Connect with us

KANUN LABARAI

Za a kwace adai-daita sahun duk wanda ya fita zanga-zanga

Published

on


Aminu Abdullahi

Gamayyarkungiyoyin direbobi da masu bada hayar adaidaita sahu a jihar Kano sun yi barazanar kwace baburin adaidaita sahun duk wanda yaki biyan harajin naira dari da gwamnatin jihar Kano ta bada umarni.

Kano Focus ta ruwaito cewa shugaban kungiyar Mansur Tanimu ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka gudanar a ranar Lahadi.

Ya ce ko kadan masu bada hayar mashin ba za su dagawa duk wani direba kafa wajen biyan kudi ba, matukar yaki fita aiki da sunan zanga zanga.

“Bama goyan bayan zanga-zangar da suke yi kuma ba da yawunmu za su tafi yajin aiki ba.
“Kuma mun sanya wakilan mu da za su dauki lambar baburin duk wani da yafito yin zanga zanga.

Kuma duk wanda muka kama zamu kwace baburin sa,” a cewar sa.

Ya ce kungiyar su za ta dagawa direbobin kafa daga karbar kudin da suke biya na babura don su biya kudaden harajin zuwa wani lokaci.

Ya kara da cewa a wasu jihohin kasar nan direbobin na biyan haraji kullum da ya zarta na jihar Kano.

Ya kuma ce ko kadan ba gaskiya bane zargin da wasu keyi na cewa gwamnati ce ta tilastawa shugabannin kungiyar su goyi bayan biyan harajin na naira dari dari ba.

“Mune ma da kanmu muka ga dacewar mu biya haraji shiyasa muka zauna da gwamnati muka gaya mata cewa wasu jihohin ma 500 zuwa 1000 kowa take biya a kullum.

“Dan haka muna kira ga mambobinmu da kada su shiga cikin wannan al’amari kuma akwai gurare 52 na yin rijista” inji shi.[tps_title][/tps_title]

Ya kuma ce duk mai son zaman lafiya da kishin jihar Kano to zayyi biyayya ga umarnin da gwamnati ta bayar.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending