Connect with us

KANUN LABARAI

 Kungiyar ‘yan sintiri ta kama wani kwararre kan kwacen waya a Kano

Published

on

 

Aminu Abdullahi

Kungiyar ‘yan sintiri ‘Vigilante’ da ke unguwar Ja’oji a karamar hukumar Kumbotso a nan Kano ta kama wani matashi Muhammd Nasir da ya kware wajen yiwa al’umma kwace da raunata su.

Kano Focus ta ruwaito ‘yan sintirin sun samu nasarar kama matashinne da yammacin ranar Laraba  a nan Kano.

A cewar shugaban kungiyar sintiri ta ja’oji Malam Musa Isah Muratala ya ce jama’ar unguwar ne suka sanar da su wasu matasa na yawo a unguwar suna yiwa jama’a kwace.

Ya ce bayan samun rahoton ne suka mai da hankali wajen fakon matasan, kuma suka samu nasarar kama guda daga cikin su.

Malam Musa ya ce  matasan sun addabi jama’ar unguwar ainun da sace-sace da kuma illata jama’a kafin yin kwacen.

Ya kuma ce tuni suka mika matashin ga ofishin ‘yan sanda da ke unguwar sheka.

Wani  daga cikin wadanda aka yiwa kwacen waya a unguwar mai suna Nura Auwalu ya ce suna cikin baburin adai-dai ta sahu kwatsam sai barayin suka sha kansu tare da zare musu wukake.

“Barayin a cikin baburin adaidaita sahu suke sun kwace waya ta tare da ta abokin tafiyata da ke cikin baburin da nake.

“Ihun da mukayi ne ya sa mutane suka fito sai dai ragowar sun gudu amma an kama daya daga cikin barayin”, inji Nura Auwalu.

Ya kara da cewa ana tsaka da lamarinne ya rike daya daga cikin barayin inda kuma al’umma suka yi tara tara aka kamashi.

Itama wata mai suna Rukayya Muhammad ta bayyanawa jaridar Kanofocus cewa gungun barayin sun zone dauke da makamai inda kuma suka kwace musu wayoyi.

A nasa bangaren direban adaidaita sahun mai suna Abba Yusuf mazaunin unguwar Rijiyar Lemo yace bai taba ganin tashin hankali irin haka ba.

“Na dauko fasinjoji a bayan mashin dina kawai sai ga wasu mutane a  adaidaita sahu suna cewa sune wadancan.

“kafin na tsaya sai suka kangene suna cewa a cire musu ni bansan mai suke nufi ba kawai sai gani nayi sun kai mana wafta. a cewar sa.

Sai dai kuma daya daga cikin wadanda aka kama da zargin kwacen cewa ya yi tunda fari abokan nasa ne sukace ya rakasu siyan sticker da za su manna a baburin adaidaita sahun su, amma su ba barayi bane.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

 

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.

 

“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.

 

“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.

 

“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.

 

“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

 

 

Continue Reading

Hausa

Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.

Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.

Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.

A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.

Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Continue Reading

Hausa

Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Published

on

Nasiru Yusuf Ibrahim

 

Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.

Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.

Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.

A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.

Continue Reading

Trending