Connect with us

KANUN LABARAI

Zanga-zanga: Al’ummar Igbo sun nemi afuwar jama’ar Kano

Published

on

Mukhtar Yahya Usman

Al’ummar Igbo mazauna Kano sun nemi afuwar gwamnatin Kano da sauran jama’a kan rikicin da ya barke da ya jayo assarar dukiya mai yawa yayin zanga-zangar #EndSARS a kwanakin nan.

Kano Focus ta ruwaito shugaban Al’ummar Igbo a nan Kano Boniface Igbekwe ne ya sanar da hakan  yayin da yake zantawa da maneman labarai a gefen taron neman zaman lafiya da lalubo bakin zaren da karamar hukumar Fagge ta shirya ranar Asabar a nan Kano.

Mista Igbekwe ya ce irin barnanar da matasan suka yi a Sabon Gari abin Allah wadai ne ba kuma dabi’un da aka san jama’ar Igbo da shi ba ne.

Ya kara da cewa ko kadan jama’ar Igbo basu goyi bayan al’amarin ba inda ya bayyana ayyukan nasu da ta’addanci.

“Masu zanga-zangar sun je har gidana suna jifa da duwatsu saboda naki goya musu baya, saboda ba zan goyi bayan ta’addanci ba.

” Tun da farko sai da na roke su kada suyi zanga-zangar, saboda Kano garin zaman lafiya ne, a lokaci guda kuma ba kanwar lasa ba ne idan aka tsokane su” A cewar sa.

Shugaban Al’ummar Igbo ya Kuma kirayi jami’an tsaro da su dauki dukkanin matakin da ya da ce ga masu kunnen kashi da suka bijierwa doka da oda.

Ya Kuma yabawa gwamnatin jihar Kano kan yadda ta shawo kan al’amarin cikin hanzari.

Da yake nasa jawabin kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Abu Sani ya bukaci shugabanin kabilu da suke jihar nan da su ja kunnenan mabiyansu kan duk wani aiki da ka iya jawo rashin zaman lafiya a jihar Kano.

A cewar sa rundunar ‘yan sanda ba za ta lamunci ayyukan rashin da’a ba da zai hana jama’ar Kano gudanar da rayuwarsu Kamar yadda ya kamata.

Da yake nasa jawabin shugaban karamar hukumar Fagge Ibrahim Shehi ya ce an shirya taron ne domin a tattauna matsalar tsaro da Kuma yadda za a lalubo bakin zaren.

Ya ce  wann taro zai yi kokari wajen lalubo hanyoyin magance matsalar yadda irin wannan al’amari ba zai sake faruwa ba a yankin dama jihar Kano baki daya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending