KANUN LABARAI
Dalilan da ya sa marasa lafiya a Kano suka zabi zuwa ‘kyamis’ maimakon asibiti
Aminu Abdullahi
Dayawa daga cikin marasa lafiya a Kano musamman ma masu karamin karafi sun zabi su je kyamis domin duba lafiyarsu maimkon asibti.
Wani bincike da jaridar Kano Focus ta yi ta gano yadda kyamis ke cika da marasa lafiya da ke neman aduba lafiyar su kamar a asibiti.
Muhammad Tukur Ibrahim da ke Gwauron Dutse a nan Kano marar lafiya ne da aka iske akan layin jiran mai kyamis, ya ce ba zai iya zuwa asibiti domin a duba shi ba.
Ya ce akwai dogon layi a asibiti, da komai ma ka iya samun mutum kafin azo kansa ga babu kulawar da ta da ce.
“Idan na kamu da rashin lafiya kyamis nake garzayawa, nan ne da naje za a yi min allura abani yan kwayoyi na dawo gida.
“Indai na je asibiti to sai idan lamarin ya ta’azzara naji alamar kamar zan mutu” acewar sa.
“Ma’aikatan lafiya a asibiti basa kula marasa lafiya yadda ya kamata, ga kyara da tsangwama.
“Hakan ta sanya marasa lafiya da dama kauracewa zuwa asibiti domin ko sunje da bakin cikin ma’aikatan za su dawo” ya kara da cewa.
Ita kuwa wata marar lafiyar da itama aka iske a layin Kyamis Hajara Isma’il dake Unguwar Mariri ta talauci ne kawai ke sata zuwa kyamis.
Ta ce komai tsananin cuta gwara taje kyamis tun da ko taje asibitin ma bata da kudim ganin likita.
Ta kara da cewa mafiya yawan likotoci da malaman jinya a sibitoci basu da kirki basa ganin darajar mutum ko kadan.
“Idan kaje asibiti za kaga yadda suke dakawa marasa lafiya tsawa, su kuma wulakantasu yadda suka ga dama, hakan ta sanya gwara muje kyamis.” Ta ce.
Shi ma wani mazaunin Gwammaja a nan Kano Khalipha Yunusa ya ce ma’aikatan jinya a asibiti sun wulakantashi yadda ba a zato akan bin layin asibiti.
Ya ce yadda ma’aikatan lafiya ke yiwa marasa lafiya a sibiti abin kare ba zai ci ba.
A don hakan ne ma ya ce gwanda ya yi tafiyar sa kyamis ya bada yan kudi tsirari a duba shi.
Ko akwai matsala karbar magani a kyamis
Wani dan jarida a nan Kano Abdulkaren Muhammad da ke unguwar Tukuntawa ya ce kiris ya rage ya rasa idanunsa sakamakon maganin da aka bashi a kyamis.
Ya ce lokacin da ya fara jin ciwon ido sai ya tafi kyamis domin a duba shi aka kuma bashi wani magani da ya yi amfani da shi sama da mako guda.
Sai da a cewar sa da yake ba likita ne ya auna shi ya bashi maganin ba kadan ya rage ya rasa idon nasa baki daya.
“Da naje Kyamis na yi masa dukkanin bayanin abin da ke damuna sannan ya dauko magani ya bane ba tare da anyi gwaji ba da hakan y kusan makantar da ni” ya ce.
Nasir Mustapha Salanta, shi ma ya sahida irin hadarin da ya fada game da karbar magani a kyamis.
Ya ce ko kadan ba zai kara zuwa kyamis karbar magani ba domin kuwa hakan ya kusan salwantar da rayuwar sa.
A cewarsa komai dogon layi gwanda ya je asibiti likita ya dubashi ya bshi magani.
Dalilan da yasa muke bada magani a kyamis
Sai dai a tattaunawar jaridar Kano Focus da wasu masu kyamis a nan Kano kan dalilian da ya sanya suke duba marasa lafiya su kuma ba likitoci ba sun ce akwai dalili.
Wani mai kyamis a unguwar Tukuntawa Ahmad Umar ya ce mafiya yawan masu kyamis basa bin dokar da aka gindaya na sayar da magani.
Ya ce a ayanzu kyamis waje ne kawai na nenan kudi da al’umma kuma suke taimakawa a tara.
Ya ce akwai da dama masu kyamis da ke rubutawa marasa lafiya magani sakaka ba tare da sanin me ke damun sa.
“Ko da yake bana cikin irin wadannan masu kyamis din amma dai masu kyamis suna abin da suka ga dama.
“Duk wanda ya zo siyan magani wajen ba tare da takardar da likita ya rubuta ba nakance masa koma ka ga likita” a cewar sa.
Shi ma wani mai kyamis Zaidu Salisu Falalu ya ce da gaskene masu kyamis na baiwa marasa lafiya magani ba tare da sanin me ke damun suba.
Sai dai ya ce ba duka ba ne aka taru aka zama daya, domin shi dai yana iya kokarin sa.
Ya ce yakan tambayi marasa lafiya kon sun yi gwaji kafin ya ce zai basu magani.
Sai dai ya ce idan yaga lamarin kamar ya tsananta to sai ya basu magani ko kuma ya yi musu allura.
Ko litoci na sane da wannan al’amari?
Tsohon shugaban kungiyar likotoci ta kasa reshen jihar Kano Sunusi Muhammad Bala ya ce doka ta tanadarwa masu kyamis yadda za su gudanar da sana’ar su.
A cewar sa abin da akasan kyamis da shi shi ne ya bada taimakon gaggawa, ya kuma sayar da magani idan likita ya rubuta.
Dakta Bala ya ce ko kadan ba aikin mai kyamis ba ne ya yiwa marasa lafiya gwaji ko kuma ya basu maganin cuta.
Ya kuma ce dukkanin marar lafiyar da ya zabi ya dinga zuwa kyamis domin a duba lafiyarsa to kuwa lafiyar sa ba za ta taba dai-daita ba.
“Abin da masu kyamis za su ce ko kana da typhoid da malaria su kuma baka magnain da zai iya kashe ka.”
Dakta Bala ya ce kungiyarsu ta aike da wani kudirin doka gaban zauren majalisar jiha da zai dinga daukar mataki kan masu yi musu sojan gona a ayyukan su.
Ya kuma ce kudirin dokar idan aka amince da shi zai hukunta dukkanin ma’aikatan lafiyan da suke shiga ayyukan likitoci suna fakewa.
Ya kuma shawarci jama’a da akowanne lokaci su guji jefa lafiyar su cikin hadari.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
Hausa
Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.
Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.
Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.
Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.
Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.
“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.
“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”
Hausa
Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote
Nasiru Yusuf Ibrahim
Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.
Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .
Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.
“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.
Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun da basu samu damar biya ba a baya.”
Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari, gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.
“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al’umma.” Dangote.
Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.
“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”
Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada rade-radi da jita-jita.