Connect with us

Hausa

Rabiu Chanhu: Dan wasan da ya hada kwallon kafa da karatu

Published

on

Jamilu Uba Adamu 

Da yawan masoya da mutanen dake bibiyar wasan Kwallon Kafa, a Arewacin Najeriya, musamman Jihar Kano ba su cika tsammanin akwai  alaka tsakanin ilimi da wasan Kwallon Kafa ba.

Kasancewar a lokuta da yawa matasan dake buga wasan Kwallon Kafa basu cika samun nasara a makaranta ba, ko samun damar yin karatu mai zurfi ba.

Amma sai dai kamar yadda bincike ya nuna, ‘yan Kwallo da yawa a fadin duniya har ma da nan gida Najeriya sun samu daukaka mai yawa a bangarorin ilimi.

A misalin irin wadannan ‘yan kwallo akwai; Socrates na Brazil, wanda yazama Dakta. Anan gida Nijeriya akwai irin su Sir, Segun Odegbami.

Anan gida Jihar Kano kuwa, Allah ya yi mana baiwar samun wannan bawan Allah da zan kawo sharhi da  takaitaccen tarihinsa, musamman akan wasan kwallon kafa.

Don saboda ya zama madubi abun dubawa ga na baya, musamman wajen hada wasannin motsa jiki da neman ilimin addini da na boko.

Rabiu Chanhu ya fara buga kwallo ne a karamin kulab mai suna Silver Stone dake unguwar Kofar Mazugal. Kuma ya yi wasanni ne na makaranta a lokacin yana karatu a makarantar sakandiren horas da malamai ta garin Bichi, inda daga nan ne Kungiyar Kwallon Kafa ta Super Star dake unguwar Makwalla ta cikin birni ke dauko shi a matsayin sojan haya dan ya buga musu wasa.

A irin wannan wasannin ne ya taimakawa Kungiyar Kwallon kafar ta Super Star samun nasara lashe gasar kofin Dan’wawu wadda ita ce mai daraja ta daya a jihar Kano a wannan zamanin.

Wanda ganin irin bajintar da kwarewar da ya nuna a wannan wasan ne yasa Kungiyar Kwallon Kafa ta Raccah Rovers ta dauke shi dan ya buga Mata wasa a shekarar 1981, kuma ta yi masa rijista.

Farfesa Rabiu Chanhu

A wancen zamanin shi da Abubakar Zagallo (yanzu shine na’ibin limamin masallancin Juma’a a wata Unguwa a New York, America) su ne suke buga lamba biyar da shida a bayan kungiyar kwallon kafa ta Raccah Rovers.

Tsohon dan wasan Kwallon kafar, ya canja sheka daga Raccah Rovers zuwa kungiyar kwallon kafa ta Bank of the North, bisa kin yarda da ya yi da cigaba da bugawa Raccah Rovers wasa bayan kungiyar ta chanja suna zuwa Nigerian Breweries.

Wanda kamar yadda ya bayyana min cewar hakan yana da nasaba da addinin sa na muslunci. Kuma tare da marigayi Usman Danlami Akawu Kofar Wanbai, Wanda shi ma shaharren dan wasan kwallon kafa ne (Allah ya gafarta masa. Ameen) suka koma kungiyar Bank of the North.

Ya ajiye takalmansa na wasan kwallon kafa ne a shekarar 1989. Sai dai kuma ya yin da yake karatunsa na master’s a jami’ar Bayero, an zabe shi a jerin Wanda zasu wakilci kasa Najeriya a gasar Jami’o’i ta Duniya a wasan Kwallon Kafa a shekarar 1995.

A zamanin da Professor yake taka wasa, saboda kwarewarsa a wasan ya samu sunayen inkiya daban-daban wanda ‘yan kallo suka lakaba masa. Sukan kira shi da Na Makwalla, Chanhu, Maigida a sama.

Yanzu dai haka, Malam Muhammad Rabiu “Chanho” Professor ne a Wanda keda kwarewa a ‘adopted physical education’, bangaren Kinetics and Health Education dake Jami’ar Bayero, Kano.

