Connect with us

KANUN LABARAI

Ko me yasa ‘yan KAROTA suka kauracewa titinan Kano

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Wani abu da ba a saba gani ba a jihar Kano shi ne a wayi gari haka sidda ba tare da ganin jami’an KAROTA a kan hanyoyi ba.

Sai dai a zagayen da Kano Focus ta gudanar a yau ta gano yadda jami’an suka yi batan dabo a kusan dukkanin titinan jihar nan.

Wannan dai ta sanya jama’a da dama ke ganin hakan na da alaka da yajin aikin da yan Adai-daita sahu ke yi a fadin Birnin Kano.

Muhammad Ibrahim wani matashi ne da muka iske yana bada hannun a maimakon jami’an KAROTA a kan titin Gadon-kaya ya ce yadda yaga al’amura sun cakude ne yasashi tallafawa.

Ya ce yana tsammanin jami’an na KAROTA sun ki fitowa ne saboda tsoron kada masu zanga-zanga su farmusu.

“Kasan yau masu Adai-daita sahu suna yajin aiki, kuma fushi suke da hukumar KAROTA.

“Kaga ke nan idan suka fito komai zai iya faruwa domin kuwa za su huce a kansu.

Shi ma Nuhu Muhammad ya ce mataukar yan KAROTA suka fito bakin aiki a yau to ba shakka al’amarin ba zai yi kayau ba.

“Yan adai-daida sahu suna ciki da su, ka ga idan suka fito aiki ai kaddamar musu kawai za a yi.

“Sun yi dabara da suka ki fitowa, don ko ni nan ina ciki da su da sun fito sai a hankali kawai.

KAROTA ta kama inyamuri da ya yi safar tabar wiwi katan 60 zuwa Kano

KAROTA ta baiwa ‘yan kasuwar katako awanni 44 da su bar bakin titi

Za mu fadada ayyukan mu zuwa wasu hukumomin gwamnati-KAROTA

Shehu Muhammad wani matukin Adai-daida sahu ne ya ce tunda sun zalincesu ai ba za su iya fitowa su yi aiki ba.

“Ta yaya za su fito bayan sun zaluncemu, sun hanamu cin abinci, kasan ba za ta yiwu ba.

“Idonmu idonsu, sai an yi kare jini biri jini da su, kuma sai Allah ya saka mana.

“Wannan cin zaline ake yi mana, kuma ai gwamnatin za ta kare ne ba yadda za su iya, haka za su tafi su kyalemu.

Duk wani kokari da mukayi domin jin ta bakin hukumar ta KAROTA lamarin ya ci tura, domin kuwa mun kasa samun shugaban hukumar da kuma kakakinsa ta wayar tarho.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending