Connect with us

KANUN LABARAI

Rufin asirin amarya: An fara bayar da hayar kayan kicin na amare a Kano

Published

on

 

Zulaiha Danjuma

Wani dan Kasuwa a nan Kano da ke kasuwar Sabon Gari Usman Mustaph, ya fara bayar da hayar kayan kicin ga amaren da za a yiwa aure kuma iyayen su ba su da halin saya.

A wata hira ta musamman da jaridar Kano Focus Usman ya ce sun fito da wannan sana’ar ne domin tallafawa sabbin amare da iyayensu kar su ji kunya.

Ya ce duk mai bukata za a bashi hayar kayan kicin na sati daya akan kudi N20,000, na sati biyu kuma N35,000 ya yin da suke bayar da na wata guda akan kudi N70,000.

Ya ce ‘yan mata masu yiwa samari gara, ana basu hayar filas na shayi, ko filas na zuba abinci don dai a birge saurayi idan yazo zance.

Sai dai ya ce akwai sharudda masu tsauri game da kayan nasu da sai mai karba ya amince sannan za a bashi.

Sharadin shi ne duk wanda ya fasa ko ya lalata wani abu daga cikin kayan da ya karba to zai biya kudin sabo.

Haka kuma idan aka kara kwana guda daga cikin kwanakin da ka kayyade to za a ci tarar mai karba wasu kudade na musamman.

Ko an fara karbar?

Malam Mustapha ya ce tun daga ranar da ya kaddamar da shirinsa na fara wannan sana’a jama’a da dama ke kiran sa a waya domin neman karba.

Ya ce a rana yakan karbi waya sama da goma duk na mabukata karbar hayar kayan.

A don hakan ne ma ya ce ba zai fara baiwa kowa ba sai ya gudanar da shiri na musamman da zai taimakawa kasuwancin nasa.

Ya kara da cewa ba wai jama’ar Kano ba harma daga jihohin Sokoto Zamfara Kaduna Da Jigawa ana kiransa domin karbar kayan.

“Abinda muke yi yanzu shi ne tallata hajar mu domin muga shin mutane ma za su karba ko akasin haka.

“Mutane na kirana suna ce min suna bukatar kayan, don Allah mu yi sauri mu fara kuma da zarar mun fara mu sanar da su.

Ko hakan zai haifar da ‘DA mai ido?

Wata malama da ke ba da shawarwari ga mata kan al’amuran aure dake kungiyar Idyllic Coaching and Counseling Services Khadija Ibrahim ta ce  wannan al’amari da ya kunno kai ba zai haifar da ‘da mai ido ba.

A cewarta mata da maza yanzu sun fada rayuwar karya na karbar hayar kayan lefe su kuma mata hayar kayan daki da hakan ke kashe aure saki ba kaidi.

Ta ce karbar irin wadannan kayayyaki na nufin mika kai ga rayuwar karya, rashin gasgata juna da hakan ke kassara aure.

Son a Burge

A cewar malama Khadija mafiya yawan wadan da ke fadawa cikin wannan al’amari na bukatar a ce sun burge ne kawai.

“Mutane na bukatar burge jama’a su nuna arziki bayan a zahiri karansu ba kai tsaiko ba.

“kuma duk wannan al’amarin ana son burge ‘yan soshiyal media ne kaiwai, kuma da zarar ka burge su ka jefa kanka cikin hadari.”

“Nasha jin labarin mazan da ke karbar hayar akwatun lefe bayan sati biyu da auren sai kaji ance barayi sun haura.

Sakamakon yin ‘dage

Malama Khadija ta ce mutane a wannan zamani na son yin rayuwar ‘dage’ da hakan  ke jefa su cikin rudani da rashin samun nasarar auren.

“A wannan zamanin jama’a na yi rayuwar karya wajen aurensu da kuma kowa ya san karya bata dorewa.

“Lokaci na nan zuwa da abokin zamanka ko abokiyar zamanka za ku fuskanci karya kuka shirya kan ku.

“Idan kuka fahinci cewar wadannan kayan kicin din, wadannan lefen da sauran su duk haya kuka karba to a nan ne fa za ku fara gane irin matsalar da kuka jefa kanku.” Ta ce

Hayar Lefe

Wani bincike da jaridar Kano Focus ta gudanar ta gano samari da yawa na karbar hayar akwatinan lefe da ma lefen kansa a wasu lokutan.

Ibrahim Idris wani dan kasuwa a nan Kano ya ce ya karbi hayar akwatunan lefe ne saboda yana son yin auren amma kudaden sa ba za su is aba.

“Na karbi hayar akwatunan lefen ne saboda kudin lefe na ba zai isa har na sayi akwatin ba.

“Kuma matata bata taba ganewaba saboda naje na biya kudin da kandan kadan har na kammala biya” a cewar sa.

Shi kuwa wani mai sana’ar tuka baburin adai-daita Sahu Garzali Shu’ibu ya ce ya karbi hayar akwatunan kayan lefe da kayan a ciki baki daya.

“Na karbi hayar akwatunan lefe makare da kaya sai dai abin takaici matata ta bankado ni.

“Masu kayan suka dinga zuwa gidana saboda na kasa biyan su ban iya biyan kayan ciki ba balantan akwatunan.

“Haka kawai wata rana suka zo gidan suka gayawa matata komai.

“Baya da na dawo ne ta fara tambayata ya akayi na hada lefen da na kai mata?

“Hakan ya sanya rigimar yau daban ta gobe daban daga karsehe dai ta bar gidan.” Ya ce.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Hausa

Wani Attajiri ya ba da kyautar makabarta a garin Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Wani Attajiri Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya ba wa mutanen garin Tsakuwa dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu kyautar makabarta.

Shugaban kwamitin Ilimi na Kungiyar Tsakuwa Mu Farka Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ne ya bayyana haka ranar Asabar.

Ya ce attajirin ya danka amanar makabartar ne karkashin kulawar Tsakuwa Mu Farka.

Malam Abdullahi Yusuf Wagadi ya ce Kungiyar Tsakuwa Mu Farka za ta tattauna yadda za a katange makabartar a taron da shugabannin Kungiyar za su yi nan gaba.

Kunshin sanarwar ya ce “Wannan ita ce tsohuwar Maqabartar Makau wacce dattijon arziki Alhaji Yakubu Dan-Zainab ya kuma sabunta kyautar ta ga Al’ummar Tsakuwa, karkashin kulawar Kungiyar Tsakuwa Mu Farka. Allahu SWT ya saka masa da mafificin Alkhairi tare da kai ladan gare Shi.

“Idan Allah ya kai Mu taron Shugabancin Tsakuwa Mu Farka da muke gabatarwa online wannan karon zai zo ne a wannan banban dandalin, tattaunawar Meeting din zaifi mai da hankali ne wajen laliban hanyoyin da za mu bi wajen katange wannan makabarta dama sauran makabartunmu da suke garin Tsakuwa.

“Lokaci ya yi da dole sai mun dauko wannan al’adar saboda yadda kullum kasa take kara daraja. Siyan filin makabarta ya fara zamarwa al’umma abu mai wahala birni da kauye.”

Continue Reading

Hausa

Ba bu inda nace nafi Yan Najeriya shan wahalar Tsadar rayuwa, amma ina Fatan matsalar ta zamo tarihi -Dangote

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.

Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .

Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.

“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafemu”, inji Sanarwar.

Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun  da basu samu damar biya ba a baya.”

Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A  bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari,  gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.

“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen  ciyar da al’umma.” Dangote.

 

Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.

“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da  neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”

Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada  rade-radi da jita-jita.

Continue Reading

Upcoming Events

There are no upcoming events at this time.

Facebook

Twitter

Trending