Connect with us

KANUN LABARAI

NMA ta yi korafi kan karancin likitoci a Kano

Published

on

Nasiru Yusuf

Kungiyar Likitoci ta kasa reshen jihar Kano ta koka kan karancin Likitoci a jihar Kano.

 

Kano Focus ta ruwaito shugaban kungiyar Usman Ali ne ya yi wannan korafin lokacin da yake ganawa da manema labarai a yayin bikin makon likitoci na bana (2020) da ake yi a birnin Kano.

Shugaban ya koka kan wawan gi6in da ake da shi na likitocin dake kula da marasa lafiya a jihar Kano.

Ya ce  rashin likitocin muninsa ya zarta wanda ake da shi a matakin kasa, inda likita daya yake kula da mutum dubu biyar (1-5,000).

Da yake fashin baki kan yawan likitocin dake Kano, Dakta Usman Ali ya ce, Asibitin Malam (AKTH) mallakar Gwamnatin Tarayya yana da likitoci 623 ya yin da Asibitin Kashi (National Orthopaedic Hospital) ya ke da likitoci 70.

Ya cigaba da cewa asibitoci mallakar Gwamnatin jihar Kano na da likitoci 568 sai kuma wasu ‘yan tsiraru dake aiki a Asibitin Jami’ar Bayero da na Yusuf Maitama sule.

Dakta Usman Ali ya kuma roki gwamnati da ta duba yiwuwar kara alawus din da ake ba wa likitoci da sauran ma’aikatan lafiya na hadarin kamuwa da cututtuka (hazard allowance) wanda ya ce a halin yanzu ana biyan likitoci Naira dubu biyar ne kacal a kowanne wata.

A lokacin bikin, Kungiyar ta karrama darakta a Hukumar dake kula da Asibitocin Kula da Lafiya a matakin farko (KSPHCMB) Dakta Imam Wada Bello saboda jajircewarsa.

Haka kuma kungiyar ta kai tallafin kayan masarufi Gidan marasa lafiya dake Tudun Maliki (Torrey Home).

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending