KANUN LABARAI
Soyayyar Instagram: Za a daura Auren ‘yar America da dan Kano ranar 13 ga Disamba
Zulaiha Danjuma
Za a daura auren matashin nan dan jihar Kano Sulaiman Isah Isah da Ba’amurkuya Janine Stanches a ranar Lahadi 13 ga watan Disamba mai zuwa.
Kano Focus ta ruwaito za a daura Auren ne a masallacin juma’a na barikin Mopol da ke unguwar Fanshekara a karamar hukumar Kumbotso.
Idan ba za a manta ba dai an sanya watan Maris di da ya gabata ne a matsayin watan da za a daura auren tsakanin masoyan biyu sai dai bullar cutar korona ta hana.
Hakan ta sanya tilas Janine ta koma kasar Amurka domin ci gaba da jira ya yin da shi ma ya koma unguwarsa ta fanshekara aka ci gaba da zaman jira.

Asalin soyyaar
Janine da Sulaiman dai sun hadu ne a sahafin sada zumunta na instagrman.
Sanchez mai shekaru 46 yar kasar Amurka tafada kokin soyayya ne da Isah dan shekaru 26 bayan watanni 10 suna soyayyata Instagram.
A wata hira da ta yi da jaridar Kano Focus mis Sanchez ta ce Isa ne ya fara yi mata magana, inda ita ma ta amsa masa, suka kuma ci gaba da hira da har ta rikide ta zama soyayya.
Shi ma Isa ya ce yana da burin ya ga auri baturiya ko dan ya yansa su ta so da kalar turawa.
“Bayan dogon lokaci muna soyayya ne kuma na gayyato ta Najeriya domin ta gana da iyaye na ta kuma ga dangina.” A cewar Isah.
Komawa Amurka
Mis Sanchez wadda ke sana’ar sayar da abinci a wani gidan abinci dake Lindon a jihar California ta ce za ta dauke Isa ne zuwa Amurka bayan sun yi Aure.
Ta ce dalilinta na dauke shi zuwa kasar Amurka sh ne, tana da yara biyu da mijinta na baya, a kuma tsarin sub a za ta iya yin nisa da yaran nata ba.
Sai dai da aka tambayeshi ko zai iya binta? Isah ya ce ba bu wani dalili da zai sa ya kasa bin ta tun da dai matarsace.
Ya ce zai dinga kowo ziyar gida akai-akai domi ganawa da dangi sa da iyayesa.
Ya ce yana daga cikin alkawarin da suka dauka cewar idan sun haihu to tilas ne yaransu su dinga zuwa Najeriya don kula da dangi.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
