Hausa
#Ranar Hausa: Yunkurin Hausantar da Kimiyya da Fasaha
Farfesa Faruk Sarkinfada
Hakika ilimin kimiyya da fasaha baiwa ce ta Ubangiji da kebanci wasu daga cikin bayinsa da ita, wanda su kuma su ke da hakkin sanar da wanda Ubangiji ya so. Amma kuma amfaninsa da tasirinsa da yin aiki da shi ya shafi kowa da komai. Don haka ba sai mutum ya karanci ilimin kimiyya da fasaha a makaranta ya cancanta ya san shi ko ya yi aiki da shi ba. Ma fi saukin sanar da ilimin kimiyya da fasaha ga al’uma shi ne samar da shi da koyar da shi cikin yarensu, ta yadda zai yi saukin fahimta garesu da kuma al’umomi masu zuwa bayansu. Wannan zai kau da kalubalen gwagwarmayar koyon harshe turanci ko faransanci da sauran harsunan da ke dauke da wannan ilimi na kimiyya da fasaha kafin saninsa.
A wani bangare kuma, samar da ilimin kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa zai taimaka wajen habaka ci gaban al’uma da kasa baki daya kamar yadda ya tabbata a sauran kasashen da suka ci gaba kamar su China da Germany, ta hanyar koyar da ilimin kimiyya da fasaha a harshen uwa da suke yi a kasashensu. A Nigeria, tuni a na ta yunkurin samar da ilimin kimiyya da fasaha a harshen Hausa ta fannoni daban-daban tare da kiraye-kirayen samar da dokar da za ta bayar da damar koyar da darussan Kimiyya da Fasaha cikin harsunan kasa a Nigeria a matakin gwamnatin tarayya da jihohi. Hakika zai fi sauki a horar da malaman da za su koyar da yara ilimin Kimiyya da Fasaha cikin Hausa fiye da koya wa dalibai harshen turanci sannan su koyi wannan ilimi.
Hakika harshen Hausa yana da nagarta da bunkasa a nahiyar Afrika da wasu sassa na duniya, ta yadda za a iya samar da dukkan fannonin ilimi a cikinsa, duba da yadda ya shahara a duniya wajen yin amfani da shi a kafafun yada labarai masu yawa a fadin duniya. Bugu da kari Allah ya albarkaci al’umar Hausawa da kwararru a dukkan bangarori na ilimin kimiyya da fasaha ta yadda babu fannin ilimin da ba za a iya samar da shi cikin harsen Hausa ba a yanzu. Don haka ya zamo kalubale ga Hausawa masana ilimin kimiyya da fasaha su kara ba da himma a kan samar da wanna ilimi cikin harshen Hausa.
A shekarun baya, masana da dama sun wallafa littattafai da kasidu a wasu fannonin kimiyya da fasaha a cikin harshen Hausa. Misali, Malam Abubakar Imam da wani Bature mai suna Rupert East sun wallafa littafin “Ikon Allah” mai dauke da labaran halittu iri-iri na Duniya. Farfesa Hambali Junju ya rubuta littafin ‘Garkuwar Hausa da tafarkin ci gaba’ mai dauke da fassarar wasu kalmomi da suka shafi kimiyya da fasaha cikin Hausa. Farfesa Muhammad Kabir ya rubuta littafin ‘Aikin Likita’, yayin da marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa ya rubuta littafin ‘Kimiyyar Sararin Samaniya’. A wannan zamani kuma, Jami’o’in Nigeria da na wajen Nigeria sun fara samar da fassarar littattafan kimiyya da fasaha kamar Lissafi, Physics, Chemistry, Biology, Kimiyyar Computer cikin Hausa. A wani bangare kuma daidaikin mutane su na rubuce-rubucen littattafa da kasidu, kai har da wakoki da su ka shafi kimiyya da fasaha a cikin Hausa. Misali, na wallaf littafin “Wani Abu a Kan Matar Sarki” a kan Ilimin ‘Yan Halittu, watau microbes, da littafin “Zaton Wuta a Makera” a kan cutar yoyon fitsari da yadda za a magance aukuwarta. Na kuma wallafa tare da rera wakoki a kan cimaka (nutrition) da cutar Korona a cikin Hausa. Har wa yau akwai wasu masana da su ke koyar da darussan Kimiyya da Fasaha a shafukan sada zumunta na Facebook da YouTube da dai sauransu. Akwai kuma cibiya mai zaman kanta ta Engausa Global Tech Hub da ta himmatu wajen koya wa matasa fasahar kere-kere da sana’o’i na zamani a cikin Hausa.
To amma akwai bukatar kara zaburar da masana su samarda ingantattun rubuce rubuce, musammam littattafa da sauran kayayyakin koyo da koyarwa cikin harshen Hausa, wadanda su ne muhimman kayan aikin dabbaka dokar koyar da darussan kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa.
Tuni mun assasa wata Gidauniyar Bunkasa Kimiyya da Fasaha cikin Hausa mai zaman kanta da manufofi kamar haka:
1. Gamayyar kwararru a fagen kimiyya da fasaha da kuma masana harshe Hausa don samar da ingantaccen ilimin kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa, don karin yaduwarsa da tasirinsa ga ci gaban al’uma.
2. Alakanta al’adu da fasahar Hausawa da kimiyya da fasahar zamani, don bunkasa tasirinsu ga ci gaban al’uma.
3. Wallafa kasidu da mujallu da muhimman labarai da suka shafi ilimin kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa domin ilmintarwa da wayar da kan al’uma bisa abubuwan da suka shafi kimiyya da fasahar zamani.
4. Bada gudunmawa da samar da manhajoji na koyo da koyarwa da bincike kan fannoni daban-daban na kimiyya da fasaha a cikin harshen Hausa, domin samar da kwararrun masana kimiyya daga tushe a al’umar Hausawa.
5. Amfani da kafafen sadarwa na zamani, don tabbatar da tsarin koyo da koyar a kimiyya da fasaha cikin al’umar Hausawa.
6. Samar da mahanga / shawarwari don nusarwa ga mahukunta da masu ruwa da tsaki a kan kafa dokoki da kudure-kudure bisa aiwatar da ilimin kimiyya da fasaha a harshen Hausa
a dukkan matakan ilimi.
A yayin da masana cikin Jami’o’i da sauran manyan makarantu su ke aikin samar da ilimin Kimiyya da fasaha cikin Hausa, wannan cibiya za ta zamanto magama mai tattaro dukkan masu ruwa da tsaki kamar gwamnati, masarautu, shuwagabannin addini, mawadata, kungiyoyin marubuta da bubkasa al’adu, ‘yan jarida, kungiyoyin ci gaban al’uma da dai sauransu, wajen samarwa da yada ingantaccen ilimin Kimiyya da Fasaha da kuma amfaninsa ga ci gaban al’uma.
Abin tambaya da jan hankali a nan shine, yaushe za a fara koyar da dalibai ilimin kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa a kasar Hausa? Ta ina za a fara? Kuma waye zai fara? Idan ba mu taka rawar kidan mu ba, to fa wasu za su taka mana.
Allah ya yi mana jagora.
Farfesa Faruk Sarkinfada
faruksarkinfada@gmail.com
26/08/2024
Hausa
Mutane 18,000 sun amfana da aikin ido kyauta ta Gidauniyar Mangal a Katsina
Kimanin marasa lafiya masu rauni 18,000 da ke fama da cututtukan ido daban-daban a jihar Katsina sun amfana da ayyukan kulawar ido da tiyata kyauta da Gidauniyar Mangal ta dauki nauyi tun bayan kafuwarta a shekarar 2016.
Wani mamba na kwamitin amintattu (Board of Trustees) na gidauniyar, Malam Hussaini Kabir, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin kaddamar da aikin tiyatar ido na zangon karshe na shekarar 2025 a Cibiyar Ido ta Katsina.
Kabir ya bayyana cewa kimanin mutane 7,000 ne suka amfana a shekarar 2025 kadai, daga sassan jihar Katsina, jihohin makwabta, har ma da wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar.

A cewarsa, gidauniyar ta fara tantance wadanda za su amfana kimanin makonni biyu da suka gabata, inda marasa lafiya da dama suka samu magunguna kyauta da tabarau na likita.
Kabir ya kara da cewa wadanda ke bukatar tiyata an dauki nauyin dukkan zaman asibitinsu gaba daya, yana mai cewa kimanin marasa lafiya 2,000 aka tantance a yayin aikin zangon karshe da ake ci gaba da yi.

Ya sake jaddada kudirin gidauniyar na inganta samun kulawar lafiya, yana bayyana shirin a matsayin wani bangare na nauyin alhakin zamantakewar kamfanoni (corporate social responsibility).
“Manufarmu ita ce tallafa wa kokarin gwamnati tare da rage nauyin kudin kula da lafiya ga mafi rauni, musamman wadanda ke fama da matsalar biyan bukatun rayuwa,” in ji shi.

Wani likitan ido a cibiyar, Dokta Ahmad Hamza, ya bayyana cewa an gano marasa lafiya da dama na fama da cutar idon toka (cataract) da glaucoma, cututtuka da galibi ke bukatar tiyata.
Ya jaddada muhimmancin duba ido akai-akai, yana mai cewa gano cuta da wuri na taimakawa wajen hana asarar gani ta dindindin da cututtukan ido masu zuwa a boye ke haifarwa, kamar glaucoma, cataract da lalacewar macula (macular degeneration).

Daya daga cikin wadanda suka amfana, Malam Yusufa Usman, ya ce ya shafe sama da shekaru biyu yana fama da matsalar gani amma ba shi da ikon biyan kudin tiyata.
“Tsawon shekaru biyu ban iya gani sosai ba, amma yau na yi tiyata kuma ina da fatan ganina zai dawo.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya saka wa Gidauniyar Mangal da alheri bisa wannan kyakkyawan aiki.
“Ina fatan sauran masu kudi za su yi koyi da wannan abin a yaba,” in ji Usman.

Wata mai amfana, Aisha Muntari daga kauyen Bakuru, ta bayyana kwarewarta yayin da take jiran a kai ta dakin tiyata.
Muntari ta ce ta kamu da matsalar ido kimanin shekara guda da ta wuce kuma ta kusa yanke tsammani kafin ta samu labarin shigar gidauniyar, tana mai bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba ganinta zai dawo.
Hausa
FG kickstarts construction of Emerging Technologies Institute in Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
As part of significant milestone in the Federal Government of Nigeria’s efforts to secure the socio-economic wellbeing of the future generation, as the ground was opened for commencement of construction of the Sustainable & Emerging Technologies Institute (SETI) under the aegis of the National Agency for Science and Engineering Infrastructure (NASENI), The Presidency.
KKANO FOCUS reports that the Executive Vice Chaiman/Chief Executive Officer (EVC/CEO) of NASENI, Mr. Khalil Suleiman Halilu during the Ground-breaking ceremony held at the Bayero University Kano (BUK) New Campus said the new institute sits on 30 hectares of the BUK land to be built, featuring state-of-the-art facilities, including innovation hubs devoted to Artificial Intelligence and other cutting-edge technologies, complemented by reliable power supply. “NASENI will fully build and equip and support the new Institute” said the EVC/CEO.
The future of socio-economic development for nations rests on human creativity, innovation and cooperation, Artificial intelligence, robotics amongst others.
Halilu said that the establishment of SETI in Nigeria is to rapidly respond to the waves of young people globally revolutionizing world economies with unprecedented emergence of socio-economic frontiers as by-products of innovations and ingenuities of these young minds.
“We in NASENI are firm believers in the potential of young Nigerians to be the prime catalysts of the type of transformation that Nigeria requires. And we will do everything within our powers to support them to fulfil this important responsibility”
“We are gathered here today to kickstart a project that will transform the lives and careers of future generations of young Nigerians. The Sustainable & Emerging Technologies Institute (SETI), located at the Bayero University Kano (BUK) by NASENI. This is very much in line with our operating principles; what we call our 3Cs: Collaboration, Creation, and Commercialization. These 3Cs are the principles that passionately drive us and guide the work that we do to ensure the industrialization of Nigeria in line with the Renewed Hope agenda of President Bola Ahmed Tinubu.”
SETI will produce innovators, technologists, entrepreneurs who will make their mark not just in Nigeria but around the world. “I’m eagerly looking forward to the day, not too long from now, when the Institute’s first set of beneficiaries will astonish the world with what they’re capable of accomplishing. These stories will put not just BUK on the global innovation map, but also Kano State and the entire Nigeria” said Halilu.
While carrying out the symbolic foundation laying ceremony of the institute as Special Guest of Honour, the Minister of Innovation, Science and Technology, Chief Uche Geoffrey Nnaji, described the project as not only laudable but NASENI’s another way of fast-tracking the placing of Nigeria on the global map of innovation and industrialization. The minister called the project an “ace project” and a pointer to secure a veritable socio-economic development for the nation.
In his goodwill message, the Vice Chancellor of BUK, Professor Sagir Adamu Abbas described the new institute as a vehicle for bringing together the three critical tripods for economic and sustainable development for nations, that is, the government, academia and industry. He described the ground-breaking event as the beginning of Nigeria’s journey in pursuit of sustainable development, massive job creation opportunities for the youths, and that the BUK was delighted to be host to such laudable initiative and momentum.
There is also, in addition to SETI, a second NASENI project for BUK is an Agri-preneurship Training Hub, that will be equipped with modern greenhouses, and facilities for Soil-less Farming, and Tissue Culture; occupying 10 hectares of land at the Old Campus. These projects collectively represent what NASENI stands for, that is, building capacity, advancing industrialization, supporting economic growth and prosperity.
NASENI appreciates the Government and people of Kano State, and the Vice Chancellor, management and students of Bayero University Kano (BUK), for all the support. Special gratitude goes to the Honourable Minister of Innovation, Science and Technology, Chief Uche Geoffrey Nnaji, the Special Guest of Honour.
NASENI thanked members of the National Assembly for their support, especially the NASENI oversight Committees in both chambers. And of course, President Bola Ahmed Tinubu, who has given NASENI the opportunity to serve Nigeria through his unwavering demonstration of commitment to the success of the Agency.
Hausa
Illar siyasantar da harkar tsaro da zaman lafiya a jihar Kano
Jaafar Jaafar
Na jima ban ga tsantsar rashin kishi da cin amanar aiki da ya wuce ƙaryar da hukumar yansandan jihar Kano ta gilla ba saboda tsananin siyasantar da harkar tsaro da zaman lafiya da cigaban al’umma.
Babu wani rahoto na sirri kan wani mugun abu da ke faruwa a birni ko ƙauye wanda gwamna bai san shi ba. A wasu lokutan ma gwamnan ya kan riga jami’an tsaro samun wani rahoton sirrin. Duk wanda ya san yadda “special service directorate” (wadda ke karkashin ofishin gwamna) ke gudanar aiki, zai fahimci inda na dosa.
Kasashen da su ka ci gaba, ba sa wasa da duk bayanin da hukumar yansanda ta fitar. Domin su a kasashen su dansanda shi ya fi kowa adalci, shi ya sa zai wahala yansanda su tuhume ka da laifi ka ga alkali bai ɗaure ka ba.
Kafin harin Boko Haram na farko a Kano a ranar 20 ga Janairu 2012, akwai wani babban jami’in gwamnati da ya faɗa min cewa ƙasar Amurka na duba yiwuwar buɗe ƙaramin ofishin jakadanci (consulate) a Kano wanda zai riƙa ba da visa da gudanar da wasu shirye-shirye a jihar Kano. Kwatsam sai a ka kawo harin bam. Daga nan maganar ta mutu murus. A tunaninka in da a ce Amurka za ta sake duba yiwuwar bude consulate a Kano, sai ta ji sanarwar hukumar yansanda ta fitar, me ka ke tunanin za ta yi? Za ta fasa ne!
Haka fa muna ji muna gani British Council ta rufe cibiyarta da ke Kano. Wannan cibiya ta taimaka gaya wajen sa wa matasa sha’awar karatu, kuma ta samar da damarmaki na karatu da tafiye-tafiyen nazari kasashe ga mutane da dama. Ita ma wannan cibiya a dalilin rashin tsaro yanzu ta tattara inata-inata ta tafi.
Ta fuskar kasuwanci, watakil wannan sanarwar karyar da hukumar yansanda ta fitar ta sa masu son zuba jari daga wasu wurare (foreign investors) su fasa. Haka zalika, watakil wannan asarar ta sa masu zuwa fatauci kasuwannin Kano su ja jiki. Ka ga sun jawo wa yan kasuwa da jihar asara.
Tarihi ya nuna tun kafin Kano ta yi shuhura a harkar kasuwanci, Katsina ita ce cibiyar kasuwanci a kasar Hausa. Babban abin da ya sa Katsina ta koma baya shi ne yaƙe-yaƙe da ta sha fama da shi, musanman a ƙarni na 18.
Kira na ga gwamnatin jihar Kano shi ne kada ta bar wannan cin amana ya wuce ba ta yi wa tufkar hanci ba. Kamata ya yi gwamna da kan shi ya kira gagarumin taron zantawa da yanjarida wanda ya ƙunshi manyan gidajen jaridu na ƙasa da waje domin fayyace wa duniya zancen. Idan ma da yiwuwar kai yandansan kotu, to yakamata gwamnati kada ta yi ƙasa a gwiwa.
Allah Ya zaunar da mu lafiya.
Jaafar Jaafar, shi ne mawallafim jaridar Daily Nigerian, ya kuma wallafa wannan rubutun ne a shafinsa na Facebook.
