Connect with us

KANUN LABARAI

Yadda muka samu silin gashin manzan Allah a Kano-Sheik Karibullah

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Shugaban darikar kadiryya na Afrika Sheik Karibubullah Sheik Nasir Kabara ya ce Allah ya  albarkanci su da samun silin gashin kan Mamzon Allah (S.A.W) a gidan Kadiryya na Kano.

Kano Focus ta ruwito sheik Karibullah ya yi wannan bayanine a hirar da ya yi da gidan rediyon Faransa a nan Kano.

Ya ce sun samu gashin daga wurin wadanda suka gajeshi tun iyaye da kakanni.

Malam Kabara ya ce asalin gashin ya fito ne daga wani sahabi da ake cewa sayyadina Rifa’atu, wanda yana daga cikin wadanda manzan Allah ya baiwa gashinsa lokacin da aka yi masa aski.

“Allah ya girmamamu  da samun wannan albarka ta wannan abu na jikin manzan (SAW) shi ne gashinsa.

“Kamar yadda yazo a cikin sahihan littafai na musulunci, a cikin sahihul Buhari, Annabi (SAW) lokacin da yayi hajjin bankwana anyi masa aski, an aske gashin kansa baki daya.

“Ya kuma dauki gashinnan ya rarrabawa sahabban sa ya bawa wasu da yawa, wasu guda goma wasu ashirin, wasu akwai wanda ya bashima sili daya.

“To shi gashin Manzan Allah kamar yadda ya ingata yana da wani abin mamaki da yake tattare da shi, shi ne baya balbalcewa, baya lalacewa indai an sameshi to indai shi ne ko shekara nawa zai yi baya lalacewa.

“Wadanda suke da riko da gadon wadannan kaya sunann da abinsu, indan kayi sa’a suna iya sammaka.

“To mu munyi sa’a wanda yazama sun gaji wannan abin a gidan su, ya girmamamu da sili daya na wannan gashin yanzu haka yana tare da mu a nan gidan Kadiriyya.

“Wannan gashi mun sameshi tare da cikakken tarihinsa, ya gada daga mahaifinsa wane, shi ma daga mahaifinsa wane, har zuwa gurin sahabin da manzon Allah ya dankamasa, shi ne sayyadina Rifa’atu Rabiyyallahu anhu.

“Sanadin namu yana nan a rubuce da sa hannu da izini, shima sai da ya nemi izini masu hakki akan abun sanna ya bamu.”a cewar sa.

Malam Kabara ya ci gaba da cewa bayan da aka danka musu gashi sai da aka basu sharadin cewar za su kula da shi fiye da dukiyar su da komai na su.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending