Connect with us

Hausa

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, Baƙon Shehu Maghili

Published

on

Magaji Galadima

 

 

A ranar Litinin 12 ga watan Disamba 2022 gwamnatin ƙasar Aljeriya ta aiko da wani jirgi na musamman domin ya ɗauki mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zuwa ƙasar ta Aljeriya domin halartar taron duniya na musamman don tunawa da rayuwa da kuma aiyukan shahararren malamin addinin Musulunci sharifi kuma masanin falsafa  wato Shehun malami Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na goma sha biyar. 

Jigin ya tashi daga Kano da karfe 9:45 na safe. A cikin waɗanda suka samu alfarmar raka Sarki wannan tafiya akwai Sarkin Dawakin Tsakar-gidan Kano Alhaji Ahmad Ado Bayero hakimin Kumbotso da Ambasada Ahmad Umar Ɗanmalikin Kano da Dakta Ibrahim Ɗahiru Bauchi wanda ya wakilci Sheikh Ɗahiru Bauchi da Malam Isa Sanusi Bayero da Dakta Lawi Atiku Sanka da kuma ni Magaji Galadima Kachallan Kano, sannan sai wasu malamai da sharifai na Kano da kuma fadawa hadiman Sarki.

Jirgin ya ɗan yada zango a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar inda ya ɗauki Sultan na Agadas da Sarkin Sharifan ƙasar Nijar da sauran malamai da muƙaddamai da malaman jami’a. Sarkin Kano da ‘yan tawagarsa sun sauka a Aljiyas babban birnin Aljeriya da misalin karfe 5:00 na yamma inda manyan ministoci da jami’an gwamnati dana diflomasiyya da kuma manyan malamai suka taryi mai martaba Sarki da tawagarsa. Daga nan akayi jerin-gwano aka raka Sarki masaukinsa.

A rana ta biyu wato Talata Sarki da ‘yan tawagarsa suka fita zuwa wajen taron ƙasa da ƙasa da aka shirya domin tunawa da shahararren malamin addinin musulunci masanin falsafa kuma sharifi wato Shehu Muhammad Abdurrahman al-Maghili wanda yayi rayuwarsa tun a ƙarni na sha biyar kuma har ya zo Kano zamanin Sarki Muhammadu Rumfa.

Al-Maghili ya zauna a Kano tsawon lokaci kuma ya bijiro da sababbin tsare-tsare ma su muhimmanci a fadar Kano, kana kuma ya yi rubuce-rubuce akan ibada da hukunci, sannan ya rubuta wani kundi da ya zama daftari na jagorar duk wani sarki na Kano da ma nahiyar yammacin Sudan.

Taron an shirya shi ne a babban ɗakin taro na ƙasar dake birnin Aljiyes.  A ranar buɗe taron Sarkin Kano da tawagarsa sun isa wajen da misalin karfe 9;00 na safe amma sai aka kaishi wani ɗaki ya zauna a kauwame har sai da ɗakin taron yayi cikar kwari sannan aka shigar dashi.

Toh dama an ɗauki makwanni ana ta yaɗawa a kafafen labarai cewa ƙasar ta Aljeriya zata karɓi bakuncin wani ƙasaitaccen Sarki mai alfarma da daraja daga garin Kano a Nijeriya, don haka mutanen ƙasar duk sun zaku suga wannan ƙasaitaccen Sarki. Saboda da haka yana shiga ɗakin taron sai duk aka tashi tsaye waje ya kaure da sowa da tafi, mata kuma na rabka guɗa, su kuma ‘yan badujala suka goce da wani irin take na musamman da ake kaɗawa mashahuran mutane in sun shigo wajen taro.

An ɗauki tsawon lokaci kafin a samu natsuwa lamurra su koma daidai sannan mai martaba Sarkin Kano figinai suka yi sayi ya zauna aka gyara aka kimtsa sannan aka fara gudanar da taro.

Daganan ne kuma sai aka fara jawabai, babban ministan harkokin addini na ƙasar shine ya wakilci shugaban ƙasa kuma yayi jawabin maraba ga mahalarta taron kana yayi godiya ta musamman ga Sarki Aminu Bayero a madadin shugaban ƙasa da al’ummar ƙasar baki ɗaya. Shima Sarkin na Kano  yayi jawabi inda ya nuna farin ciki da godiya ga gwamnati da jama’ar ƙasar baki ɗaya saboda kyakkawar taryar da aka yi masa, ya kuma isar da gaisuwar jama’ar masarautar Kano da Nijeriya baki ɗaya a garesu.

Sarkin ya yaba da hangen nesan waɗanda suka assasa wannan taro na tunawa da Shehu Maghili wanda yace yafi cancanta a kira shi da Bakano maimakon dan Aljeriya saboda da dalilai da dama. Ya baiyanawa mahalarta taron cewa a yanzu haka a cikin birnin Kano akwai unguwar Sharifai waɗanda asali jama’ar da suka zo Kano tare da Shehu Maghili sune ke zaune a wannan unguwa tun lokacin har zuwa yanzu, kuma shugabansu Sidi Fari shine Sarkin Sharifan Kano kuma yana da gurbin zama a majalisar Sarkin Kano.

A ƙarshen jawabin Sarki yayi godiya ga Allah wanda Ya ƙudura cewa a zamaninsa ne akayi wannan babbar hobbasa ta sake dawo da wannan tsohuwar alaƙa tsakanin Kano da Nijeriya da kuma ƙasar Aljeriya kamar yadda su Shehu Maghili suka shimfiɗa.

Daga nan kuma sai aka buɗe fage inda malamai da masana suka yita ƙwami akan tarihin rayuwa da rubuce-rubucen Shehu Maghili.

Bayan an tashi daga taron wannan rana ta farko, sai mutane suka yanyame Sarkin Kano, malamai da jami’an gwamnati da baƙi daga sauran ƙasashe kowa burinsa shine ya samu ya ɗauki hoto da Sarkin Kano.

Bayan an fito waje ma haka har zuwa inda ya shiga mota. Mu ma ‘yan kwarakar Sarki da kyar muka yakice ‘yan jarida masu son jin kwakwaf domin yawansu babu lokaci da zamu warware musu zare da abawa. Koda muka isa masauki sai muka tarar ashe tuni wasu jama’ar sun yi kwamba suna jiran isowar Sarki domin su samu su gaisa kuma su ɗauki hoto da shi.

 

Bayan ya shiga ɗaki kuma sai manyan malaman ƙasar su kuma suka yi layin shiga suna yiwa sarki addu’a har saida rana tayi gora sannan jami’an tsaro suka tare mutane suka hana su shiga don a kyale Sarki ya huta.

A rana ta biyu mai martaba Sarki da tawagarsa ya sake komawa wajen taron inda malamai suka ci gaba da gabatar da takardu.

Bayan anyi hutun zango na farko sai mai martaba Sarki ya fita domin kai ziyara ofishin jakadancin Nijeriya dake kasar ta Aljeriya.

Jakadiyar Nijeriya Hajiya Aisha Muhammad Garba ta taryi Sarki da tawagarsa kuma anyi jawabai masu muhimmanci.

Da maraice kuma har ila yau sai Jakadiyar ta shiryawa mai martaba sarki wata liyafar alfarma a gidanta inda aka gaiyaci ‘yan Nijeriya mazauna ƙasar Aljeriya da kuma wasu malamai daga Nijeriya.

A rana ta uku kuwa mai martaba Sarki ya halarci bikin rufe taron kuma abin ya ƙayatar ƙwarai musamman yadda Sarkin Kanon ya zama tauraro a wajen taron domin dai hankalin kowa na kansa tun daga farko har i zuwa lokacin da aka ja labulen rufe taron.

Da yammaci kuma sai shugaban ƙasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya gaiyaci Sarki Aminu zuwa fadarsa inda suka zauna suka yi zantuka na girma. Shugaban ƙasar yace yayi murna matuƙa da karɓar baƙuncin Sarkin, ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar tasu tana sane da tarihin masarautar Kano da rawar da Shehu Maghili ya taka wajen bunƙasa al’adu da addinin Musulunci a birnin Kano.

Shugaba Tebboune yace Sarkin Kano a wannan ziyara shi baƙon Shehu Maghili ne, duk da yayi wafati fiye da shekaru 600, wannan ziyara ta Sarki lallai Shehu Maghili shine sila.

Shi kuma a lokacin da yake maishe da jawabi Sarki Aminu yayi godiya ga Allah da Ya bashi ikon amsa gaiyatar shugaban ƙasar da kawo wannan ziyara, ya yabawa gwamnatin ƙasar Aljeriya saboda ɗawainiyar ɗaukar nauyin wannan taro mai muhimmanci.

Daga nan kuma sai yayi kira ga shugaban na Aljeriya da su haɗu su farfaɗo da hulɗar cinikayya da kasuwanci tsakanin Kano da Aljeriya wanda yace zai taimaka wajen ƙara yauƙaƙa danƙon zumunci tsakanin nahiyoyin biyu. Baya ga wannan kuma da yake ance lokacin iska ake cin ɗan jinjimi sarkin ya bukaci gwamnatin ƙasar ta Aljeriya da ta bawa ɗaliban jihar Kano tallafi na guraben ƙara ilmi a fannoni dabam-daban a jami’oin ƙasar inda shugaban ƙasar nan take yayi wuf yace ya amince da wannan shawara kuma yana jira in Sarki ya koma gida,  ya tsaro jadawalin yadda duk yake so ayi , su kuma in Allah Yaso zasu aiwatar. a nan dai akayi muwafuƙa duk shawarar tasu tazo daidai.

Daga nan suka yi bankwana cikin farin ciki da girmama juna.

A rana ta hudu mai martaba Sarkin Kano tare da wasu daga cikin ‘yan tawagarsa sun ziyarci garin Ain-Madhi wato ainihin garin da aka haifi Maulana Shehi Ahmadu Tijjani (RA) wanda ya kafa ɗarikar Tijjaniyya.

Sarkin ya ziyarci muhimman wuraren tarihi a garin sannan ya gana da manyan malamai da sharifai zuriyar Shehin inda suka yiwa Sarkin da Kano da Nijeriya  addu’oi na musamman.

A rana ta biyar Sarki ya kammala ziyarar kamar yadda aka tsara, don haka sai ya karyo linzami zuwa gida. Manyan jami’an gwamnati da malamai da kusoshin diflomasiyya da kuma jakadiyar Nijeriya sune suka raka mai martaba Sarki zuwa filin jirgin sama, akayi ban kwana kowa na cike da farin ciki.

Ko shakka babu wannan ziyara da mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayero ya kai jamhuriyyar dimokuraɗiyyar ƙasar Aljeriya ta buɗe wani sabon babi na dangantaka mai ƙarfi tsakanin ƙasar da kuma Nijeriya. Wannan tagomashi da Sarkin Kano yake samu a duk inda yaje lallai abin godiya ga Allah ne ga duk mai ƙaunar ci gaban jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Ɗadin daɗawa gashi har mai martaba Sarki yayi hobbasa har shugaban ƙasar na Aljeriya yayi alkawarin baiwa ɗaliban jihar Kano guraben ƙaro ilmin jami’a kyauta da shiryawa malamai da limamai kwasa-kwasai na ƙara sanin makamar aiki, sannan a waje ɗaya kuma shugaban na Aljeriya ya bada umarni cewa ayi duk abinda za ayi don ganin kwance duk wani daurin Gwarmai don sassauta hulɗar kasuwanci ga ‘yan kasuwar Nijeriya masu sha’awar zuwa Aljeriya.

Mai martaba Sarki ya samo nasarar da ba a taɓa samowa ba a bigiren dangantakar  siyasa ko diflomasiyya, don haka babu abin yi da ya wuce mu yiwa Allah godiya da muka samu Sarki wanda addu’ar magabata da kyakkawar mu’amala  da nagartaccen lamiri suke haskaka masa turbar tafiyarsa, ba kuskunda ba jalla-kujalle.

Fatanmu shine Allah Mabuwayi Ya kara wa Sarki lafiya da jimiri da jinkiri, yadda yake fafutukar samawa al’ummar Kano tudun dafawa, shima Allah Ka dafa masa.

Yadda Sarki ya ɗauko saitin gwadabe tun ba a je ko’ina ba a tafiyar yayi nuni da cewa nan da ɗan lokaci zai ginawa Kanawa rijiya gaba dubu wacce ko da an shekara saran  ruwa toh sai tamfatse.

A laaaafiya baƙon Shehu Maghili !!!

Magaji Galadima
Kachallan Kano
Disamba 25, 2022.

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Shekara 60 na Hausawa a Doron Ƙasa (4) – Farfesa Malumfashi

Published

on

Wannan wani raddi ne da Farfesa Ibrahim Malumfashi ya yi wa Abduljalil Ismail Ajis

 

Bayan dukkan wannan balaguro tare da sauran al’ummar duniya wannan ya haifar da damar da aka samu Hausawan wajen ƙasar Hausa suka sake haɗuwa da sauran ‘yan uwansu, musamman na ɓangaren jinin Uwa da ba su yi balaguro zuwa ko’ina ba a sassan duniya, waɗanda suke zaune a nahiyar Afirka a tsawon shekaru. Wannan haɗakar barbarar ‘yan’yawa ita ta samar da kai da ni da duk wani Badauri ko Bagobiri ko Bakatsine ko Bazamfare ko Bakabe ko Bazazzage ko Basantolo ko Bakano ko Bagunge ko Bahaɗeje ko Barane da wasu ƙasashe da al’ummun Hausawa da dama da suka yi rayuwa, suka ɓace a tsawon tarihi.

Wannan ba komi yake nuna mana ba sai al’ummar Hausawa ba na yanzu ba ne, shi harshen Hausa ne na yanzu, shi ma ba yanzun-yanzu, irin na yau ba ne, shekara dubbai ne ake magana. Ƙila tambayar da wasu kan iya yi zuwa yanzu ita ce yaya aka yi aka san waɗannan batutuwa da yawanci ba su a rubuce ko ba a ci karo da su ba a rubucen ko kuma me ya sa ba a zubo hujjoji da za a iya gani ƙwaro-ƙwaro domin tabbatar da batun ko akasin haka ba? Ta yaya yawancin irin waɗannan bayanai ba su bayyana ba ko da kuwa daga kunnuwa da suka girmi kakanni, ta ina aka samar da tunanin?

Ire-iren waɗannan tambayoyi an sha yin su game da wannan bincike, abin da zan iya cewa shi ne, yawancin bayanai ba su ɓullo daga tarihin da muka saba karantawa ba ne, sannan yawancin bayanan da yake sun tusgo ne daga rayuwar lokacin da ba tarihi a rubuce ko ajiye suna da wahalar karɓuwa nan da nan, haka kuma fagen nazarin tarihi da tarihihi da muka gwanance a ka, ba su iya fasalta su da kyau ba, amma wasu daga cikin bayanan na nan kimshe cikin adabinmu na gargajiya da waƙoƙi da kalamominmu na yau da kullum, ba mu dai kula ko nazarce su da kyau ba ne. Wannan giɓi shi ya sa aka koma cikin gonar nazarin ilmin ƙwayar halitta da ke tattare da jinin al’ummar duniya, ciki ko har da Hausawa domin samun mafita.

Shi wannan fage na nazarin ilimin ƙwayar halitta ya zama kandami ne na fahimtar rayuwa ta tsawon tarihi ko da kuwa ba a rubuta ko ajiye shi ba. Saboda binciken masana kimiyya ya gano cewa a cikin gudan jini ko ƙwayar halitta akwai tarihin al’umma da ke jibge, sai an buɗa shi za a kwashi ilimin da ke ɓoye. Domin kowane kalami ko waƙa ko zancen azanci ko gudanuwar addini ko kuma bazuwar al’adu na haihuwa ko aure ko soyayya ko mutuwa suna damfare a cikin jinin al’umma, ba su ɓacewa baki ɗaya, ke nan daga lokaci zuwa lokaci ana iya ƙwaƙulo su domin nazarin rayuwar yau.

Saboda haka yawancin bayanan da muka zubo a nan, sun samo asali ne daga bincike da nazari da aka samu yi daga ɗibar miyan bakina da jini, a matsayin Bahaushe aka ƙwanƙwance tarihin da ke ƙunshe a ciki a shekarar 2017, a can Amurka, a ɗakin bincike na (Genographic project), a lokacin kuma akwai tarin bayanai kan Hausawa da ‘yan uwansu da suka rigayi nawa, daga wannan banki ne aka samar da bayanai da suka nuna yadda rayuwar ‘Hausawa’ ta kasance a tsawon tarihi.

Daga sakamakon wannan bincike ne aka fitar da bayanan da ke haskaka mana yadda Hausawan wannan zamani suka wanzu, mai nuna daga ina Hausawa suka tuzgo, su wane ne ‘yan uwansu na kusa da na nesa. Abin da kuma ya fito fili ya haɗa da:

•Akwai jinin al’ummar yankin sassan ƙasashen Maleshiya zuwa Indonesiya da Filifins a cikin Hausawa wannan zamani, (miya ta kuka ko taushe da muke da su yanzu, akwai su a harshen Malay da makusanta).

• Akwai jinin Barbar na yankin Siwa a Arewacin ƙasar Masar har kashi 20 cikin 100 a cikin jinin Hausawan wannan zamani. A wannan yanki ne Hausawa suka yi bautar rana da muke bayyanawa ta waƙoƙin gargajiya da suka nashe a ƙasar Hausa tun da daɗewa. Wasun mu ba su manta irin wannan waƙa ba; ‘rana, rana buɗe, buɗe in yanka miki rago ki sha jini, shar, shar’. Ba aron wannan waƙa aka yi ba, jini da gado ne daga al’ummar Hausawa da suka rayu a Masar ta dauri. Nan kuma aka samo kalmomi irin na auratayya da soyayya da ke jibge a tunanin Hausawan yau, misali ‘so’ da ‘soyayya’ da ‘aure’ da ‘mata’ da ‘miji’ da wasu irin su da dama!

• Haka kuma Hausawa yau suna ɗauke da jinin mazajen da ke zaune a kudancin ƙasar Masar na kimanin kashi 6 cikin ɗari, shi ya sa ake cewa Hausawan yau tsittsigensu na Yahudawa da Kibɗawa ne, wato ‘yan uwa ne ga al’ummar Annabi Musa da ta Fir’auna.

 

Farfesa Ibrahim Malumfashi malami ne a Jami’ar jihar Kaduna ya wallafa wannan rubutun ne a shafinsa na Facebook.

Continue Reading

Hausa

Shekara 60 na Hausawa a Doron Ƙasa (3) – Farfesa Malumfashi

Published

on

Farfesa Malumfashi

Wannan wani raddi ne da Farfesa Ibrahim Malumfashi ya yi wa Abduljalil Ismail Ajis

 

Ke nan ko a wancan lokaci waɗannan al’umma ta Hausawa suna a doron ƙasa, a matsayin al’umma kuma ƙabila. Wani ƙarin haske kuma shi ne, ko kafin zuwan su wannan yanki na tsakiyar Afirka, ai sun rayu a matsayin mutane a sassan Arewacin Afirka; sun rayu a Kudancin Masar, inda yawancin ahalin Hausawa ta ɓangaren Uba suka wanzu, suka rayu a musamman yankin Siwa, wanda ke a Yammacin ƙasar Masar da iyakar ƙasar Libya kusan shekara dubu 20 da suka wuce.

Daga baya, Hausawa da ahalinsu sun yi rayuwa a wannan yanki na tsakiyar Afirka, kamar yadda na faɗa can baya, nan ne kuma aka samar da harsunan da aka yi wa laƙabi da ‘yan Ahalin Afrika da Asiya a daidai shekaru dubu 10 zuwa 9, nan kuma aka samar da tsatson ahalin harsunan Chadic, daga shekara ta 9,600 zuwa 5,200, inda aka haifar da harshen ‘Hausa’ da ‘yan uwansa, irin su Gwandara da Ron da Tangale da Warji da Bade da Angas da Barawa da Kare-Kare da sauran su. Ke nan akwai al’umma da ƙabilu da mutane masu mabambanta addinai da al’adu a wannan yanki, tun da daɗewa.

Idan aka nazarci harshen Hausa da harsuna da al’ummar waɗannan yankuna da ‘Hausawa’ suka taso daga ciki can baya, musamman daga yankin Maleshiya a Asiya da yankin Larabawa, musamman ɓangarorin Yemen da Falasɗinu da Saudi Arabiya da Masar da Isira’ila za a tsinci wasu al’adun ‘Hausawa’ da addinai da wasu kalmomi na harsunan waɗannan yankuna a cikin rayuwar Hausawa ta yau; dubi lamarin bautar rana, ire-iren abinci da sutura da soyayya da mulki da waƙe-waƙen gargajiya. Akwai misalai na kalmomin Hausa na yau da suka samo asali daga waɗannan yankuna da addinai da al’adu da za su yi mana jagora, in sha Allah.

Bayan haka zaman Hausawa na tsawon tarihi a Arewacin Afirka, a tsakanin ‘yan uwa da abokan hulɗa kamar na zamanin Annabi Ibrahim da Annabi Musa, wato waɗanda suka wanzu cikin harsunan Ibrahimanci da na Misirawan dauri da Yahudawan zamanin da kuma Kibɗawa, daga cikin waɗannan al’umma, wasu sun yi hijira zuwa yankin ƙasar Hausa da maƙwabtanta na yanzu tun wancan zamanin, inda suka yi tarayya da ‘yan uwansu, wato ‘Hausawa’ zaunannu, waɗanda suka daɗe suna bautar gargajiya, kuma ba su san wani abu addinin zamani ba, domin ba a saukar musu da addini ko Annabi ba, sai daga baya ta hanyar shigowar waɗannan baƙi da suka taɓa yin ire-iren waɗannan addinai a can baya da suka nashe da su, har kafin zuwan masu yaɗa addini na zamani daga baya.

An ga ɓirbishin irin waɗannan al’umma a wasu sassan ƙasashen Hausa da suka haɗa da Daura da Gobir da Kano, wanda ya nuna mana cewa ‘Ibrahimawa’ da ‘Larabawa’ da da ‘Misirawa’ da ‘Yahudawa’ da ‘Kibɗawa’ da wasu alummu masu yawa sun zaunu, sun zaune, a sassan ƙasar ‘Hausa’ ko kafin sake bayyanar Larabawa da addinin Musulunci ƙasar Hausa, daga baya.

Idan an natsu, za a fahimci cewa ‘Hausawan’ dauri kusan iri uku ne ko huɗu, wasu na ganin ma sun kai biyar a doron ƙasa kafin Hausawa zamani. Sun kuwa haɗa da ‘Hausawa’ da suka rayu cikin aljanna a zamanin Annabi Adamu, (atishawa kalma ce tun zaman aljanna) da kuma Hausawa da suka rayu a doron ƙasa bayan an sauko da Adamu da Hawwa’u wannan duniyar, suka haihu da hayayyafa har ta kai Ƙabila ya kashe Habila aka fara mutuwa a doron ƙasa, (ke nan sunan Adamu da Hawwa’u da mutuwa) suna tare da ‘Hausawa’ tun wancan lokaci. Akwai ‘Hausawa’ da suka rayu cikin kwale-kwalen Annabi Nuhu da kuma bayan ruwan Ɗufana da sake sauka a bisa doron ƙasa. Kalmomi irin su Nuhu da Ɗufana da Tantabara, (uwar alƙawari) da Jaki da doki, tun lokacin ‘Hausawa’ ke tafe da su a rayuwarsu, har zuwa yau, ba aro suka yi ba.

Haka batun yake game da rayuwa a zamanin Annabi Ibrahim, ‘Hausawa’ ma sun nasu a lokacin, Abram makusanci ne da Abiramu ko Abrahamu ko Ibrahimu ko Ibrahim, haka kuma Basaraken nan Lamarudu (Namrud ko Nimrod) da ƙasar da Annabi Ibrahim ya tare daga baya, wato Ƙan’ana, (Canaan), akwai su ko a zamanin Dauramomin ‘Daura’, kafin zuwan Musulunci da Kiristanci a ƙasar Hausa.

Farfesa Ibrahim Malumfashi malami ne a Jami’ar jihar Kaduna. Ya wallafa wannan rubutun ne a shafinsa na Facebook.

Continue Reading

Hausa

Shekara 60 na Hausawa a Doron Ƙasa (2) – Farfesa Malumfashi

Published

on

 

 

Farfesa Ibrahim Malumfashi

 

Wannan wani raddi ne da Farfesa Ibrahim Malumfashi ya yi wa Abduljalil Ismail Ajis

Kashi na farko, an fahimci cewa ko da ‘ya’yan Adam na zamani suka wanzu a doron ƙasa daga shekara dubu 200, wasu suka ce daga shekara dubu 150, kamar yadda masana kimiyyar asali (geneticists) suka bayyana, al’ummar Hausawa iri biyu ne aka yi a lokacin; zaunannu, wato ‘yan ƙasa, (autochonous) waɗanda ba su yi ragaita ba a doron duniya, iyakar su nahiyar Afirka ta dauri, sun kuma rayu a yankin tsakiyar Afirka, musamman ɓangaren ƙasar Habasha ta yanzu, a wani loko da ake kira Omo-Kibish.

Waɗannan al’umma su ne kaɗai suka rayu a ban ƙasa, su ne kuma daga baya suka barbazu zuwa sassan duniya, suka samar da dukkan al’umnar duniya, baƙake da farare, wato waɗanda masanan ke cewa sun taimaka wajen gina sabuwar duniya da mutane da ke cikin ta, (peopling of the world), ciki har da al’ummar da suka yi rayuwa a sassan ƙasar Hausa.

Ke nan ko da wasu ‘yan uwan Hausawa suka garzaya a doron duniya domin hayayyafa da zaunewa a duniya, sauran ‘yan uwan Hausawan na nan gida zaune, sun kuma rayu shekaru aru- aru da suka wuce, su ne Hausawan asali in ka ga dama kira su da Maguzawa. Za mu dawo kan su nan gaba.

Tunani na biyu shi ne ne su ‘yan uwan Hausawa da suka bar yankin Afirka da ke a Omo-Kibish, a ƙasar Habasha ta yanzu, a farkon wannan zamani da aka samar ɗan Adam na zamani wato (modern man), sun fara hayayyafa a bisa doron ƙasa ne a bisa hanyarsu ta zuwa sassan Arewacin Afirka ta dauri, irin sassan ƙasashen yankin Tsakiyar Afirka zuwa yankin Aljeriya da Marutaniya da Maroko da Masar da Sudan, inda suka bar wasu al’ummar a wurin, suka wuce zuwa sassan nahiyar Larabawa da Lebenti (Lavent) na yanzu, suka rayu a tsawon zamani, a wurare irin su yankin ƙasashen Larabawa, irin su Saudiyya da Yemen da Falasɗinu da Isra’ila da Jordan da Lebanon da Siriya.

Nan ma sun bar wasu daga danginsu, suka wuce zuwa Kudu maso gabashin Asiya, suka yi zango na ƙarshe a rayuwarsu ta zaune duniya. Ƙasashen ko yankunan da za a iya samun gyauro waɗannan al’umma a yau sun haɗa da Maleshiya da Tailan da Filifin da Indoneshiya da Burunai da Singafo, nan ne yankin da al’ummar Malay suka rayu, ana iya cewa su ne kakannin-kakannin-kakannin Hausawa na zamani ko na ƙarshe da masu nazarin jini da ƙwayar halitta suka tabbatar.

Waɗannan al’umma sun zaune a wancan yanki na tsawon shekaru, daga baya wasu daga cikin tsatson Hausawa da suka rayu a can sun taso, wato sun baro wannan yanki, musamman daga shekara dubu 60 da na yi bayani a can baya, suka sake bin rariyar da iyaye da kakanninsu suka biyo, domin komawa nahiyar Afirka. A bisa wannan tafiya sun sake haɗuwa da sarƙewa da wasu daga ‘yan uwansu da suka bari a baya wajen wancan tafiya ta farko da suka yi inda suka bar su da sake zama a yankin Larabawa da Labenti da kuma yankin Afrika ta Arewa.

Saboda ko da suka sake haɗuwa da narkewa da sauran ‘yan uwansu da suka bari tun da daɗewa wasu sun ƙara yin gaba, zuwa yankin nahiyar Turai, su ne ake cewa ba su da alaƙa ta ƙuƙut da Hausawa na dauri, domin sun raba hanya da daɗewa, ba su kuma ƙara haɗuwa da juna ba. Daganan kuma wasu daga cikin sauran ‘yan uwansu suka suka tsallaka zuwa nahiyar Amurka, a daidai shekara dubu 15 da suka wuce.

Su kuwa gyauron Hausawan da suka zaunu a sassan Larabawa da Labenti da Arewacin Afirka na tsawon shekaru, sai daga shekara ta dubu 20 zuwa dubu 15, wasu suka motsa zuwa yankin kogin Chadi inda suka yi mazauni na tsawon lokaci.
A zamansu ne na wannan yanki kamar yadda na faɗa a wani rubutun can baya, aka samar da harsunan da aka yi wa laƙabi da ‘yan Ahalin Afrika da Asiya a daidai shekaru dubu 10 zuwa 9, nan kuma aka samar da tsatson ahalin harsunan Chadic, wanda ya haifar da harshen Hausa da ‘yan uwansa, irin su Gwandara da Ron da Tangale da Warji da Bade da Angas da Barawa da Kare-Kare da sauran su.

 

Farfesa Ibrahim Malumfashi malami ne a Jami’ar jihar Kaduna ya wallafa wannan rubutun ne a shafinsa na Facebook.

Continue Reading

Trending