Jamilu Uba Adamu

Mai bibiyar Tarihin wasanni kwallon kafa ne. Za a iya samunsa a +234 803 207 8489

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, Baƙon Shehu Maghili

Published

on

Magaji Galadima

 

 

A ranar Litinin 12 ga watan Disamba 2022 gwamnatin ƙasar Aljeriya ta aiko da wani jirgi na musamman domin ya ɗauki mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zuwa ƙasar ta Aljeriya domin halartar taron duniya na musamman don tunawa da rayuwa da kuma aiyukan shahararren malamin addinin Musulunci sharifi kuma masanin falsafa  wato Shehun malami Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na goma sha biyar. 

Jigin ya tashi daga Kano da karfe 9:45 na safe. A cikin waɗanda suka samu alfarmar raka Sarki wannan tafiya akwai Sarkin Dawakin Tsakar-gidan Kano Alhaji Ahmad Ado Bayero hakimin Kumbotso da Ambasada Ahmad Umar Ɗanmalikin Kano da Dakta Ibrahim Ɗahiru Bauchi wanda ya wakilci Sheikh Ɗahiru Bauchi da Malam Isa Sanusi Bayero da Dakta Lawi Atiku Sanka da kuma ni Magaji Galadima Kachallan Kano, sannan sai wasu malamai da sharifai na Kano da kuma fadawa hadiman Sarki.

Jirgin ya ɗan yada zango a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar inda ya ɗauki Sultan na Agadas da Sarkin Sharifan ƙasar Nijar da sauran malamai da muƙaddamai da malaman jami’a. Sarkin Kano da ‘yan tawagarsa sun sauka a Aljiyas babban birnin Aljeriya da misalin karfe 5:00 na yamma inda manyan ministoci da jami’an gwamnati dana diflomasiyya da kuma manyan malamai suka taryi mai martaba Sarki da tawagarsa. Daga nan akayi jerin-gwano aka raka Sarki masaukinsa.

A rana ta biyu wato Talata Sarki da ‘yan tawagarsa suka fita zuwa wajen taron ƙasa da ƙasa da aka shirya domin tunawa da shahararren malamin addinin musulunci masanin falsafa kuma sharifi wato Shehu Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na sha biyar kuma har ya zo Kano zamanin Sarki Muhammadu Rumfa.

Al-Maghili ya zauna a Kano tsawon lokaci kuma ya bijiro da sababbin tsare-tsare ma su muhimmanci a fadar Kano, kana kuma ya yi rubuce-rubuce akan ibada da hukunci, sannan ya rubuta wani kundi da ya zama daftari na jagorar duk wani sarki na Kano da ma nahiyar yammacin Sudan.

Taron an shirya shi ne a babban ɗakin taro na ƙasar dake birnin Aljiyes.  A ranar buɗe taron Sarkin Kano da tawagarsa sun isa wajen da misalin karfe 9;00 na safe amma sai aka kaishi wani ɗaki ya zauna a kauwame har sai da ɗakin taron yayi cikar kwari sannan aka shigar dashi.

Toh dama an ɗauki makwanni ana ta yaɗawa a kafafen labarai cewa ƙasar ta Aljeriya zata karɓi bakuncin wani ƙasaitaccen Sarki mai alfarma da daraja daga garin Kano a Nijeriya, don haka mutanen ƙasar duk sun zaku suga wannan ƙasaitaccen Sarki. Saboda da haka yana shiga ɗakin taron sai duk aka tashi tsaye waje ya kaure da sowa da tafi, mata kuma na rabka guɗa, su kuma ‘yan badujala suka goce da wani irin take na musamman da ake kaɗawa mashahuran mutane in sun shigo wajen taro.

An ɗauki tsawon lokaci kafin a samu natsuwa lamurra su koma daidai sannan mai martaba Sarkin Kano figinai suka yi sayi ya zauna aka gyara aka kimtsa sannan aka fara gudanar da taro.

Daganan ne kuma sai aka fara jawabai, babban ministan harkokin addini na ƙasar shine ya wakilci shugaban ƙasa kuma yayi jawabin maraba ga mahalarta taron kana yayi godiya ta musamman ga Sarki Aminu Bayero a madadin shugaban ƙasa da al’ummar ƙasar baki ɗaya. Shima Sarkin na Kano  yayi jawabi inda ya nuna farin ciki da godiya ga gwamnati da jama’ar ƙasar baki ɗaya saboda kyakkawar taryar da aka yi masa, ya kuma isar da gaisuwar jama’ar masarautar Kano da Nijeriya baki ɗaya a garesu.

