KANUN LABARAI
Tilastawa ma’aikatan Kano rijista da APC ta’addancin siyasane-PDP
Aminu Abdullahi
Jam’iyyar PDP ta ce matakin da shugabannin jam’iyyar APC suka dauka na tilastawa ma’aikatan gwamnati yin rijita da jam’iyar a jihar Kano taaaddancin siyasane.
Kano Focus ta ruwaito sakataren yada labaran jam’iyar na kasa Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata.
Ya ce wannan ya nuna karara yadda jama’a a Kano ke ci gaba da kin amincewa da jam’iyyar kuma suke juya mata goya mata baya.
Ya ce abin takaicine yadda shugaban jam’iyar APC na jihar Kano Abdulahi Abbas, ya yiwa ma’aikatan gwamnati da sauran al’umma barazana da su shiga jam’iyyarsu kosu rasa duk wata fa’ida da dama daga gwamnatin jihar.

Ya kara da cewa a gaskiyance APC batada wani tasiri maimakon haka ta koma tilastawa ‘yan Najeriya a wuraren da ake ganin sun fi karfi kamar jihohin Kano, Kaduna, da kuma jihar Katsina.
Ya ce wannan na nuna cewa APC tuni ta mutu a jihohin sakamakon cin amanarsu a cikin shekaru shida da suka gabata.
” Jam’iyyar mu ta yi tir da barazanar da APC ta yi a matsayin abinda ya saba da kundin tsarin mulkin kasa kuma ta’addancin siyasa ne.
“Shugabannin APC suna bukatar a fadakar da su cewa irin wannan barazanar, cin zarafi ne ga ‘yancin al’ummar kasa da kundin tsarin mulki ya tanada kuma wannan na iya haifar da mummunan rikici a cikin al’umma, tare da lalata tsarin demokradiyyar kasar mu,” a cewar sa.
Ya kuma ce yana da kyau a sanar da APC cewa yayin da suke kokarin tilasta mutane da kirkirar alkaluma, miliyoyin ‘yan Najeriya nata tururuwa zuwa ofisoshin jam’iyar PDP a jihohin kasar domin yin rijista da jam’iyar.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
