Connect with us

Hausa

Yadda zaman sulhu tsakanin Shekarau da Ganduje ya kasance a Gidan Gwamnatin Kano – Bello Sharada

Published

on

Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Malam Ibrahim Shekarau

Bello Muhammad Sharada

Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin riko sannan shugaban kwamitin shirya taron fitar da shugabannin jam’iyyar APC na kasa shi ne ya kafa kwamitin sasanci da daidaito a duk fadin Najeriya, saboda warware matsaloli na korafe-korafe  daga ‘ya’yan APC.

Ranar 14 ga watan Satumba 2021 Mai Mala ya rantsar da kwamitin mutum tara domin su yi masa aikin sasanta masu kuka da korafi. Mutanen da aka baiwa wannan aikin sune: Sanata Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan jihar Nassarawa, a matsayin shugaba. ‘ ‘ sauran ‘yan kwamitin sune; Barista Ali Sa’adu Birnin Kudu tsohon gwamnan jihar Jigawa da Alhaji Sulaiman Argungu, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kebbi  da tsohon gwamnan Enugu Sullivan Chime da tsohon kakakin majalisar tarayya Rt. Yakubu Dogara da tsohon gwamnan Binuwai George Akume da tsohuwar mataimakiyar gwamnan Lagos Oluranti Adebule, da  kwamishinan lafiya na jihar Cross River Beta Edu  sai Moses Adeyemi a matsayin sakatare.

Ranar 13 ga watan Oktoba 2021 Sanatoci guda uku na Kano karkashin jagorancin Sanata Mallam Ibrahim Shekarau da Sanata Barau I. Jibrin da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da ‘yan majalisar tarayya guda hudu, Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe da Hon. Nasir Abduwa Gabasawa da Hon. Haruna Isa Dederi da Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada suka hadu a gidan Sardaunan Kano na Abuja suka tattauna yadda za su gabatar da kokensu ga uwar jam’iyyar APC ta kasa a rubuce. Da asubahin fari Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya sanar da ficewarsa daga wannan shiri da tsari.

Ranar 14 ga watan Oktoba 2021  bayan sallar Juma’a wadannan shugabannin tare kuma da Alhaji Shehu Dalhatu na TBO suka je hedikwatar APC suka mika kukansu. Uwar jam’iyyar APC ta dankawa kwamitin sasanci na Sanata Abdullahi Adamu wannan korafi domin su yi aiki a kansa.

Ranar Litinin 29 ga watan Nuwamba 2021 wannan kwamitin ya fara aikinsa da matsalar Kano. Ya zo Kano, kuma duk wadannan shugabannin sun amince Sanata Mallam Ibrahim Shekarau shi ne zai yi magana a madadinsu. Haka kuwa aka yi.  Matsayin da suka dauka guda daya shi ne basu amince da yadda aka yi shugabancin APC ba a Kano a dukkan matakai. Bukatarsu kuma a rusa abin da aka yi, a sake sabon lale a baiwa kowane mai bukata damarsa.

Bayan sun gama zaman a Tahir Hotel ‘yan kwamitin sun bukaci bangaren Sanata Shekarau su zama cikin shiri domin za a yi zama gemu da gemu da gwamna Dokta Abdullah Umar Ganduje. Sun ce za su fara zauna wa da shi da mukarabbansa, sannan a hadu gaba daya. An samu haduwa a gidan gwamnatin Kano da tsakiyar dare na ranar Litinin har zuwa wayewar gari da asuba ranar Talata.

Bangaren Sanata Mallam Shekarau,  ya je zaman. A tawagarsa akwai Farfesa Hafizu Abubakar da Hon. Aliko Shuaibu Muktar da Dokta Umar Mustapha Musa da Injiniya Sarki Labaran da Barista Habibu Kankarofi. A wajen zaman gwamnan Kano, Dokta Ganduje yaje da mataimakinsa (Dr)  Nasir Yusuf Gawuna da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da shugaban masu rinjaye a majalisar kasa Hon. Alasan Ado Doguwa da kakakin majalisar dokoki na Kano  Rt Hon. Chidari da Alhaji Nasir Aliko Koki.

Sanata Abdullah Adamu ya yi bayani da farko na gabatar wa da rokon cewa alheri aka zo a kulla da kuma fatan a samu dacewa. Barista Ali Saadu Birnin Kudu ya tsefe abubuwa guda uku cewa akansu gaba daya za a gina wannan zama. Na farko an kasa samun haduwa da gwamna da Sanata Mallam Shekarau don a tattauna wanda ya kawo rashin fahimta. Na biyu kin saka  masu ruwa da tsaki cikin al’amuran da suka shafi jam’iyya. Na uku an gudanar da  shugabancin APC na kowane mataki babu jama’ar  da suka taka rawa kuma suna da gudunmawa da za su bayar.

Bayan wannan jawabin sai aka baiwa  gwamna Ganduje dama ya yi bayaninsa. Da farko ya baiwa  Mallam Shekarau hakuri, ya ce gidan gwamnatin Kano nasa ne baya bukatar iso tunda ga Kabiru Ibrahim Gaya ma ko yaushe yana shigowa. Mallam  Shekarau ya ce shi ba tsarinsa bane, sai ya yi tuntuba ko an kira shi an bashi dama zai zo abu.

Tashin farko gwamna Ganduje sai ya furta cewa ya yi alkawarin duk dan majalisar jiha dana tarayya da ‘yan majalisar dattijai kowa zai koma kan kujerarsa. Sannan na biyu kuma ya ce duk shugabannin jam’iyyar APC zabensu aka yi bisa doka kowa yana kan kujerarsa ba zai yi rawa ba. Amma za a yi sabbin nade-nade domin a shigo da wasu cikin gwamnati domin a bada kofar gyara kukan da aka yi. Anan ne Mallam Shekarau ya ce shi ba abin da ya kawo su ba kenan, baya maganar wata kujera, yana magana akan jam’iyya da kowa yake da hakki a cikinta. Abin da suke da bukata shi ne a rushe duk wani abu da aka yi a sake sabon lale a shigo da kowa.

Hon.Alasan Ado Doguwa yana cikin tawagar gwamna Ganduje, ya zo da wani fayil cike da sunayen mutane wadanda a cewarsa Ganduje ya basu mukamai a gwamnati su 526 daga bangaren Shekarau. Ya yi maganganu kausasa, na rashin ladabi ga Mallam Shekarau, yana cewa shi ana yin komai da shi haka sauran yan majalisar tarayya da dattijai. Wannan ya hassala ‘yan kwamiti kuma ya kawo hayaniya da ta hargitsa zaman. A haka kuma Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya goya masa baya.

Malam Shekarau ya bada amsa cewa shi ba ya maganar mukaman gwamnati, a gurinsa nadi da saukewa na gwamna ne ba ya ja, amma jam’iyyar APC ta ‘yan APC ce kuma suna da ruwa da tsaki da hakki. Ba a zo karshen magana ba, da kansa gwamna Ganduje ya ce a ajiye wannan maganar tattaunawa akan jam’iyya tunda komai yana gaban alkali. A jira hukuncin kotu, a daidai wannan lokacin kuma an fara kiran assalatu, Mallam Shekarau da tawagarsa suka fita Sallah, ba su dawo ba kowa ya tafi gidansa.

Bello Muhammad Sharada shi ne Jami’in kula da walwala na jam’iyyar APC na jihar Kano (State welfare officer) 6angaren Danzago.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

FG kickstarts construction of Emerging Technologies Institute in Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

As part of significant milestone in the Federal Government of Nigeria’s efforts to secure the socio-economic wellbeing of the future generation, as the ground was opened for commencement of construction of the Sustainable & Emerging Technologies Institute (SETI) under the aegis of the National Agency for Science and Engineering Infrastructure (NASENI), The Presidency.

 

KKANO FOCUS reports that the Executive Vice Chaiman/Chief Executive Officer (EVC/CEO) of NASENI, Mr. Khalil Suleiman Halilu during the Ground-breaking ceremony held at the Bayero University Kano (BUK) New Campus said the new institute sits on 30 hectares of the BUK land to be built, featuring state-of-the-art facilities, including innovation hubs devoted to Artificial Intelligence and other cutting-edge technologies, complemented by reliable power supply. “NASENI will fully build and equip and support the new Institute” said the EVC/CEO.

 

The future of socio-economic development for nations rests on human creativity, innovation and cooperation, Artificial intelligence, robotics amongst others.

 

Halilu said that the establishment of SETI in Nigeria is to rapidly respond to the waves of young people globally revolutionizing world economies with unprecedented emergence of socio-economic frontiers as by-products of innovations and ingenuities of these young minds.

 

“We in NASENI are firm believers in the potential of young Nigerians to be the prime catalysts of the type of transformation that Nigeria requires. And we will do everything within our powers to support them to fulfil this important responsibility”

 

“We are gathered here today to kickstart a project that will transform the lives and careers of future generations of young Nigerians. The Sustainable & Emerging Technologies Institute (SETI), located at the Bayero University Kano (BUK) by NASENI. This is very much in line with our operating principles; what we call our 3Cs: Collaboration, Creation, and Commercialization. These 3Cs are the principles that passionately drive us and guide the work that we do to ensure the industrialization of Nigeria in line with the Renewed Hope agenda of President Bola Ahmed Tinubu.”

 

SETI will produce innovators, technologists, entrepreneurs who will make their mark not just in Nigeria but around the world. “I’m eagerly looking forward to the day, not too long from now, when the Institute’s first set of beneficiaries will astonish the world with what they’re capable of accomplishing. These stories will put not just BUK on the global innovation map, but also Kano State and the entire Nigeria” said Halilu.

 

While carrying out the symbolic foundation laying ceremony of the institute as Special Guest of Honour, the Minister of Innovation, Science and Technology, Chief Uche Geoffrey Nnaji, described the project as not only laudable but NASENI’s another way of fast-tracking  the placing of Nigeria on the global map of innovation and industrialization. The minister called the project an “ace project” and a pointer to secure a veritable socio-economic development for the nation.

 

In his goodwill message, the Vice Chancellor of BUK, Professor Sagir Adamu Abbas described the new institute as a vehicle for bringing together the three critical tripods for economic and sustainable development for nations, that is, the government, academia and industry. He described the ground-breaking event as the beginning of Nigeria’s journey in pursuit of sustainable development, massive job creation opportunities for the youths, and that the BUK was delighted to be host to such laudable initiative and momentum.

 

There is also, in addition to SETI, a second NASENI project for BUK is an Agri-preneurship Training Hub, that will be equipped with modern greenhouses, and facilities for Soil-less Farming, and Tissue Culture; occupying 10 hectares of land at the Old Campus. These projects collectively represent what NASENI stands for, that is, building capacity, advancing industrialization, supporting economic growth and prosperity.

 

NASENI appreciates the Government and people of Kano State, and the Vice Chancellor, management and students of Bayero University Kano (BUK), for all the support. Special gratitude goes to the Honourable Minister of Innovation, Science and Technology, Chief Uche Geoffrey Nnaji, the Special Guest of Honour.

 

NASENI thanked members of the National Assembly for their support, especially the NASENI oversight Committees in both chambers. And of course, President Bola Ahmed Tinubu, who has given NASENI the opportunity to serve Nigeria through his unwavering demonstration of commitment to the success of the Agency.

Continue Reading

Hausa

Illar siyasantar da harkar tsaro da zaman lafiya a jihar Kano

Published

on

Jaafar Jaafar

 

Na jima ban ga tsantsar rashin kishi da cin amanar aiki da ya wuce ƙaryar da hukumar yansandan jihar Kano ta gilla ba saboda tsananin siyasantar da harkar tsaro da zaman lafiya da cigaban al’umma.

 

Babu wani rahoto na sirri kan wani mugun abu da ke faruwa a birni ko ƙauye wanda gwamna bai san shi ba. A wasu lokutan ma gwamnan ya kan riga jami’an tsaro samun wani rahoton sirrin. Duk wanda ya san yadda “special service directorate” (wadda ke karkashin ofishin gwamna) ke gudanar aiki, zai fahimci inda na dosa.

 

Kasashen da su ka ci gaba, ba sa wasa da duk bayanin da hukumar yansanda ta fitar. Domin su a kasashen su dansanda shi ya fi kowa adalci, shi ya sa zai wahala yansanda su tuhume ka da laifi ka ga alkali bai ɗaure ka ba.

 

Kafin harin Boko Haram na farko a Kano a ranar 20 ga Janairu 2012, akwai wani babban jami’in gwamnati da ya faɗa min cewa ƙasar Amurka na duba yiwuwar buɗe ƙaramin ofishin jakadanci (consulate) a Kano wanda zai riƙa ba da visa da gudanar da wasu shirye-shirye a jihar Kano. Kwatsam sai a ka kawo harin bam. Daga nan maganar ta mutu murus. A tunaninka in da a ce Amurka za ta sake duba yiwuwar bude consulate a Kano, sai ta ji sanarwar hukumar yansanda ta fitar, me ka ke tunanin za ta yi? Za ta fasa ne!

 

Haka fa muna ji muna gani British Council ta rufe cibiyarta da ke Kano. Wannan cibiya ta taimaka gaya wajen sa wa matasa sha’awar karatu, kuma ta samar da damarmaki na karatu da tafiye-tafiyen nazari kasashe ga mutane da dama. Ita ma wannan cibiya a dalilin rashin tsaro yanzu ta tattara inata-inata ta tafi.

 

Ta fuskar kasuwanci, watakil wannan sanarwar karyar da hukumar yansanda ta fitar ta sa masu son zuba jari daga wasu wurare (foreign investors) su fasa. Haka zalika, watakil wannan asarar ta sa masu zuwa fatauci kasuwannin Kano su ja jiki. Ka ga sun jawo wa yan kasuwa da jihar asara.

 

Tarihi ya nuna tun kafin Kano ta yi shuhura a harkar kasuwanci, Katsina ita ce cibiyar kasuwanci a kasar Hausa. Babban abin da ya sa Katsina ta koma baya shi ne yaƙe-yaƙe da ta sha fama da shi, musanman a ƙarni na 18.

 

Kira na ga gwamnatin jihar Kano shi ne kada ta bar wannan cin amana ya wuce ba ta yi wa tufkar hanci ba. Kamata ya yi gwamna da kan shi ya kira gagarumin taron zantawa da yanjarida wanda ya ƙunshi manyan gidajen jaridu na ƙasa da waje domin fayyace wa duniya zancen. Idan ma da yiwuwar kai yandansan kotu, to yakamata gwamnati kada ta yi ƙasa a gwiwa.

 

Allah Ya zaunar da mu lafiya.

Jaafar Jaafar, shi ne mawallafim jaridar Daily Nigerian, ya kuma wallafa wannan rubutun ne a shafinsa na Facebook. 

 

Continue Reading

Hausa

EFCC arraigns one for N108 million fertiliser fraud in Kano

Published

on

Sanusi Hashim

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

The Kano Zonal Directorate of the Economic and Financial Crimes Commission, EFCC, has arraigned one Sanusi Hashim for allegedly misappropriating and converting to his personal use, the sum of 108 million Naira. 

 

KANO FOCUS reports that Hashim was arraigned before Justice Kabiru Dabo of the Kaduna State High Court sitting in Zaria on a one -count charge of misappropriation contrary to Section 293 and punishable under section 294 of the Penal Code.

 

He was alleged to have collected a total sum of 108 million Naira from one Ahmad Mohammad Liman and Basiru Mohammad for the supply of fertilizer but instead misappropriated and diverted the money for his personal use.

 

The lone-count charge reads ‘’That you Sanusi Hashim sometime in April 2020 under the jurisdiction of the Kaduna State High Court dishonestly misappropriated and converted to your own use, the sum One Hundred and Eight Million Naira (N108,000,000) property of one Ahmad Mohammad Liman and Basiru Mohammad for the supply of fertilizer from Indorama Eleme Fertilizer and Chemicals and you thereby committed an offence under Section 293 and punishable under Section 294 of the Penal Code’’.

 

The defendant pleaded not guilty when the charge was read to him.

 

Counsel to the prosecution, Bright C. Ogbonna prayed the court for a trial date in view of the defendant’s plea.

 

Consequently, Justice Dabo remanded the defendant in a Correctional Centre and adjourned the matter to February 10, 2025 for hearing of bail application.

Continue Reading

Trending