Sarkin ya yaba da hangen nesan waɗanda suka assasa wannan taro na tunawa da Shehu Maghili wanda yace yafi cancanta a kira shi da Bakano maimakon dan Aljeriya saboda da dalilai da dama. Ya baiyanawa mahalarta taron cewa a yanzu haka a cikin birnin Kano akwai unguwar Sharifai waɗanda asali jama’ar da suka zo Kano tare da Shehu Maghili sune ke zaune a wannan unguwa tun lokacin har zuwa yanzu, kuma shugabansu Sidi Fari shine Sarkin Sharifan Kano kuma yana da gurbin zama a majalisar Sarkin Kano.

A ƙarshen jawabin Sarki yayi godiya ga Allah wanda Ya ƙudura cewa a zamaninsa ne akayi wannan babbar hobbasa ta sake dawo da wannan tsohuwar alaƙa tsakanin Kano da Nijeriya da kuma ƙasar Aljeriya kamar yadda su Shehu Maghili suka shimfiɗa.

Daga nan kuma sai aka buɗe fage inda malamai da masana suka yita ƙwami akan tarihin rayuwa da rubuce-rubucen Shehu Maghili.

Bayan an tashi daga taron wannan rana ta farko, sai mutane suka yanyame Sarkin Kano, malamai da jami’an gwamnati da baƙi daga sauran ƙasashe kowa burinsa shine ya samu ya ɗauki hoto da Sarkin Kano.

Bayan an fito waje ma haka har zuwa inda ya shiga mota. Mu ma ‘yan kwarakar Sarki da kyar muka yakice ‘yan jarida masu son jin kwakwaf domin yawansu babu lokaci da zamu warware musu zare da abawa. Koda muka isa masauki sai muka tarar ashe tuni wasu jama’ar sun yi kwamba suna jiran isowar Sarki domin su samu su gaisa kuma su ɗauki hoto da shi.

 

Bayan ya shiga ɗaki kuma sai manyan malaman ƙasar su kuma suka yi layin shiga suna yiwa sarki addu’a har saida rana tayi gora sannan jami’an tsaro suka tare mutane suka hana su shiga don a kyale Sarki ya huta.

A rana ta biyu mai martaba Sarki da tawagarsa ya sake komawa wajen taron inda malamai suka ci gaba da gabatar da takardu.

Bayan anyi hutun zango na farko sai mai martaba Sarki ya fita domin kai ziyara ofishin jakadancin Nijeriya dake kasar ta Aljeriya.

Jakadiyar Nijeriya Hajiya Aisha Muhammad Garba ta taryi Sarki da tawagarsa kuma anyi jawabai masu muhimmanci.

Da maraice kuma har ila yau sai Jakadiyar ta shiryawa mai martaba sarki wata liyafar alfarma a gidanta inda aka gaiyaci ‘yan Nijeriya mazauna ƙasar Aljeriya da kuma wasu malamai daga Nijeriya.

A rana ta uku kuwa mai martaba Sarki ya halarci bikin rufe taron kuma abin ya ƙayatar ƙwarai musamman yadda Sarkin Kanon ya zama tauraro a wajen taron domin dai hankalin kowa na kansa tun daga farko har i zuwa lokacin da aka ja labulen rufe taron.

Da yammaci kuma sai shugaban ƙasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya gaiyaci Sarki Aminu zuwa fadarsa inda suka zauna suka yi zantuka na girma. Shugaban ƙasar yace yayi murna matuƙa da karɓar baƙuncin Sarkin, ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar tasu tana sane da tarihin masarautar Kano da rawar da Shehu Maghili ya taka wajen bunƙasa al’adu da addinin Musulunci a birnin Kano.

Shugaba Tebboune yace Sarkin Kano a wannan ziyara shi baƙon Shehu Maghili ne, duk da yayi wafati fiye da shekaru 600, wannan ziyara ta Sarki lallai Shehu Maghili shine sila.

Shi kuma a lokacin da yake maishe da jawabi Sarki Aminu yayi godiya ga Allah da Ya bashi ikon amsa gaiyatar shugaban ƙasar da kawo wannan ziyara, ya yabawa gwamnatin ƙasar Aljeriya saboda ɗawainiyar ɗaukar nauyin wannan taro mai muhimmanci.

Daga nan kuma sai yayi kira ga shugaban na Aljeriya da su haɗu su farfaɗo da hulɗar cinikayya da kasuwanci tsakanin Kano da Aljeriya wanda yace zai taimaka wajen ƙara yauƙaƙa danƙon zumunci tsakanin nahiyoyin biyu. Baya ga wannan kuma da yake ance lokacin iska ake cin ɗan jinjimi sarkin ya bukaci gwamnatin ƙasar ta Aljeriya da ta bawa ɗaliban jihar Kano tallafi na guraben ƙara ilmi a fannoni dabam-daban a jami’oin ƙasar inda shugaban ƙasar nan take yayi wuf yace ya amince da wannan shawara kuma yana jira in Sarki ya koma gida,  ya tsaro jadawalin yadda duk yake so ayi , su kuma in Allah Yaso zasu aiwatar. a nan dai akayi muwafuƙa duk shawarar tasu tazo daidai.

Daga nan suka yi bankwana cikin farin ciki da girmama juna.

A rana ta hudu mai martaba Sarkin Kano tare da wasu daga cikin ‘yan tawagarsa sun ziyarci garin Ain-Madhi wato ainihin garin da aka haifi Maulana Shehi Ahmadu Tijjani (RA) wanda ya kafa ɗarikar Tijjaniyya.

Sarkin ya ziyarci muhimman wuraren tarihi a garin sannan ya gana da manyan malamai da sharifai zuriyar Shehin inda suka yiwa Sarkin da Kano da Nijeriya  addu’oi na musamman.

A rana ta biyar Sarki ya kammala ziyarar kamar yadda aka tsara, don haka sai ya karyo linzami zuwa gida. Manyan jami’an gwamnati da malamai da kusoshin diflomasiyya da kuma jakadiyar Nijeriya sune suka raka mai martaba Sarki zuwa filin jirgin sama, akayi ban kwana kowa na cike da farin ciki.

Ko shakka babu wannan ziyara da mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayero ya kai jamhuriyyar dimokuraɗiyyar ƙasar Aljeriya ta buɗe wani sabon babi na dangantaka mai ƙarfi tsakanin ƙasar da kuma Nijeriya. Wannan tagomashi da Sarkin Kano yake samu a duk inda yaje lallai abin godiya ga Allah ne ga duk mai ƙaunar ci gaban jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Ɗadin daɗawa gashi har mai martaba Sarki yayi hobbasa har shugaban ƙasar na Aljeriya yayi alkawarin baiwa ɗaliban jihar Kano guraben ƙaro ilmin jami’a kyauta da shiryawa malamai da limamai kwasa-kwasai na ƙara sanin makamar aiki, sannan a waje ɗaya kuma shugaban na Aljeriya ya bada umarni cewa ayi duk abinda za ayi don ganin kwance duk wani daurin Gwarmai don sassauta hulɗar kasuwanci ga ‘yan kasuwar Nijeriya masu sha’awar zuwa Aljeriya.

Mai martaba Sarki ya samo nasarar da ba a taɓa samowa ba a bigiren dangantakar  siyasa ko diflomasiyya, don haka babu abin yi da ya wuce mu yiwa Allah godiya da muka samu Sarki wanda addu’ar magabata da kyakkawar mu’amala  da nagartaccen lamiri suke haskaka masa turbar tafiyarsa, ba kuskunda ba jalla-kujalle.

Fatanmu shine Allah Mabuwayi Ya kara wa Sarki lafiya da jimiri da jinkiri, yadda yake fafutukar samawa al’ummar Kano tudun dafawa, shima Allah Ka dafa masa.

Yadda Sarki ya ɗauko saitin gwadabe tun ba a je ko’ina ba a tafiyar yayi nuni da cewa nan da ɗan lokaci zai ginawa Kanawa rijiya gaba dubu wacce ko da an shekara saran  ruwa toh sai tamfatse.

A laaaafiya baƙon Shehu Maghili !!!

Magaji Galadima
Kachallan Kano
Disamba 25, 2022.

 

Continue Reading

Hausa

Kano ba ta dace da APC ba – Bello Sharada

Published

on

APC Flag

Bello Muhammad Sharada

 

 

 

A tarihi Kano gari ne na ilimi. Kano gari ne na addini. Kano gari ne na kasuwanci. Kano gari ne na sarauta. Kano gari ne ‘yanci da walwala da tarbiyya. Kano ana yi mata kirari da Tumbin Giwa, jallabar Hausa ko da me ka zo an fika. Limisliki alfun.

Ka auna tarihin Sarakunan Kano na Hausa da Sarakunan Kano na Fulani. Ka koma yadda Kano take bayan Turawan mulkin mallaka sun zo har suka ci mu da yaki a 1903 da lokacin da aka bamu ‘yancin kai a 1960, da sanda aka kirkiro jihar Kano a 1967, da zamanin soja na Audu Bako da Sani Bello da Ishaya Aboi Shekari kafin a baiwa farar hula mulki a jamhuriya ta biyu a shekarar 1979 da zamanin mulkin Rimi da Abdu Dawakin Tofa da Sabo Bakin Zuwo a tsakanin shekara biyar 1979-1984. Da yanayin da gwamnonin  sojoji suka yi mulki a shekara 15 tun daga watan Augusta 1985 har zuwa watan Mayu 1999, aka yi gwamna Hamza Abdullah da Idris Garba da Ahmad Daku da Ndatsu Ummaru da Kabiru Gaya da Abdullahi Wase da Dominic Oneya da Aminu Isa Kwantagora basu saba da tsarin Kano ba sai a shekara bakwai da take hannun Hadimu.

Abin da ya jawo haka, an kauce tsarin Kaka da kakanni na siyasar Kano da tsarinta da dabi’unta. Jihar Kano ta dada sukurkucewa ne a zamanin mulkin APC na Gandujiyya. Duk girman Kano da daukakarta da yawan jama’a da Allah ya hore mata, mutum biyar ne kadai sai abin da suka shata, suka kitsa ko kana so ko baka so. Sun ce lokacinsu ne. Da sannu zasu tafi. Na farko gwamna Ganduje. Na biyu uwargidansa Farfesa Hafsat. Na uku Murtala Sule Garo. Na hudu Abdullahi Abbas. Na biyar Alasan Ado Doguwa. Mataimakin gwamna Ganduje sunansa ma Mota ba Fasinja saboda ba shi da wani tasiri, an ajiye shi safayar taya. Takarar gwamna da aka ba shi dole ce uwar naki. Shi kuma Usman Alhaji Sakataren gwamnati hoto ne. A gefe guda kuma suka dan dosana shugaban majalisar jiha Rt Hon Chidari. Wanda duk bai gamsu ba ya tambayi Dr Baba Impossible.

Babu wani abu da za a yi sai da izinin wadannan mutanen. Rigimar G7 da kafuwar NNPP ita ce kadai ta rage kaifin Goggo da Dan Sarki da Alasan Doguwa. Burin dan Sarki ya zama Sarki, burin Goggo kwamanda ya zama gwamna, burin Ganduje ya zama Sanata ko mataimakin shugaban kasa. Burin Alasan Ado Doguwa ya maye gurbin Femi Gbajabimilla.

SU biyar din nan  kowa da bukatar da ta hada su. Zaka gansu jumlatan, amma zuciyoyinsu daban-dabam. Dukkansu suna jifan juna. Murtala ya taba keta Alasan, ya taba cakume Abdullahi Abbas, a kwanan nan kuma Alasan Ado sai da ya mari Murtala a gaban Gawuna kuma a cikin gidansa. Alasan zai iya zagin kowa da sunan siyasa. Hatta Ahmed Aruwa sai da Alasan ya hankade shi a gaban mahaifiyarsa. A gaban Abdullahi Adamu shugaban jam’iyya na kasa na APC da gwamna Ganduje ya hayayyako wa Sardaunan Kano, har suka yi cacar baki da Aliko Dan Shuaiba, aka shiga tsakani. Yan wannan guruf din sune suka tsangwami Barau, an kai matsayin da Sanata Barau bai isa ya zo taro ba a Kano sai dai ya yi harkarsa a Abuja. Kwanan nan Sanata Barau ya baiwa Ganduje kyautar miliyan 150.

Abin da ya nace APC ba ta dace da Kano ba, a wadannan shekarun ne gwamna Ganduje ya kalli manyan masu daraja ya keta musu alfarma, sannan ya kirasu da Dattawan Wukari. A wannan lokacin ne gwamna ya dauki aikin da aka zabe shi domin ya aiwatar amma ya danka shi a hannun uwargidansa, har kuma ta nada wanda zai gaje shi.

An kai matsayin da komai ba a yinsa daidai a Kano a mulkin Ganduje. In kuma ka tanka sai a daureka. Ko a saka wasu karnuka su yi tayi maka haushi. GA Kano garin kasuwanci an yanka kasuwa ko ina ba tsari. Kullum a cikin rigimar fili. Kano garin Sarauta, ita kanta masarautar an yi mata filla-filla, Alasan Ado Doguwa ma Sardaunan kasar Rano ne, da rawaninsa ma ya kwankwashi bakin Murtala. Kano garin malanta, Council of Ulama sai da aka yi mata kishiya, hatta halifancin Tijjaniya sai da aka kutsa ga na Sarki ga na gwamna. Siyasa kuma ba a zancenta, Rarara ya taba zambo da tsulan biri aka yi masa tafi. Ya yi habaici da duna aka yi masa dariya. Ya buga misali da hankaka ana shirin kulle shi.

Babu wani lamarin APC da ake yi cikin adalci. Kowa kuka yake yi. Ga shi kansa Mai gidan APC na kasa babu wani abin alheri mai girma da aka yi wa jama’ar Kano a saboda kauna da biyayya da goyon baya da suke yi masa tsawon shekara 18.

APC bata dace Kano ba. A 2023 Sai an canza da kuri’armu cikin yardar Allah.

Bello Muhammad Sharada jigo ne a Siyasar gidan Malam Ibrahim Shekarau 

Continue Reading

Hausa

Yusuf Qaradawi: Tsakanin Malaman Al’umma da Malaman Hakuma

Published

on

Farfesa Umar Labdo Muhammad

 

 

Mutuwar Dr Yusuf Qaradawi, Allah ya yi masa rahama, ta fito da abubuwa wadanda a da suke boye. Misali, ta bayyana malaman Al’umma masu yanci, wadanda ba sa tsoron zargin mai zargi dangane da al’amarin Ubangiji, da kuma malaman Hakuma masu amshin shata ga azzaluman shugabanni. Ta nuna yadda daidaikun Al’umma suke bambancewa tsakanin wannan nau’i biyu na malamai.

Da aka ba da sanarwar rasuwarsa, hukumomi a Misira, wacce ita ce kasar haihuwarsa, sun haramta yi masa salatul ga’ib a duk fadin kasar. Don haka malaman fada suka ja bakinsu suka yi shuru, babu wanda ya ce Allah ya jikan sa a bainar jama’a. Shaihun Azhar, wanda yan kwanaki kadan da suka wuce ya yi ta’aziyyar Sarauniyar Ingila Yazzabul a bainar jama’a, ya kasa furta harafi daya don ta’aziyyar Qaradawi tare da cewa Qaradawi dan Azhar ne wanda ya zama mamba na babba majalisar malamanta.

A kasar Saudiyya ba su sa doka ba, amma ba wani fitaccen malami da ya fito a bainar jama’a ya ce Allah ya jikan Qaradawi, saboda su dama sun san abinda sarakansu suke so da abinda ba sa so. Kuma su ko tari za ka yi idan ka san sarki atishawa yake so, to sai ka murde tarin ka mayar da shi atishawa!

Haka nan, a Hadaddiyar Daular Larabawa (Dubai) an samu wasu da suka fadi miyagun maganganu dangane da marigayin.

A daya bangaren kuma, talakawan Musulmi da malamansu masu yanci sun nuna matukar alhini da rasuwar kuma sun yi jana’iza daga nesa (salatul ga’ib). Daga cikin wuraren da aka gabatar da irin wannan Sallah akwai kasashen India, Pakistan, Indonesia, Moritania, Malaysia da Palasdinu inda aka gabatar da sallar a Masallacin Aqsa.

Haka nan, matasan Musulmi a ko wane bangare na duniya sun cika dandalin sada zumunci da sakonnin ta’aziyya wadanda suka kunshe da kalmomin kauna da girmamawa da fatan gafara da rahamar Allah.

Allah ya jikan Qaradawi, ya gafarta masa, ya daukaka darajarsa a Illiyyuna.

Farfesa Umar Muhammad Labdo, Malami ne a Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano.

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending