Connect with us

Hausa

Gajeruwar Tunatarwa Akan Watan Sha’aban

Published

on

Daga Imam Murtadha Gusau

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Ya bayin Allah! Babban Malamin mu, Ash-Sheikh Sulaiman Ar-Ruhaili yana cewa:

“Yaku masoyana ina yi maku kashedi game da Allah, ku kiyayi Allah, hakika Allah yayi maku ni’imah, kasancewar ya sanya ku cikin wadanda suka riski wannan wata na Sha’aban, alhali kuna cikin koshin lafiya da karfi da alkhairi. Don haka, ku godewa Allah mai girma da daukaka a bisa wannan ni’imar da yayi maku; ku kyautatawa kanku ta hanyar yawaita azumi a wannan wata na Sha’aban, la’alla Allah ya sanya ku cikin wadanda zasu samu Aljannah, a dalilin azumtar wannan wata da kuka yi, kuma ya ‘ƴantar da ku daga azabar wuta. Yaku bayin Allah! Ina yi maku gargadi da kashedi, game da Allah, a bisa wannan ganimar da ya baku. Kada kuyi sakaci da ita, kada kuyi kasala a cikinta. Kuyi rige-rige a cikinta, wurin aikata ayukkan alkhairi. Ku sani, abun sayarwar yana da tsada, hakika abun sayarwar Allah shine Aljannah. Kuma tabbas, kudin sayenta da ake nema a wurin ku, dan kadan ne, ya ku bayin Allah.”

Ya ku masoyana, masu girma! Imam Abubakar Al-Bulkhi Allah yayi masa rahama, ya kasance yana cewa:

“Ku sani, watan Rajab wata ne na shuka, watan Sha’aban kuma wata ne na ban ruwa (wato bayi), watan Ramadan kuma wata ne na girbi.”

Sannan ya kara da cewa:

“Watan Rajab kamar iska ne (wato guguwa), shi kuma watan Sha’aban kamar hadari ne, shi kuma watan Ramadan shine ruwan saman.”

Wani babban Malami daga cikin magabata yana cewa:

“Shekara tana nan kamar bishiya ce, watan Rajab shine lokacin fidda furen ta, watan Sha’aban kuma shine lokacin fidda ‘ya’yanta, watan Ramadan kuma shine lokacin tsinkar ‘ya’yan, kuma muminai sune suka cancanci tsinkan ‘ya’yan. Ga mutumin da ya bakanta littafinsa da zunubai, sai ya faranta shi da tuba zuwa ga Allah a cikin wannan watan, wanda kuma ya bata shekarunsa a banza, to sai ya ribaci abunda ya rage na shekarunsa.”

Uwar Muminai, Ummu na Aisha Allah ya kara yarda da ita, ta ke cewa:

“Manzon Allah ya kasance yana yin azumi a cikin wannan watan, har sai munyi tsammanin ba zai ajiye ba. Sannan idan ya ajiye, har sai munyi tsammanin ba zai dauka ba.”

Sannan ta kara da cewa:

“Ban taba ganin Manzon Allah (SAW) ya azumci wani wata gaba ɗayan sa ba, sai Ramadan. Sannan babu wani wata da Annabi yake yawaita azumi a cikinsa kamar Sha’aban.” [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito]

Habib Bin Thabit Allah yayi masa rahamah, ya kasance idan watan Sha’aban ya kama, yana cewa:

“Wannan (watan Sha’aban) shine watan Kurra’u (wato watan makaranta Alkur’ani).”

Amru Bin Kais Al-Mula’i Allah yayi masa rahamah, ya kasance idan watan Sha’aban ya kama, yana kulle shagonsa, ya kebance kansa ga karatun Alkur’ani kawai.

Salmata Bin Kuhail, Allah yayi masa rahamah, yana cewa:

“Ya kasance ana kiran watan Sha’aban da watan Kurra’u.”

Alhassan Bin Shahil, Allah yayi masa rahamah, ya kasance yana yawaita karatun Alkur’ani a cikinsu (wato watan Sha’aban da watan Ramadan) sannan sai yace: “Ya Allah, ka sanya ni a tsakanin watanni guda biyu masu girma.” [Duba littafin, Lata’iful-Ma’arif]

Usamah Bin Zaid yace:

“Ya Manzon Allah, ban ga kana azumtar wani wata kamar yadda kake azumtar Sha’aban ba? Sai Annabi (SAW) yace: Wannan shine watan da mutane suke gafala da shi, tsakanin Rajab da Ramadan, alhali wata ne da ake kai aikin bayi zuwa ga Ubangijin Talikai, shine nike son akai aiki na wurin Allah alhali ina cikin azumi.” [Nasa’i ne ya ruwaito shi, kuma Sheikh Albani ya inganta shi]

An ruwaito daga babban Sahabi, Anas Bin Malik, Allah ya kara yarda da shi yace:

“Sahabban Manzon (SAW), sun kasance idan watan Sha’aban ya kama, sun dukufa kenan akan Alkur’ani, suna karanta shi, sannan su fitar da zakkar dukiyarsu, su karfafi masu rauni, da miskinai, da marasa galihu, a kan azumin watan Ramadan, sannan Musulmai su kira bayinsu, su ce mun yafe maku harajin da ke kanku a cikin watan Ramadan (Abun nufi, wato sun yafe masu. Babu biyan haraji a kansu, har Ramadan ya wuce). Shugabanni kuma su kira ‘yan fursuna, wanda yake da hukuncin haddi sai ayi masa. Wanda kuma laifinsa babu haddi sai a yafe masa, a sake shi ya tafi. Sannan kuma shugabannin al’ummah suna raba kayan arziki ga talakawa” [Duba littafin IKHRAJI-ZAKAT na Ibn Rajab Al-Hanbali]

Ya ku bayin Allah masu girma! Mu dage da addu’a a wannan lokaci mai albarka, musamman a kan matsalolin da suke addabar wannan kasa tamu mai albarka, da kuma yankin mu na arewa. Ku sani, ita addu’a ba ta faduwa kasa banza!

Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi yace:

“Babu wani Musulmi da za ya roƙi Allah da wata Addu’a wadda babu sabon Allah a cikinta ko kuma yanke zumunta, face sai an bashi ɗayan abubuwa uku: ko dai Allah ya gaggauta bashi abinda ya roƙa nan take, ko kuma Allah ya jinkirta masa sai a lahira a biya shi, ko kuma ya kawar masa da wani mummunan abu da zai same shi. Sai Sahabbai suka ce, lallai zamu yawaita yin addu’a kuwa. Sai Manzon Allah (SAW) yace, Allah zai yawaita.” [Imam Ahmad ne ya ruwaito]

A dage da addu’a ya bayin Allah, sannan a guji yin gaggawa wurin amsawa!

Sannan ‘yan uwana Musulmi, duk yadda za’ayi, kada ku bar zikirorin safiya da kuma na marece, domin zasu kusanta ku ga Allah. Sannan zaku samu kariya daga dukkan abin ƙi, na daga shaidanu da mutane. Kuma kariya ne daga sharrin hassada, da kambun baka, kai da ma dukkan wani abu mai cutarwa!

Ya Allah, ka nuna muna Ramadan muna masu Imani da koshin lafiya.

Ya Allah, kasa muna daga cikin bayin ka da zaka ‘ƴanta a cikin wannan wata mai albarka.

Daga karshe, Abu Darda yana cewa:

“Babban abun tsoro na shine, in tsaya a gaban Allah ranar sakamako, ace da ni, Abu Darda, me kayi da ilimin da ka koya?” [Duba littafin Addaʾu wad-dawa’]

Dan uwa na mai daraja, abun tambaya a nan shine: Shin da ni, da kai, da ke, da ku, da su, mun taba tambayar kawunan mu game da yadda muke sarrafa abunda muka koya na ilimi kuwa? Shin mu ma wane tanadi mu kayi wurin amsa wannan tambayar a gaban Allah, gobe kiyama😭?!

Sannan a kashe, wallahi ina shaida maku cewa, duk wanda yake son ya more wa rayuwar duniya da ta lahira, to yabi Allah…!

Wassalamu Alaikum,

Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, jihar Kogi, Najeriya. Za’a same shi a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.

Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .

Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.

“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.

Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun  da basu samu damar biya ba a baya.”

Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A  bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari,  gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.

“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen  ciyar da al’umma.” Dangote.

 

Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.

“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da  neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”

Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada  rade-radi da jita-jita.

Continue Reading

Hausa

A kwanaki 100, VON ta farfaɗo, ci gaba ya bayyana da kuma fatan fin haka nan gaba – Ndace

Published

on

Jibrin Baba Ndace

 

A zafin ranar 29 ga watan Oktoba, 2023 ne aka samu wani canji na alheri da ya lulluɓe harabar Voice of Nigeria (VON) mai cike da sa’ida, sakamakon naɗin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi mini a matsayin Darakta-Janar na gidan rediyon na ƙasa, inda hakan ya zamto wani ɗamba na sauyin zamani a kafar yaɗa labaran ta ƙasa.

Bikin karɓar aiki daga hannun wanda na gada, Osita Okechukwu ya wuce a ce biki ne na sallamar ma’aikaci. Da ga karɓar shugabancin, guguwar sauyi ta fara kaɗa wa bayan na halarci taron AFRICAST 2023 a Legas. Sai na yi amfani da wannan damar na ziyarci cibiyoyin watsa shirye-shiryen tashar ta mu da ke Ikoyi da Ikorodu, inda hakan ya bani kwarin gwiwar cewa akwai dama mai ƙarfi da zan samu na kawo gagarumin ci gaba a gidan rediyon.

Dawowa ta shelkwatar VON da ke Abuja kuma, sai na fuskanci akwai aiki ja a gaba na. A yanayin lalacewar gine-gine da kayan aiki da na gani a cibiyar mu ta Ikko, sai na ji cewa ya zama wajibi na tashi tsaye na kawo gyara cikin gaggawa.

Duk da cewa kusan hakan yanayin ya ke a cibiyar watsa shirye-shiryen mu ta Lugbe a Abuja, akwai abinda ya bani ƙarfin gwiwa, shi ne wutar sola da na tarar. Sai na fahimci cewa wato akwai ɗumbin nasarori a VON, amma ana buƙatar jajirtaccen shugaba da zai farfaɗo da ita.

Bayan gine-gine da kayan aiki, ma’aikata su ne ƙashin bayan VON, sai dai kuma kash! akwai ƙarancin karsashi a tare da su ma’aikatan gidan rediyon a duka tashoshin namu na Abuja da Legas sakamakon rashin biyan su alawus-alawus na su da kuma kuɗaɗensu na ƙarin matsayi. Wannan ƙalubale ne da ya ke buƙatar kawo ɗauki cikin gaggawa domin samun gaba mai kyau.

Tun asali, kamata ya yi a samu wani kundi na tsare-tsare. Zaburar da ma’aikata na buƙatar ƙirƙiro da dabarun inganta walwalar su da kuma ƙara musu matsayi akai-akai lokacin da ya dace da kuma basu lambobin yabo bisa ƙwazon su a aiki. Kada kuma a manta da cewa haɗin kai tsakanin shugabanni da ma’aikata shi ne babban sinadarin kawo sauyi Na ci gaba a ma’aikata.

Halastar mu zuwa babban taron UNESCO na duniya, karo na 42 da aka yi a birnin Paris da kuma taron ranar rediyo na duniya a Dubai, ba wai mun je yawon buɗe-ido ba ne, sai dai wata babbar dama ce ta samun damammaki daga ƙasashen duniya. Waɗannan tarukan wata babbar dama ce ta nuna wa duniya irin ƙwazon VON na watsa shirye-shirye daidai da yadda ya ke a duniya da kuma ƙulla alaƙa, duk a ƙoƙarin ta na zama a aji ɗaya da manyan kafafen yaɗa labarai na duniya.

Ganawar farko ta shugabannin VON da ta gudana a ranar 19 ga watan Disamba, 2023, ba wai an yi zaman hira ne kawai ba, sai dai zaman ya kasance wata ɗamba ce aka kafa wajen samar da haɗin gwiwa domin fitar da dabarun aiki da za su ƙara taimaka wa gidan rediyon ya cimma muradun sa.

Aiyuka na bi-da-bi me ya haifar da nasarar da mu ka samu ta ganawa da kwamitin majalisar dattawa kan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma, kare kasafin kudin da mu ka yi wa kwamitocin majalisar dattawa da na majalisar wakilai da kuma ziyarar aiki da mu ka kaiwa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris. Waɗannan aiyukan sun kasance tubalin mu na gina alaƙa, wacce za ta samar mana da taimako da kuma fahimtar juna.

Hakazalika, alaƙar da mu ka ƙulla da ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu, da suka hada da Thunderbird, Image Marchants Promotions Limited, SEMEDAN, GOTNI, NIPR, Ciyaman na NUJ a Minna da kuma wakilci da ga Dangote Group da Jaiz Bank, ba wai ziyara ba ce kaɗai, sai dai sun zamto tattaunawa da za su buɗe kofa, su gina mana gadoji da kuma alaƙa da za su taimaka wa VON ta kai gaci.

Sannan, ziyarorin da muka kai wa Media Trust, National Orientation Agency, News Agency of Nigeria, Nigerian Diaspora Commission da NTA da kuma manyan shugabannin sojoji ya nuna ƙwazon mu na kawo gyara mai inganci a VON tare da bata suffar da ta ke buƙata.

A kwanaki 100 na farko a matsayin Darakta-Janar, na bada umarnin cewa duk wani ɗan hidimar ƙasa (NYSC) da masu koyon aiki a VON, dole a basu horo na musamman, da nufin su ji a ransu kamar su ma ma’aikata ne a tsawon lokacin da za su yi a gidan rediyon. Daɗin daɗawa kuma mun ƙulla alaƙa da Guards Polo Club da ƙungiyar shugabannin ma’aikatu ta Afirka domin jawo hankalin al’umma ga irin aikace-aikacen VON.

Bayan duk wadannan, irin bayanan sam-barka da ke fitowa daga bakunan ma’aikatan VON masu albarka, ya ƙara mana ƙaimi da ƙwarin gwiwa. Maida hankali da mu ka yi wajen gyara lalatattun kayan aikin mu da neman tallafin gwamnati wajen farfaɗo da tashar mu ta Lugbe ya nuna yadda shugabancin mu ke da zuciyar kawo gyara da kuma ɗaukaka VON.

A yayin da muka cika kwanaki 100 da karɓar ragamar shugabancin VON, magana a ke yi ta fara ganin guguwar sauyi ta fara kaɗa wa. Kalubalen da mu ka taras ya zamto wani ginshiƙi na gyara mai inganci. Sannan, dabarun da mu ke ɓullo da su sau ɗau saiti na fito dartabar VON ba wai a matsayin shahararren gidan rediyo ba, har ma ta zamto a bar koyi a fannin watsa shirye-shirye a faɗin duniya. Yayin da ake ci gaba da samar da hanyoyin gyara, lokaci kaɗai mu ke jira da zai fito da VON da har karan ta zai kai tsaiko a idon duniya.

Mallam Jibrin Ndace shi ne Darakta-Janar na VOICE of Nigeria, VON. Tashar watsa labarai na duk duniya ta Nijeriya.

Continue Reading

Hausa

Gwamna Abba Kabir Yusuf: Kano na Bukatar Sabuwar Alkibla!

Published

on

Farfesa Faruk Sarkinfada

 

Bayan nasarar da Allah Madaukakin Sarki ya baiwa Gwamnan jihar Kano Eng Abba Kabir Yusuf a kotun koli ta Nigeria bisa tabbatar da zaben sa, jihar Kano na bukatar sabuwar alkiblar jagoranci da ta gaza samu tun dawowar mulkin demokradiyya a shekarar 1999.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na bukatar assasawa da gudanar da jagorancin da zai tabbatar da zaman lafiya da ci gaba da bunkasar arzikin jihar kano ta hanyar dinke baraka ta bangarori da dama, musamman na siyasa, malamai da masarautu, don samun nasarar gudanar da mulkin adalci ga jama’ar jihar Kano. Mai girma Gwamna ya na da kyakyawan abin koyi daga rayuwar fiyayyen halitta, Annabin mu Muhammadu tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi, dangane da kalubalen da ya fuskanta a karon farko, da kuma gada bisani yayin da budi da nasarar Ubangiji Allah su ka saukar masa.

A karon farko, yayin halin tsanani da jarrrabawa na tsawon shekaru goma sha uku a garin Makka, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya rayu cikin kyawawan dabi’u, kamar dogaro ga Allah, juriya, rashin tsoro, hakuri, da su ka bayyana yayin halin gwagwarmaya wadanda ba za a iya fahimtarsu ba a cikin halin yalwa da iko. Ya kuma ci gaba da isar da sako ba tare da gajiyawa ba duk da rashin yawan mabiya da kuma tsangwama da ya yi ta fuskanta. Wannan juriya da tsaiwa tsayin daka akan kira ga Allah ya ja hankulan da yawa daga cikin wadanda ba su bada gaskiya ba suka musulunta. A kashi na biyu na rayuwarsa, wato lokacin da nasara ta samu, iko da mulki suka samu Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya bayyana kyawawan halaye kamar su hangen nesa, yafiya, kauna, saukin kai, da jajircewa, wadanda su ka kara jawo hankulan mutane da dama ya zuwa musulunci. Ya yafe wa wadanda suka nuna masa tsana da kiyayya, ya bada cikakken tsaro da kariya ga wadanda suka fitar da shi daga mahaifarsa (Makka), ya ba da dukiya mai yawa ga matalautan su. Wadannan kyawawan dabi’u ya sa ko da wadanda ke adawa su ka karbi kiran Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma duk tsirarun makiyansa suke zama masu kaunarsa daga bisani.

Hakika mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf na da kyakyawan darussa daga rayuwar Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata gare shi a halin tsanani da ya shiga tun zaben 2019, sanda bai sami nasarar zama gwamnan Kano ba, da kuma halin nasarar sa a yanzu da ya yi nasara a zaben 2023 kuma kotun koli ta Nigeria ta tabbatar masa da wannan Nasara. Gwamna Abba Kabir Yusuf na bukatar dinke baraka a wannan lokaci, ta hanyar yafiya, musamman ga wadanda su ka tsangwame shi a baya da kuma kyakyawan hangen nesa, nuna kauna, saukkin kai, da jajircewa, da kare hakkin duk wani mai hakki ba tare da nuna bambanci ta kowannen bangare ba.

Jinina ga mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf don kafa majalisar dattawan Kano (KEC), wadda za ta zama mai ba da shawara ga gwamnati, kuma ta hada da muhimman jagorori ‘yan asalin jihar Kano, da kuma tshofaffin gwamnonin ta, Dr Rabiu Musa Kwankwaso, Mallam Ibrahim Shekarau da Kuma Dr Abdullahi Umar Ganduje. Har way au mu na kira da babban murya musamman ga wadannan shuwagabanni uku da su ka mulki jama’ar Kano tun daga 1999 zuwa yanzu, su kau da banbance-banbancen da ke tsakanin su wajen tallafa wa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf don samar wa jihar Kano sabuwar alkiblar shugabanci na gari. Hakika a tsawon shekaru kusan 24, kowanne daga cikikin wadannan shuwagabanni ya ba da gudunmawa, gwargwadon ikon su, wajen samar da ayyukan ci gaba ta bangarori da dama a jihar Kano. A yanzu ne mutanen Kano su ka fi bukatara gudunmawarku wajen wanzar da abubuwan alkhairai da ku ka dasa, da kuma cike gurabun da ku ka bari, don bunkasar jihar Kano a Nigeria da duniya gaba daya. Hakika za su zamanto ababen alfahari a gare mu in har wannan tsari ya tabbata.

Shi fa kyakyawan shugabanci mai dorewa, ya na samuwa ne lokacin da aka samu jagororin da su ka cancanta daga cikin al’uma, kuma ma su zartar da kudurorin da su ka dace a lokutan da su ka dace, domin tunkara da warware matsalolin da ke addabar al’umar su a wannan lokaci. Lallai Kanawa na matukar kishirwar ingantaccen shugabanci tare da hadin guiwar dukkanin masu ruwa da tsaki daga shuwagabannin siyasa, malamai, sarakuna, ‘yan kasuwa, ma’aikata, ma su manya da kananan sana’o’i da matasa da dukkanin jama’a. Don haka dole ne a rage, ko a kawar da banbance-banbancen siyasa da kiyayya a tsakanin shuwagabanni da mabiya a wannan jiha tamu, domin mu tunkari manyan matsalolin mu na cin hanci da rashawa, magudin zabe, matsanancin talauci, tabarbarewar ilimi, lafiya da tattalin arziki da kuma siyasar rashin kishin talaka ta hanyar yawan ketarawar daga jam’iyya zuwa wata jam’iyyar don maslahar kawunan su.

Kano na bukatar sabuwar alkibla don wanzar da matsayin ta na cibiyar kasuwanci da al’adu da siyasar Arewacin Nigeria. Allah Madaukakin Sarki ya shiryar da shuwagabannin mu, Ya ba mu lafiya da zaman lafiya da yalwar arziki mai amfani.

Ameen.

Farfesa Faruk Sarkinfada
fsarkinfada@yahoo.co.uk

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending