KANUN LABARAI

Na shirya tsaf domin tunkarar malaman Kano-Abduljabbar Kabara

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara ya ce ya shirya tsaf domin yin mukabala da malaman Kano kamar yadda gwamnatin Kano ta bukata.

Kano Focus ta ruwaito malamin ya bayyana haka ne ta bakin lauyansa Rabi’u Abdullahi ya yin da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a nan Kano.

Rabi’u Abdullahi ya ce ya yi magana da malamin kan ko ya shirya shiga, inda ya amsa da cewar ya matsu ranar ta zo domin a tattauna.

“Inaso na sanar daku cewa Sheik Abduljabbar Kabara ya shirya tsaf domin tunkarar malaman Kano, fiye ma da yadda gwamnati ta matsu da a yi”

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 3 ga watan Fabrairun wanna shekara ne gwamnatin Kano ta dakatar da sheik Abduljabbar daga yin wa’azi biyo banyan zarginsa da furta kalamai marasa dadi.

Haka kuma gwamnati ta amince ya zauna da malaman Kano a tattuna kamar yadda ya nema.

Gwamnatin Kano ta kuma amince a yi zaman tsakaninsa da sauran malamai a fadar mai martaba Sarkin Kano a wata rana da za a sanar nan gaba.

Click to comment

Trending