KANUN LABARAI
NDLEA na son batawa dan takararmu suna nen kawai-al’ummar Babban Giji
Zulaiha Danjuma
Matasa a uguwar Hausawa Babban Giji da ke karamar hukumar Tarauni sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da soke dan takarar kansilansu da aka yi bayan gwaji ya nuna yana ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Kano Focus ta ruwaito hukumar NDLEA ta ayyana sunan Mubarak Shua’ibu Yakubu da ke takarar Kansila a mazabar Babban Giji da cewar yana daya daga cikin wadanda sakamakonsu ya nuna suna shan kwaya.
Matasan dai sun gudanar da zanga-zangarne a jiya Litinin.
Ya yin zanga-zangar an ga maza da mata dauke da rubutu iri-iri da ke nuna adawa da sauya wanda suke so din.

Ado Sharu gudane cikin masu zanga-zangar ya ce suna adawa da matakin na hukumar NDLEA, kuma ya ce wanna anyi ne kawai domin a batawa dan takararsu suna.
“Mun fitone domin mu nuna bakincikinmu kan batancin da aka yiwa dan takarar mu Mubarak da aka kakaba masa shan kwaya haka kawai.
“ Mu kuma sanin da muka yiwa wannan bawan Allah ko sigari ba ya sha.
“Idan ba a gaya mana yadda aka sameshi da shaye-shaye ba mu mazabarmu ta babban giji mun hakura da zaben.
Haka zalika ita ma wata mata Hadiza Abbas da ta kasance cikin masu zanga-zangar ta ce a idon su aka haifeshi don haka sun tabbata baya shaye-shaye.
“A idon mu aka haifeshi, a idon mu ya girman, baya ko cin goro ballantana sigari, amma haka aka lika masa abinda baya yi.
Da yake jawabi dan takarar da ake zargin akansa Mubarak Shu’aib ya ce ya dauki lamarin a matsayin kaddara.
“Gaskiya lokacin da naji na yi mamaki sosai, ban taba tsintar kaina a irin wannan yanayi na shaye-shayeba.
“Ban taba shan ko sigari ba gidannmu ko mutun daya baya shan taba bamu da yan shaye-shaye.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
