Hausa

Bakuwar cuta ta hallaka mutum 4 da jikkata 284 a Kano

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Akalla mutane 4 ne suka rasa rayukansu, a Kano wasu 284 suka kwanta rai a hannun Allah a asibiti sakamakon kamuwa da wata bakuawar cuta da har yanzu ba a kai ga ganota ba.

Kano Focus ta ruwaito kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai ranar Talata a nan Kano.

Tsanyawa ya ce cutar da ake alakantawa da shan lemo na hoda da ake karawa ruwa ta fantsama a kanan hukumomi goma sha 13 da ke fadin jihar nan.

Haka kuma ya ce an sallami mutane 101 inda har yanzu 189 ke kwance a asibiti suna karbar magani.

Kwamishinan ya ce tun bayan bullar cutar kwanaki goma da suka wuce ma’aikatar ta kama lemukan da basu da kyau na kimanin miliyan 59.

Ya kuma ce tuni aka dauki samfurin wadanda suka kamu da cutar aka kuma aike da shi Birnin tarayya Abuja domin gwadawa.

Haka kuma ya ce sakamakon farko ya fito na binciken inda aka tabbatar cutar bata da alaka da ruwan makabarta da aka ce tun a baya

Click to comment

Trending