Connect with us

KANUN LABARAI

Kungiyar ‘yan gwanjo ta gudanar da adduo’in neman zaman lafiya a Kano

Published

on

Aminu Abdullahi

Wata kungiya mai suna Musan Juna Jeans and T-Shirts Association da ke kasuwar Kofar Wambai a nan Kano ta gudanar da saukar alqur’ani da addu’o’i domin neman daukin Allah kan matsalolin da suka addabi jihar Kano da kasa baki daya.

Kano Focus ta ruwaito cewa kungiyarta gudanar da taron addu’ar ne a ranar Labara a maimakon taron da take gudanarwa duk karshen shekara.

Haka zalika kungiyar ta tallafawa mambobin kungiyar goma sha biyar da aka yi musu fashi a hanyar Kano zuwa Onitsha da kudade domin rage musu a sarar da suka yi.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin Abdulkadir Jiyali ya ce ‘yan fashin sun karbe masa naira miliyan daya da dubu dari hudu da ya jefa shi cikin katutun bashi.

Ya ce yana matukar farin ciki da tallafin da aka bashi domin kuwa yana ji tamkar am bashi sabon jarine da zai cigaba da gudanar da sana’ar sa.

A nasa bangaren wani dan kabilar Igbo da ya amfana da tallafin mai suna Sunday ya ce ya dade da fidda rai na cigaba da kasuwanci.

“Ina kwance sai naji ance nazo taro abinda banyi tsammani ba kenan.

Ina zuwa sai naga wannan abin alheri gaskiya nayi matukar farin ciki,” inji Sunday.

Ya kuma ce yana fata jarin sa ya sake habaka don ya ci gaba da dogara da kansa kamar yadda yake a da.

Shugaban kungiyar Musbahu Ibrahim Aliyu Sudawa ya ce kungiyar ta tallafawa wadanda suka yi asararne da kaso daya cikin biyar na abinda kowannen su ya rasa.

Ya kara da cewa kusan shekaru shida da kafa kungiyar, tana bada tallafi ga bangarori daban daban ga ‘yan kungiyar da suka gamu da wani iftila’i ba tare da yin la’akari da kabila ko yaren mutum ba.

A nasa bangaren mai magana da yawun kungiyar Gwani Idris Abdulsalam Maihaniniya ya ce kungiyar ta na duba mambobin kungiyar masu karamin karfi don tallafa musu.

Ya ce daga kafa kungiyar zuwa yanzu kungiyar nada mambobin fiye da dari biyu.

“Duk wata muna yin saukar karatun alqur’ani kuma wannan yazo akan gaba dukkan wata nasara muna samuntane da hadin kan ‘yan kungiyar,” a cewarsa.

Haka zalika ya yi addu’ar neman samun zaman lafiya a jihar Kano da kasa baki daya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending