KANUN LABARAI

Babbar Kotu a Kano ta dakatar da karamar kotu tuhumar shugaban Hukumar KAROTA

Published

on

Aminu Abdullahi

Babbar kotun jihar Kano mai lamba bakwai ta dakatar da kotun majestiri mai lamba 12 daga ci gaba da sauraron shari’ar zargin  cin hanci da rashawa da ake yiwa shugaban Hukumar KAROTA Bappa Babba Dan Agundi.

Kano Focus ta ruwaito mai shari’a Malam Usman Na’abba ne ya bada umarnin  dakatarwar ranar Litinin har sai babbar kotun ta duba ko ma karamar kotun na da hurumi umartar wanda ake kara da ya bayyana da kansa a gabanta.

Haka kuma ta sanya ranar 26 ga watan Oktoba da muke ciki domin fara nazartar shari’ar da aka faro a karamar kotun.

Tun da fari dai lauyan da ke kare shugaban hukumar Karota Barista Mutawakil Ishaq Muhammad, ne ya garzaya babbar kotun yana kalubalantar hukuncin da kotun Majistiret mai lamba 12 karkashin mai shari’a Muhammad Jibril da ta nemi shugaban Hukumar ta KAROTA Bappa Babba Dan Agundi ya gurfana a gaban ta ba tare da wakilci ba.

Idan ba a manta ba dai wani direban Adai-daita sahu Abdullahi Yahya Mai Sango ne ya shigar da karar gaban kotun Majestiri yana kalubalantar Baffa Babba Dan Agundi bisa laifin cin hanci da rashawa da kuma cuta kan na’urar Tracker.

Hakan ta sanya kotun majistirin ta aike da sammaci har sau biyu ga Dan Agundi da ya bayyana a gaban ta sai dai hakan yaci tura.

Sai dai lauyan mai kara Barista Abba Hikima Fagge yace dakatarwar da babbar kotun tayi na ci gaba da sauraron shari’ar a karamar kotun ba yana nufin mista Dan Agundi ba zai bayyana a gaban kotu ba.

A cewar sa hakan zai kawo tsaiko ne kawai amma da zarar babbar kotun ta kamala nazarin ta za ta bada umarini ya bayyana.

Click to comment

Trending