Connect with us

KANUN LABARAI

Shin da gaske ne maza na kukan aure?

Published

on

Zulaiha Danjuma

kukan aure wani lamarine da aka saba gani ga mata musamman ma lokacin da aka dauke su za a kai su dakin mazajen su.

Sai dai wani bincike da jaridar Kano Focus ta gudanar ya nuna cewa dayawa maza ma na shan kuka lokacin bikin su.

A zantawar jaridar Kano Focus da wasu matasa a nan Kano sun ce tabbasa maza kan yi kukan aure bisa dalin shakuwa da uwa, numa farinciki, jin dadin mallakar amaryar da sauran su.

Shakuwa da uwa

Wani matashi a nan Kano Umar Faruq Musa da ke sana’ar daukan hoto ya ce ya sha ganin angwaye na rusa kuka ranar daurin auren su ko kuma awurin biki.

Ya ce wasu da ya gani suna irin wannan kukan tsananin shakuwa ce da mahaifiyar su ya sanyasu gurshekar kuka.

“Mun zo tafiya da shi domin kai shi dakin sa, nan take mahaifiyarsa ta fara kuka shima sai ya barke da kukan”

“A lokacin ma akwai wadanda suka nuna cewar yana namiji amma yake sheka kuka dan zai bar gida?  Sai dai a fahintata shakuwa da uwa ba wasa bane.

“Suma masu fadar hakan watakia basu shakun bane kamar shi” a cewar sa.

Farin ciki  

Haka zalika wani magidanci da ke unguwar Gaida a nan Kano Nafi’u Usman ya ce angwaye da dama na yin kuka dalin farin ciki.

A cewarsa wani angon bai taba tsammanin jama’a za  su taru saboda shi ba, amma da ya waiga ya ga irin jama’ar da suka taro dominsa farinciki kan saka shi kuka.

“A fahintata abune da ya kamata, dai-dai ne ango ya sha kukan sa lokacin biki ba gazawa ba ne farin ciki ne.

Idan farin ciki ya cikawa mutum zuciya ba kowane zai iya dannewaba, tilas wani sai ya amayar an gani” a cewar sa.
Haka dai wani magidancin Injiniya Aliyu Ibrahim ya  ce ya rarrashi angwaye da dama  da suka sha kuka lokacin bikin su.

“Abokina da ya yi kuka a bikinsa ya yi ne sakamakon ganin  abokanan arziki da suka halarci   daurin auransa.

“Ya fara godewa jam’a ne kawai sai muka ga idanunsa na rawa, ba jimawa kawai sai muka ji ya barke da kuka” ya ce..

Wahalar samun mata

Wasu matasan sunce angwaye na yin kuka ne domin yi wa kai barka da samun matar.

A cewar su wasu mazan har ranar da za a daura musu aure suna shakkun ko matar mallakinsu ce ko kuma za su iya rasa ta.

A cewar Usman Sa’idu da kyar ya rarrashi abokinsa da ya fara kukan barka-barka.

“Abokina da kyar muka rarrasheshi, saboda yunkurin salwantar masa da amaryar da aka yi,

“Danginta suna ta son hadata da wani na dangi sai da kyar Allah ya kwato ya bashi.

“Ai kuwa ana kammala daurin aurenne ya samu wuri ya dinga rusa kuka abin sa saboda ya tabbatar ya kubuta.

Ko ya da ce aga ango na kuka?

Wasu ba’arin matasan sunce ko kadan bai da ce ba aga ango na kuka, la’akari da cewar mata aka sani da yin hakan.

A cewar Malam Sa’idu mazaunin unguwar Jakara a nan Kano  namiji da karfin zuciya aka sanshi ba wai kawai saboda an daura masa aure ya kama kuka ba.

“A fahinta ta matukar namji ya fara da kuka tun daga ranar bikin sa to matarsa ta samu lagonsa .

“Haka kuma wadanda basu san dalilin kukan sa ba za su yi masa kallon kuriciya ne kawai” a cewar sa.

Ra’ayin mata

Sai dai daga bangaren mata kuma sun ce babu wani aibu dan namji ya yi kuka a bikin sa.

Rukaiyya Tijjani da ke sana’ar kwalliyar mata ta ce ko kadan babu abun kunya dan namaji ya sha kukan sa.

Ta ce wasu ma kafin aurensu sun shan yin kuka a gaban ‘yan matan su ballantana maganar aure.

Ta ce taga maza da suka yi kuka gaban yan matan su har kashi uku domin neman sasantawa bayan da suka samu matsala.

Sai dai a ra’ayin Khadija Sani Maitama  tace, matukar taga namiji yana kuka ranar auren sa to za ta yi masa kallon dan soyayya ne kawai.

Ta ce dukakanin wanda ya aibunta namiji don ya yi kuka akan matar da yake so tabbas bai samu wadanda za su yi kuka a kansu ba ne.

Bai  kamata namiji ya yi kuka ba

Wasu daga cikin matan ra’ayin su ya banbanta inda suka ce bai kamata namiji ya ya yi kuka ba sabo da kawai ana bikin sa

A cewar matashiya  Rabi’a Namaradda  bashi da ma’ana, a ga namiji na kuka a bikinsa.

“Gaskiya kamar ya bada kaine,  wasu ma cewa za su yi angontama sai da yayi kuku a ranar”

“Na taba zuwa wata walima naga ango na kuka mutane suka fara bai dace ba, bai dace na miji yayi kuka ba”

“Kamar ya rage martabar sane na mazaje, kamar a cikin mazajen ya dawo na kasan ne kamar shi ba gwarzon namiji bane” a cewar ta.

Haka zalika Amira Sani da ke unguwar ciranci a nan Kano ta ce duk namijin da yayi kuka a bikin sa to ba shakka sakarai ne

“Gaskiya ina yiwa duk namijin da ya yi kuka a bikin sa kallon sakarai”

“kuka a wurin namiji saboda ana yi masa aure shashanci ne a ganina gaskiya”

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending