taron Al-kiyama sune wadanda suka fi ku kyakkyawan hali. Kuma hakika mafiya zama abin kyama a wuri na daga cikin ku kuma mafiya nesa da ni a taron ranar Al-kiyama sune masu alfahari, masu almubazzaranci, masu girman kai.” (Sunanut-Tirmizi).

Domin yin koyi da yin biyayya da nuna da’a ga Allah da Manzon sa (SAW), da kuma girmama wadannan nassoshi, da girmama addinin Allah, yasa Alhaji Bashir Usman Tofa ya zamanto mutum mai kyawawan halaye da dabi’u masu kyau, kuma nagari.

A cikin shekaru ashirin da biyar da Allah ya hada ni dashi, tun daga 1997 zuwa yau da Allah ya karbi rayuwarsa, wallahi Allah shine shaida, ni ban san wannan bawan Allah da wasu munanan halaye ko dabi’u abin Allah waddai ba.

Allah yayi shi mai kyawawan halaye, da dabi’u masu kyau, wadanda duk wanda yayi mu’amala da shi, tabbas sai ya yabe shi.

Alhaji Bashir Usman Tofa zai baka shawara tsakanin sa da Allah, shawarar da wallahi ko dan cikinsa da ya haifa, iyakar shawarar da zai bashi kenan. Ba zai munafunceka ba, ba zai yaudare ka ba.

Idan aka kwana biyu bai ji ni ba, wallahi zai dauki waya ya kira ni, domin yaji ko lafiya. Kuma ban taba kiran sa yaki daukar kira na ba, duk da matsayin sa da girman sa, sai fa idan lokacin da na kira baya kusa da wayar, kuma idan ya ga kiran zai biyo ni da kira.

Duk lokacin da na shiga Kano, zan yi masa waya cewa na shigo, don haka zan zo in gaishe shi. Nan take zai sanar da masu gadi cewa, wane mai suna kaza zai zo, don haka ku bar shi ya shigo.

Duk Sallah karama da Sallah babba, sai yayi man sakon barka da Sallah.

Duk da wannan, a iya sani na da shi, Alhaji Bashir Usman Tofa mutum ne mai hakuri da yafiya. Mutum ne mai Ikhlasi (wato yin abu domin Allah). Shi mai kyakkyawar mu’amala ne ga ko wane mutum. Mutum ne mai son gyara a koda yaushe, mutum ne mai tsananin kishin addinin sa, mai kishin kasar sa mai kishin yankin sa na arewa.

Mutum ne shi mai kaunar Malaman addini, kuma mai yawan mu’amala ta mutunci da su.

Mutum ne mai yawan umurni da a aikata kyakkyawan aiki da kuma kokarin hani akan aikata mummunan aiki.

Alhaji Bashir Usman Tofa mutum ne mai yawan kiyaye harshensa daga surutu da maganganun banza, musamman marasa amfani. Amma fa idan a wurin fadar gaskiya ne, to baya shakkar ko wane mutum ko yaji tsoron sa. Ya kasance mutum mai yawan ibada, mai tausayi da saukin kai.

Bashir Tofa mutum ne mai tsantseni. Mutum ne marar rowa, wanda baya hana abun da aka roke shi, ko aka tambayeshi, sai fa idan baya da shi ne.

An shaide shi da cewa shi mutum ne mai karfin imani da tawakkali. Mutum ne mai tausayin marayu da son yara kanana. Mutum ne mai yawan yin rangwame da afuwa ga mutane, mai tsoron Allah da kamewa.

Alhaji Bashir Tofa mutum ne mai ciyar da abinci ga mabukata, mai son taimakon marasa karfi. Mutum ne mai fadin gaskiya komai dacinta, kuma baya shakkar duk abinda zai same shi wurin fadin gaskiyar. Yana da himma da kokari wurin girmama iyakokin Allah da dokokin sa. Shi mai sakin fuska ne ga mutane, miyagun mutane ne kadai baya saurara masu, kuma baya son zalunci da azzalumai. Haka nan baya kaunar rashin gaskiya, baya kaunar miyagun ‘yan siyasa da ashararai cikin al’ummah.

Ya kasance mutum mai rikon amana da cika alkawari; sannan gashi jarumi, mai karfin jarumtaka da rashin tsoro. Mutum ne karimi mai yawan karamci da hakuri tare da jurewa akan haka. Kuma gashi mutum yawan kunya.

Ya kasance mai kankan da kai, mai tawadu’u, mai yawan nuna rahama, tausayi da jin kai ga talakawa da kuma marasa galihu, kuma ga shi mai saukin kai, mai yafiya da hakuri kuma adali, mai tsananin tsoron Allah, kuma mai wadatar zuci da hakuri da kadan.

Ya kasance mai son yin alheri ga kowa da kowa; Musulmi da wanda ba Musulmi ba, kai hatta ma makiyansa alhairan sa sun kai gare su.

Bashir Tofa mutum ne mai son zaman lafiya, mai adawa da tsahin hankali ko rikici, ko zubar da jinin bayin Allah.

Bai nesanta kansa daga talakawa ba, yana tare dasu a koda yaushe, yana cudanya da su, kuma yana sauraron koke-koken su.

Shi mai kokari ne wurin zuwa gaishe da marasa lafiya, kuma ya biya kudin maganinsu (Hospital Bills), yayi masu alheri mai tarin yawa, Musulmi ne su ko kuma wadanda ba Musulmi ba. Sannan ga rashin girman kai, da yin godiya ga duk wanda yayi masa alheri, da kuma kokarin saka masa shi ma, da abunda zai iya.

Bashir Tofa mutum ne mai tsananin son dukkanin wani abu mai kyau da tsabta da kuma kamshi. Baya son datti, da kazanta da wari ko doyi.

Mutum ne mai son ganin al’ummah sun hada kai, baya son rarrabuwa da fada tsakanin al’ummah. Yana yawan shiga tsakani da kuma kokarin yin sulhu da sasanci tsakanin mutane.

Alhaji Bashir Usman Tofa yayi wa ilimi hidima matuka. Zaka fahimci wannan ta hanyar karanta rubuce-rubucen sa. Ya rubuta littafai masu dimbin yawa. Duk littafan da ya rubuta babu wanda bai bani ba da hannun sa. Kuma ya bani masu tarin yawa yace a raba wa bayin Allah masu son karatu.

A duk lokacin da ka samu damar yin fira da shi, wallahi zaka ji cewa damuwar sa har kullun ita ce, yaya za’a yi al’amarin kasar nan ya gyaru? Yaya za’a yi a samar da shugabanni nagari? Yaya za’a yi a samu zaman lafiya a arewa da Najeriya baki daya? Yaya za’a yi rayuwar talaka ta inganta? Yaya za’a yi al’ummah su hada kai domin a zauna lafiya? Kai ma a sani na, wallahi ya taba yin amfani da kudin aljihun sa, da dukiyar sa, yayi yawo, ya zagaya kasar nan, ya gana da Malamai daban-daban, wurin kokarin ganin ya hada kan Malaman addini.

Sannan ni dai a iya sani na, shine kadai mai kudi, kuma babban mutum, da ya samar da tsarin yin taruruka, tun daga matakin anguwanni. Kuma ko wane taro za’a yi da shi ake yi, tare da talakawa, wani lokaci ma a gidan sa ake yin taron. Duk wannan yana yi ne domin kokarin ciyar da al’ummah gaba.

Wadannan su ne kadan daga halaye da dabi’un Alhaji Bashir Tofa, wadanda Allah ya fahimtar da ni, a cikin ahekaru ashirin da biyar da nayi ina hulda da shi; dabi’un da wallahi duk wanda yayi hulda da shi, ko yake hulda da shi, zai shaida hakan.

Fata na, da roko na, shine, Allah yasa kyawawan aikin sa nagari su bishi. Allah ya haskaka makwancin sa, ya yalwata kabarin sa, amin.

Lallai kam al’ummah tayi babban rashi. An samu wani irin wawakeken gibi, wanda Allah ne kadai yasan yadda za’a cike shi.

Wassalamu Alaikum

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, Babban Limamin Masallacin Juma’ah na Nagazi-Uvete, da Masallacin Alhaji Abdurrahman Okene, da ke Okene Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa ta wannan lambar waya kamar haka: 08038289761.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Shugabannin Fulani sun goyi bayan takarar Tinubu

Published

on

Aminu Abdullahi

 

 

Shugabannin Fulani wato (Ardo) daga sassa daban-daban na Najeriya sun jaddada goyon bayansu ga dan takarar jam’iyyar APC Sanata Bola Ahmed Tinubu a wani taro da suka gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar lahadi.

A taron da suka yi tare da hadin gwiwar Kungiyar Sabuwar Arewa wato “Arewa New Agenda” shugabannin sun yi alkawarin yin amfani da ‘yan kungiyar 33,661 wajen tattaro sauran ‘yan uwansu Fulani domin su zabi Sanata Bola Tinubu.

A lokacin da yake nasa jawabin bayan an kammala al’adar Fulani ta rabon goro ga mahalarta taron, shugaban Kungiyar Aliyu Liman Bobboi ya ce raba goron da aka yi yana nufin shugabannin za su koma gida su isar da sakon shawarar da aka yanke a wajen taron zuwa ga mabiyansu.

Ya kara da cewa taron an gudanar da shi ne domin su nuna wa duniya goyon bayansu ga Tinubu saboda sun yarda, sun kuma yi amanna da cancantarsa, suna kuma masu adduar samun nasara a zabe mai zuwa.

Ya kara da cewa Ardo a matsayinsu na shugabanni suna da ta cewa sosai akan wanda mutanensu zasu zaba, kuma suna da yakinin cewa magoya bayan nasu za su yi ma su biyayya.

Liman ya yi nuni da makusanta shakikai dake tareda Tinubu kamar Gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje, Abubakar Badaru na jigawa, tsohon shugaban EFCC Malam Nuhu Ribadu, da sauran manyan Fulani yace wannan na nuni ga yadda Tinubu ya dauki kabilar ta Fulani da muhimmanci.

Kungiyar ta shuwagabannin Fulani ta kuma bawa Tinubu sarautar Barkindo.

Gwamnan jahar kano Abdullahi Umar Ganduje da yake bayani ya yi tsokaci akan irin bajinta da kwarewa da kuma cancantar Tinubu da ya shugabanci Najeriya. Ya kuma kara da cewa Fulani a matsayinsu na kabila dake fuskantar barazana a sassa daban-daban, suna bukatar zabar shugaban da zai iya basu kariya.

Ganduje ya kara da cewa suna nan kan kokarin samarwa Fulani da wani tsari wanda zai bunkasa hanyoyin kiwo a duk fadin kasar nan.

A nasa bayani dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Sanata Tinubu ya yi tsokaci akan irin kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da mahaifiyarsa a bangare daya da kuma Fulani a dayan bangaren. Ya nuna cewa alakarsa da Fulani amana ce ta dindindin.

Ya kara jaddada niyyarsa ta samarwa Fulani hanyoyin kiwo na zamani da za su kawo cigaba da kuma yalwa ba tare da tsangwama ba.

Tinubu ya kara da cewa bai taba tsammanin zai hadu da bafulatanin da ya fi shi jin yaren yarbanci ba sai gashi yau ba zato ba tsammani ya hadu dasu. Ya ce wannan abun a yaba ne.

“Wannan itace irin Najeriyarda muke bukata, kasa daya al,umma daya.  Ina mai tabbatar maku idan da zamu kasance anan tsawon sa,o,I biyar iyakacindai zancenda zakucigaba da ji daga gareni kenan.  Ina mai matukar mika godiya da gareku.

“Tabbas makiyayan Najeriya na fama da matsaloli dabban dabban amma ina mai tabbatar maku da cewa munada tsari na musamman da zai magance wudannan matsalolin,’ a cewar Tinubu.

A nasa jawabin Malam Nuhu Ribadu ya bayyana Tinubu a matsayin mutumin da ya cancanta, ya dace wanda kuma zai iya kawo ci gaba mai dorewa ga kabilar ta Fulani.

Ya kuma yi godiya ga goyon bayan da suka bashi tareda alkawarin ba zai ba su kunya ba.

Continue Reading

Hausa

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, Baƙon Shehu Maghili

Published

on

Magaji Galadima

 

 

A ranar Litinin 12 ga watan Disamba 2022 gwamnatin ƙasar Aljeriya ta aiko da wani jirgi na musamman domin ya ɗauki mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zuwa ƙasar ta Aljeriya domin halartar taron duniya na musamman don tunawa da rayuwa da kuma aiyukan shahararren malamin addinin Musulunci sharifi kuma masanin falsafa  wato Shehun malami Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na goma sha biyar. 

Jigin ya tashi daga Kano da karfe 9:45 na safe. A cikin waɗanda suka samu alfarmar raka Sarki wannan tafiya akwai Sarkin Dawakin Tsakar-gidan Kano Alhaji Ahmad Ado Bayero hakimin Kumbotso da Ambasada Ahmad Umar Ɗanmalikin Kano da Dakta Ibrahim Ɗahiru Bauchi wanda ya wakilci Sheikh Ɗahiru Bauchi da Malam Isa Sanusi Bayero da Dakta Lawi Atiku Sanka da kuma ni Magaji Galadima Kachallan Kano, sannan sai wasu malamai da sharifai na Kano da kuma fadawa hadiman Sarki.

Jirgin ya ɗan yada zango a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar inda ya ɗauki Sultan na Agadas da Sarkin Sharifan ƙasar Nijar da sauran malamai da muƙaddamai da malaman jami’a. Sarkin Kano da ‘yan tawagarsa sun sauka a Aljiyas babban birnin Aljeriya da misalin karfe 5:00 na yamma inda manyan ministoci da jami’an gwamnati dana diflomasiyya da kuma manyan malamai suka taryi mai martaba Sarki da tawagarsa. Daga nan akayi jerin-gwano aka raka Sarki masaukinsa.

A rana ta biyu wato Talata Sarki da ‘yan tawagarsa suka fita zuwa wajen taron ƙasa da ƙasa da aka shirya domin tunawa da shahararren malamin addinin musulunci masanin falsafa kuma sharifi wato Shehu Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na sha biyar kuma har ya zo Kano zamanin Sarki Muhammadu Rumfa.

Al-Maghili ya zauna a Kano tsawon lokaci kuma ya bijiro da sababbin tsare-tsare ma su muhimmanci a fadar Kano, kana kuma ya yi rubuce-rubuce akan ibada da hukunci, sannan ya rubuta wani kundi da ya zama daftari na jagorar duk wani sarki na Kano da ma nahiyar yammacin Sudan.

Taron an shirya shi ne a babban ɗakin taro na ƙasar dake birnin Aljiyes.  A ranar buɗe taron Sarkin Kano da tawagarsa sun isa wajen da misalin karfe 9;00 na safe amma sai aka kaishi wani ɗaki ya zauna a kauwame har sai da ɗakin taron yayi cikar kwari sannan aka shigar dashi.

Toh dama an ɗauki makwanni ana ta yaɗawa a kafafen labarai cewa ƙasar ta Aljeriya zata karɓi bakuncin wani ƙasaitaccen Sarki mai alfarma da daraja daga garin Kano a Nijeriya, don haka mutanen ƙasar duk sun zaku suga wannan ƙasaitaccen Sarki. Saboda da haka yana shiga ɗakin taron sai duk aka tashi tsaye waje ya kaure da sowa da tafi, mata kuma na rabka guɗa, su kuma ‘yan badujala suka goce da wani irin take na musamman da ake kaɗawa mashahuran mutane in sun shigo wajen taro.

An ɗauki tsawon lokaci kafin a samu natsuwa lamurra su koma daidai sannan mai martaba Sarkin Kano figinai suka yi sayi ya zauna aka gyara aka kimtsa sannan aka fara gudanar da taro.

Daganan ne kuma sai aka fara jawabai, babban ministan harkokin addini na ƙasar shine ya wakilci shugaban ƙasa kuma yayi jawabin maraba ga mahalarta taron kana yayi godiya ta musamman ga Sarki Aminu Bayero a madadin shugaban ƙasa da al’ummar ƙasar baki ɗaya. Shima Sarkin na Kano  yayi jawabi inda ya nuna farin ciki da godiya ga gwamnati da jama’ar ƙasar baki ɗaya saboda kyakkawar taryar da aka yi masa, ya kuma isar da gaisuwar jama’ar masarautar Kano da Nijeriya baki ɗaya a garesu.

Sarkin ya yaba da hangen nesan waɗanda suka assasa wannan taro na tunawa da Shehu Maghili wanda yace yafi cancanta a kira shi da Bakano maimakon dan Aljeriya saboda da dalilai da dama. Ya baiyanawa mahalarta taron cewa a yanzu haka a cikin birnin Kano akwai unguwar Sharifai waɗanda asali jama’ar da suka zo Kano tare da Shehu Maghili sune ke zaune a wannan unguwa tun lokacin har zuwa yanzu, kuma shugabansu Sidi Fari shine Sarkin Sharifan Kano kuma yana da gurbin zama a majalisar Sarkin Kano.

A ƙarshen jawabin Sarki yayi godiya ga Allah wanda Ya ƙudura cewa a zamaninsa ne akayi wannan babbar hobbasa ta sake dawo da wannan tsohuwar alaƙa tsakanin Kano da Nijeriya da kuma ƙasar Aljeriya kamar yadda su Shehu Maghili suka shimfiɗa.

Daga nan kuma sai aka buɗe fage inda malamai da masana suka yita ƙwami akan tarihin rayuwa da rubuce-rubucen Shehu Maghili.

Bayan an tashi daga taron wannan rana ta farko, sai mutane suka yanyame Sarkin Kano, malamai da jami’an gwamnati da baƙi daga sauran ƙasashe kowa burinsa shine ya samu ya ɗauki hoto da Sarkin Kano.

Bayan an fito waje ma haka har zuwa inda ya shiga mota. Mu ma ‘yan kwarakar Sarki da kyar muka yakice ‘yan jarida masu son jin kwakwaf domin yawansu babu lokaci da zamu warware musu zare da abawa. Koda muka isa masauki sai muka tarar ashe tuni wasu jama’ar sun yi kwamba suna jiran isowar Sarki domin su samu su gaisa kuma su ɗauki hoto da shi.

 

Bayan ya shiga ɗaki kuma sai manyan malaman ƙasar su kuma suka yi layin shiga suna yiwa sarki addu’a har saida rana tayi gora sannan jami’an tsaro suka tare mutane suka hana su shiga don a kyale Sarki ya huta.

A rana ta biyu mai martaba Sarki da tawagarsa ya sake komawa wajen taron inda malamai suka ci gaba da gabatar da takardu.

Bayan anyi hutun zango na farko sai mai martaba Sarki ya fita domin kai ziyara ofishin jakadancin Nijeriya dake kasar ta Aljeriya.

Jakadiyar Nijeriya Hajiya Aisha Muhammad Garba ta taryi Sarki da tawagarsa kuma anyi jawabai masu muhimmanci.

Da maraice kuma har ila yau sai Jakadiyar ta shiryawa mai martaba sarki wata liyafar alfarma a gidanta inda aka gaiyaci ‘yan Nijeriya mazauna ƙasar Aljeriya da kuma wasu malamai daga Nijeriya.

A rana ta uku kuwa mai martaba Sarki ya halarci bikin rufe taron kuma abin ya ƙayatar ƙwarai musamman yadda Sarkin Kanon ya zama tauraro a wajen taron domin dai hankalin kowa na kansa tun daga farko har i zuwa lokacin da aka ja labulen rufe taron.

Da yammaci kuma sai shugaban ƙasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya gaiyaci Sarki Aminu zuwa fadarsa inda suka zauna suka yi zantuka na girma. Shugaban ƙasar yace yayi murna matuƙa da karɓar baƙuncin Sarkin, ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar tasu tana sane da tarihin masarautar Kano da rawar da Shehu Maghili ya taka wajen bunƙasa al’adu da addinin Musulunci a birnin Kano.

Shugaba Tebboune yace Sarkin Kano a wannan ziyara shi baƙon Shehu Maghili ne, duk da yayi wafati fiye da shekaru 600, wannan ziyara ta Sarki lallai Shehu Maghili shine sila.

Shi kuma a lokacin da yake maishe da jawabi Sarki Aminu yayi godiya ga Allah da Ya bashi ikon amsa gaiyatar shugaban ƙasar da kawo wannan ziyara, ya yabawa gwamnatin ƙasar Aljeriya saboda ɗawainiyar ɗaukar nauyin wannan taro mai muhimmanci.

Daga nan kuma sai yayi kira ga shugaban na Aljeriya da su haɗu su farfaɗo da hulɗar cinikayya da kasuwanci tsakanin Kano da Aljeriya wanda yace zai taimaka wajen ƙara yauƙaƙa danƙon zumunci tsakanin nahiyoyin biyu. Baya ga wannan kuma da yake ance lokacin iska ake cin ɗan jinjimi sarkin ya bukaci gwamnatin ƙasar ta Aljeriya da ta bawa ɗaliban jihar Kano tallafi na guraben ƙara ilmi a fannoni dabam-daban a jami’oin ƙasar inda shugaban ƙasar nan take yayi wuf yace ya amince da wannan shawara kuma yana jira in Sarki ya koma gida,  ya tsaro jadawalin yadda duk yake so ayi , su kuma in Allah Yaso zasu aiwatar. a nan dai akayi muwafuƙa duk shawarar tasu tazo daidai.

Daga nan suka yi bankwana cikin farin ciki da girmama juna.

A rana ta hudu mai martaba Sarkin Kano tare da wasu daga cikin ‘yan tawagarsa sun ziyarci garin Ain-Madhi wato ainihin garin da aka haifi Maulana Shehi Ahmadu Tijjani (RA) wanda ya kafa ɗarikar Tijjaniyya.

Sarkin ya ziyarci muhimman wuraren tarihi a garin sannan ya gana da manyan malamai da sharifai zuriyar Shehin inda suka yiwa Sarkin da Kano da Nijeriya  addu’oi na musamman.

A rana ta biyar Sarki ya kammala ziyarar kamar yadda aka tsara, don haka sai ya karyo linzami zuwa gida. Manyan jami’an gwamnati da malamai da kusoshin diflomasiyya da kuma jakadiyar Nijeriya sune suka raka mai martaba Sarki zuwa filin jirgin sama, akayi ban kwana kowa na cike da farin ciki.

Ko shakka babu wannan ziyara da mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayero ya kai jamhuriyyar dimokuraɗiyyar ƙasar Aljeriya ta buɗe wani sabon babi na dangantaka mai ƙarfi tsakanin ƙasar da kuma Nijeriya. Wannan tagomashi da Sarkin Kano yake samu a duk inda yaje lallai abin godiya ga Allah ne ga duk mai ƙaunar ci gaban jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Ɗadin daɗawa gashi har mai martaba Sarki yayi hobbasa har shugaban ƙasar na Aljeriya yayi alkawarin baiwa ɗaliban jihar Kano guraben ƙaro ilmin jami’a kyauta da shiryawa malamai da limamai kwasa-kwasai na ƙara sanin makamar aiki, sannan a waje ɗaya kuma shugaban na Aljeriya ya bada umarni cewa ayi duk abinda za ayi don ganin kwance duk wani daurin Gwarmai don sassauta hulɗar kasuwanci ga ‘yan kasuwar Nijeriya masu sha’awar zuwa Aljeriya.

Mai martaba Sarki ya samo nasarar da ba a taɓa samowa ba a bigiren dangantakar  siyasa ko diflomasiyya, don haka babu abin yi da ya wuce mu yiwa Allah godiya da muka samu Sarki wanda addu’ar magabata da kyakkawar mu’amala  da nagartaccen lamiri suke haskaka masa turbar tafiyarsa, ba kuskunda ba jalla-kujalle.

Fatanmu shine Allah Mabuwayi Ya kara wa Sarki lafiya da jimiri da jinkiri, yadda yake fafutukar samawa al’ummar Kano tudun dafawa, shima Allah Ka dafa masa.

Yadda Sarki ya ɗauko saitin gwadabe tun ba a je ko’ina ba a tafiyar yayi nuni da cewa nan da ɗan lokaci zai ginawa Kanawa rijiya gaba dubu wacce ko da an shekara saran  ruwa toh sai tamfatse.

A laaaafiya baƙon Shehu Maghili !!!

Magaji Galadima
Kachallan Kano
Disamba 25, 2022.

 

Continue Reading

Hausa

Kano ba ta dace da APC ba – Bello Sharada

Published

on

APC Flag

Bello Muhammad Sharada

 

 

 

A tarihi Kano gari ne na ilimi. Kano gari ne na addini. Kano gari ne na kasuwanci. Kano gari ne na sarauta. Kano gari ne ‘yanci da walwala da tarbiyya. Kano ana yi mata kirari da Tumbin Giwa, jallabar Hausa ko da me ka zo an fika. Limisliki alfun.

Ka auna tarihin Sarakunan Kano na Hausa da Sarakunan Kano na Fulani. Ka koma yadda Kano take bayan Turawan mulkin mallaka sun zo har suka ci mu da yaki a 1903 da lokacin da aka bamu ‘yancin kai a 1960, da sanda aka kirkiro jihar Kano a 1967, da zamanin soja na Audu Bako da Sani Bello da Ishaya Aboi Shekari kafin a baiwa farar hula mulki a jamhuriya ta biyu a shekarar 1979 da zamanin mulkin Rimi da Abdu Dawakin Tofa da Sabo Bakin Zuwo a tsakanin shekara biyar 1979-1984. Da yanayin da gwamnonin  sojoji suka yi mulki a shekara 15 tun daga watan Augusta 1985 har zuwa watan Mayu 1999, aka yi gwamna Hamza Abdullah da Idris Garba da Ahmad Daku da Ndatsu Ummaru da Kabiru Gaya da Abdullahi Wase da Dominic Oneya da Aminu Isa Kwantagora basu saba da tsarin Kano ba sai a shekara bakwai da take hannun Hadimu.

Abin da ya jawo haka, an kauce tsarin Kaka da kakanni na siyasar Kano da tsarinta da dabi’unta. Jihar Kano ta dada sukurkucewa ne a zamanin mulkin APC na Gandujiyya. Duk girman Kano da daukakarta da yawan jama’a da Allah ya hore mata, mutum biyar ne kadai sai abin da suka shata, suka kitsa ko kana so ko baka so. Sun ce lokacinsu ne. Da sannu zasu tafi. Na farko gwamna Ganduje. Na biyu uwargidansa Farfesa Hafsat. Na uku Murtala Sule Garo. Na hudu Abdullahi Abbas. Na biyar Alasan Ado Doguwa. Mataimakin gwamna Ganduje sunansa ma Mota ba Fasinja saboda ba shi da wani tasiri, an ajiye shi safayar taya. Takarar gwamna da aka ba shi dole ce uwar naki. Shi kuma Usman Alhaji Sakataren gwamnati hoto ne. A gefe guda kuma suka dan dosana shugaban majalisar jiha Rt Hon Chidari. Wanda duk bai gamsu ba ya tambayi Dr Baba Impossible.

Babu wani abu da za a yi sai da izinin wadannan mutanen. Rigimar G7 da kafuwar NNPP ita ce kadai ta rage kaifin Goggo da Dan Sarki da Alasan Doguwa. Burin dan Sarki ya zama Sarki, burin Goggo kwamanda ya zama gwamna, burin Ganduje ya zama Sanata ko mataimakin shugaban kasa. Burin Alasan Ado Doguwa ya maye gurbin Femi Gbajabimilla.

SU biyar din nan  kowa da bukatar da ta hada su. Zaka gansu jumlatan, amma zuciyoyinsu daban-dabam. Dukkansu suna jifan juna. Murtala ya taba keta Alasan, ya taba cakume Abdullahi Abbas, a kwanan nan kuma Alasan Ado sai da ya mari Murtala a gaban Gawuna kuma a cikin gidansa. Alasan zai iya zagin kowa da sunan siyasa. Hatta Ahmed Aruwa sai da Alasan ya hankade shi a gaban mahaifiyarsa. A gaban Abdullahi Adamu shugaban jam’iyya na kasa na APC da gwamna Ganduje ya hayayyako wa Sardaunan Kano, har suka yi cacar baki da Aliko Dan Shuaiba, aka shiga tsakani. Yan wannan guruf din sune suka tsangwami Barau, an kai matsayin da Sanata Barau bai isa ya zo taro ba a Kano sai dai ya yi harkarsa a Abuja. Kwanan nan Sanata Barau ya baiwa Ganduje kyautar miliyan 150.

Abin da ya nace APC ba ta dace da Kano ba, a wadannan shekarun ne gwamna Ganduje ya kalli manyan masu daraja ya keta musu alfarma, sannan ya kirasu da Dattawan Wukari. A wannan lokacin ne gwamna ya dauki aikin da aka zabe shi domin ya aiwatar amma ya danka shi a hannun uwargidansa, har kuma ta nada wanda zai gaje shi.

An kai matsayin da komai ba a yinsa daidai a Kano a mulkin Ganduje. In kuma ka tanka sai a daureka. Ko a saka wasu karnuka su yi tayi maka haushi. GA Kano garin kasuwanci an yanka kasuwa ko ina ba tsari. Kullum a cikin rigimar fili. Kano garin Sarauta, ita kanta masarautar an yi mata filla-filla, Alasan Ado Doguwa ma Sardaunan kasar Rano ne, da rawaninsa ma ya kwankwashi bakin Murtala. Kano garin malanta, Council of Ulama sai da aka yi mata kishiya, hatta halifancin Tijjaniya sai da aka kutsa ga na Sarki ga na gwamna. Siyasa kuma ba a zancenta, Rarara ya taba zambo da tsulan biri aka yi masa tafi. Ya yi habaici da duna aka yi masa dariya. Ya buga misali da hankaka ana shirin kulle shi.

Babu wani lamarin APC da ake yi cikin adalci. Kowa kuka yake yi. Ga shi kansa Mai gidan APC na kasa babu wani abin alheri mai girma da aka yi wa jama’ar Kano a saboda kauna da biyayya da goyon baya da suke yi masa tsawon shekara 18.

APC bata dace Kano ba. A 2023 Sai an canza da kuri’armu cikin yardar Allah.

Bello Muhammad Sharada jigo ne a Siyasar gidan Malam Ibrahim Shekarau 

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending