Hausa
Shekara 60 na Hausawa a Doron Ƙasa (1) – Farfesa Malumfashi
Farfesa Malumfashi
Wannan wani raddi ne da Farfesa Ibrahim Malumfashi ya yi wa Abduljalil Ismail Ajis
Afwan, na so na dawo da zancen a sahar da ka yi naka martanin, amma da na leƙa sai na ga ba mutane da yawa a wurin da za a iya tattaunawa, a ƙaru, shi ya sa na dawo da mu a nan. Ko ba komi nan ne asalin batun tun farko.
Abubuwa uku ke da muhimmanci daga martanin da ka yi kan nawa batun, kuma su ne za su yi mana jagora daga yau, ISA.
1. Asalin samuwar Ɗan Adam da samuwar al’ummar Hausawa da sauran al’ummar duniya da harsunansu da al’adu.
2. Abu na biyu shi ne mu tambayi kanmu ko al’ummar Hausawa sun rayu a wasu yankuna na duniya kafin su zaune a yankin ƙasar Hausa da suke yanzu ko kuwa dai ba wata al’ummar da za a kira da Hausawa sai Maguzawa da muka saba ji da gani, waɗanda za a kira da kifin rijiya?
3. Shin babu wasu kalmomi ko jumloli ko batutuwa na asali da Hausawa suka gada daga samuwar ɗan Adam tun daga aljanna har zuwa doron ƙasa da bayan ruwan ɗufana da samuwar ɗan Adam na zamani daga shekara ta dubu 150. Idan Hausawa sun rayu a waɗannan zanguna, wanda ba a iya ƙaryatawa kai tsaye; (a kula, ina magana ne kan Hausawa, wato al’umma a nan, ba masu harshe ko magana da Hausa a yau ba,) to kuwa waɗannan mutane sun taho da rayuwar waɗancan zamunna, kuma sun ci gaba da tu’ammali da su zuwa wani lokaci suka ɓata daga baya suka sake cin karo da su a zamantakewa ta zamani.
A saha irin haka da muke irin wannan tattaunawa, inda ba cikakken aji ba ne da za a iya darje komi ya fito fili, dole a samu irin wannan tunani naka da ma wasu irin ka, kamar yadda aka samu a ‘yan kwanakin nan dangane da asalin Hausawa.
Ba na yi wancan rubutu ba ne domin koɗa ko nuna isa ta Hausawa da neman ɗora su a matsayin da ba nasu ba, na yi ne saboda haka batun yake, abin da aka karantar da ni da kuma abubuwan da na yi nazari ne a tsawon shekaru, wannan ya nusar da ni cewa Hausawa mutane da suka rayu kamar sauran al’ummar duniya, ba su da bambanci da sauran al’umma ta fannin asalin bil Adama, sai dai wani abu da yawancin mutane masu nazari da sharhi ba su kai hannu gare shi ba shi ne, bincike na asalin Hausawa ya wuce abin da aka saba ji, wato daga shekara dubu 1 ko 2 ko 3 ko kuma 5 da ake tsayawa.
Wannan ne ya sa kai da masu irin naka tunanin ke ganin ina ma aka san wasu Hausawa a doron ƙasa, domin Hausawa ba kowan kowa ba ne da za a haɗa su da Larabawa ko Girkawa ko Yahudawa ko Asiyawa da makamantan su, sai ka ce su waɗannan da ake magana kai, tun daga farkon rayuwa su kaɗai aka halitta!
Saboda daidaita tunani zan ƙoƙarta tattaɓo wasu daga cikin waɗannan matsaloli da ake fuskanta ISA. Na so na yi bayanin irin na malamin jami’a da ke magana da masana ‘yan uwansa a fagen nazari, ana yi ana kawo tushen bayani domin kafa hujja, amma ba zai samu ba, saboda sahar fesbuk ba jami’a ba ce da ƙila kowa zai iya fahimtar inda aka fito da inda ake da yadda aka samu matsaya game da batutuwa irin wannan. Amma in na kammala tattaunawar ISA, ƙila cikin kwana 3 ko 4 nan gaba, zan ajiye maka manazarta da za ka bibiya domin tabbatar da abin da na faɗa ko ƙaryatawa ko kuma samun ƙarin haske.
Wannan fage na asali da samuwar ɗan Adam da kuma Hausawa, masana da dama sun taɓo waɗannan batutuwa masu rikitarwa a wurare da dama da ba lokacin da zan daddage su saboda kafa hujja, amma ga abubuwa uku da za su iya yi mana jagora kafin mu ci gaba da faɗaɗa tunanin.
Farfesa Ibrahim Malumfashi malami ne a Jami’ar jihar Kaduna ya wallafa wannan rubutun ne a shafinsa na Facebook.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Kwankwaso Congratulates Gov. Yusuf on NUT Award for Education Reforms
Former Kano State Governor and National Leader of the New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, has congratulated the current governor, Abba Kabir Yusuf, on receiving the prestigious NUT Golden Award from the Nigeria Union of Teachers (NUT) in recognition of his significant contributions to the education sector.
In a message posted on his verified X (formerly Twitter) handle, Kwankwaso commended Governor Yusuf for his unwavering dedication to revitalizing Kano’s education system.
He described the governor as a “game changer” in the sector and encouraged him to remain steadfast in pursuing his educational reforms.
“Congratulations to His Excellency Abba Kabir Yusuf on the NUT Golden Award for his achievements in the education sector,” Kwankwaso wrote.
He further urged Governor Yusuf to strengthen his commitment toward achieving his broader goals in education reform.
The award was presented during the 2024 World Teachers’ Day celebration, which took place at Eagle Square, Abuja.
Organized by the NUT in collaboration with the Federal Ministry of Education, the event brought together teachers and educational leaders from across Nigeria to recognize and celebrate significant achievements in education reform.
Governor Yusuf was honored with the NUT Golden Award for his transformative efforts in rescuing Kano’s education system, which had suffered from years of neglect.
His administration has been lauded for implementing policies aimed at improving school infrastructure, increasing access to quality education, and ensuring the professional development of teachers in Kano.
This recognition comes as part of a broader acknowledgment of his leadership and commitment to enhancing educational opportunities for all in the state.
The event, which marked the 2024 edition of World Teachers’ Day, highlighted the importance of teachers and their role in national development, with the NUT acknowledging the critical support of political leaders like Governor Yusuf, who are spearheading reform efforts.
The governor’s administration has undertaken various initiatives to address the challenges in Kano’s education system, including rebuilding dilapidated schools, recruiting more teachers, and prioritizing student enrollment, especially for girls.
Governor Yusuf’s receipt of the NUT Golden Award serves as a milestone in his administration’s ongoing efforts to reposition Kano as a leading state in education, setting an example for others across the country. His reforms have drawn praise.