KANUN LABARAI
Angwaye a Kano na daga aure saboda hauhawar farashin siminiti
Aminu Abdulahi
Hauhawar farashin siminti ya jayo matasa masu shirin yin aure musamman ma masu karamin karfi a jihar Kano daga auren su.
Kano Focus ta ruwaito a ‘yan kwanakin nan ne aka samu kari mai yawa akan farashin siminti da hakan ya janyo karuwar farashin wasu daga cikin kayan gine-gine.
Farshin siminti dai ya tashi ne daga N2,700 ya koma N3,500 kana daga bisani ya koma N4,000 kan kowannen buhu.
A binciken da jaridar Kano Focus ta gudanar ta gano yadda simintin ya yi karanci a kasuwa duk da karuwar farshin nasa.
Nazifi Dangi Al-Mustapha mazaunin unguwar Tukuntawa a nan Kano ya shaidawa jaridar Kano focus cewa matukar farashin siminti ya cigaba da tafiya a haka, to tabbas akwai yiwuwar ya dakatar da shirye shiryen auran sa.
Ya ce ya fara aikin gina gidan sa da zai tare nan da watanni uku masu zuwa sai dai sakamakon karin kudin simitin hakan yasa dole ya tsaida ginin gidan nasa.
Shi kuwa Abubakar dake unguwar Kankarofi a birnin Kano cewa ya yi an daga bikin sa da ya kamata a yi nan da makwanni biyu saboda rashin karasa Gidan da zai shiga.
A cewar sa yanayin samun kudin sa ba zai iya sayan simiti a farashin naira N4,000 ba kana ya biya sauran bukatun sa na rayuwa.
“Ba yadda zanyi ya zamemin dole a daga bikin domin kuwa bazan iya siyan simitin a farashin naira N4,000 ba”.a cewar sa.
Shi kuwa malam Yusuf Rabi’u Kanemi, dake garin Tudun Wadar Dankade, ya ce abin takaici ne ace ana siyan simiti naira N3,500 zuwa N4,000 la’akari da halin da ake ciki na matsin rayuwa.
Kanemi ya kuma ce yanaso ya yi aure amma tsadar siminti tasa dole ya dakata da ginin gidan sa zuwa wani lokaci.
Bama samun ayuka yadda ya kamata
Wasu daga cikin magina da Kano Focus ta zanta da su sun bayyana yadda kasuwar ta su ta tsaya cak.
Wani magini a nan Kano Yusuf Salisu Kankarofi ya ce matukar hakan ta ci gaba da faruwa to kuwa suna cikin fargarbar daina samun aiki yadda ya kamata.
“Da yawa abokan aikina sun kirani sun gayamin cewa basa samun aiki saboda siminti ya yi tsada.
“Hakan ya sa mutane da dama suka tsaida gine-ginensu musamman ma masu karamin karfi.” inji Kankarofi.
Zanga-zanga ta haifar ta tashin farashin
Su kuwa masu sayar da siminti da Kano Focus ta zanta da su sunce halin da ake ciki na rashin kwanciyar hankali a kasar nan ne ya jawo matsalar tashin farashin.
Guda daga cikin masu sayar da simintin a nan Kano Malam Ahmad Shu’aibu ya ce mafiya yawan masu dakon simintin sun daina daukowa zuwa arewacin kasar nan.
Haka zalika ya kara da cewa kamfanonin da ke samar da simintin suma ba safai suke samarwa ba kamar a baya.
Sai dai ya yi albishir da cewa farashin zai sauka nan ba da jimawa ba da zarar lamura sun koma dai-dai.
Hausa
Mutane 18,000 sun amfana da aikin ido kyauta ta Gidauniyar Mangal a Katsina
Kimanin marasa lafiya masu rauni 18,000 da ke fama da cututtukan ido daban-daban a jihar Katsina sun amfana da ayyukan kulawar ido da tiyata kyauta da Gidauniyar Mangal ta dauki nauyi tun bayan kafuwarta a shekarar 2016.
Wani mamba na kwamitin amintattu (Board of Trustees) na gidauniyar, Malam Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin kaddamar da aikin tiyatar ido na zangon karshe na shekarar 2025 a Cibiyar Ido ta Katsina.
Kabir ya bayyana cewa kimanin mutane 7,000 ne suka amfana a shekarar 2025 kadai, daga sassan jihar Katsina, jihohin makwabta, har ma da wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar.

A cewarsa, gidauniyar ta fara tantance wadanda za su amfana kimanin makonni biyu da suka gabata, inda marasa lafiya da dama suka samu magunguna kyauta da tabarau na likita.
Kabir ya kara da cewa wadanda ke bukatar tiyata an dauki nauyin dukkan zaman asibitinsu gaba daya, yana mai cewa kimanin marasa lafiya 2,000 aka tantance a yayin aikin zangon karshe da ake ci gaba da yi.

Ya sake jaddada kudirin gidauniyar na inganta samun kulawar lafiya, yana bayyana shirin a matsayin wani bangare na nauyin alhakin zamantakewar kamfanoni (corporate social responsibility).
“Manufarmu ita ce tallafa wa kokarin gwamnati tare da rage nauyin kudin kula da lafiya ga mafi rauni, musamman wadanda ke fama da matsalar biyan bukatun rayuwa,” in ji shi.

Wani likitan ido a cibiyar, Dokta Ahmad Hamza, ya bayyana cewa an gano marasa lafiya da dama na fama da cutar idon toka (cataract) da glaucoma, cututtuka da galibi ke bukatar tiyata.
Ya jaddada muhimmancin duba ido akai-akai, yana mai cewa gano cuta da wuri na taimakawa wajen hana asarar gani ta dindindin da cututtukan ido masu zuwa a boye ke haifarwa, kamar glaucoma, cataract da lalacewar macula (macular degeneration).

Daya daga cikin wadanda suka amfana, Malam Yusufa Usman, ya ce ya shafe sama da shekaru biyu yana fama da matsalar gani amma ba shi da ikon biyan kudin tiyata.
“Tsawon shekaru biyu ban iya gani sosai ba, amma yau na yi tiyata kuma ina da fatan ganina zai dawo.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya saka wa Gidauniyar Mangal da alheri bisa wannan kyakkyawan aiki.
“Ina fatan sauran masu kudi za su yi koyi da wannan abin a yaba,” in ji Usman.

Wata mai amfana, Aisha Muntari daga kauyen Bakuru, ta bayyana kwarewarta yayin da take jiran a kai ta dakin tiyata.
Muntari ta ce ta kamu da matsalar ido kimanin shekara guda da ta wuce kuma ta kusa yanke tsammani kafin ta samu labarin shigar gidauniyar, tana mai bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba ganinta zai dawo.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
