KANUN LABARAI
Makafi da guragu za su tsaya takarar chairman da kansila a Kano
Aminu Abdullah
Masu bukata ta musamman da suka hadar da guragu da makafi ne suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar chairman da kansila a zaben kananan hukumomi da ke tafe.
Kano Focus ta ruwaito cewa duk da irin kalubalen da suke fuskanta na rayuwa amma sunce bana suma sai an dama da su.
A tattaunawar jaridar Kano Focus da shugaban kungiyar masu bukata ta musamman a nan Kano malam Musa Muhammad Shaga, ya ce akwai nau’ikan masu bukata ta musaman da za su shiga zabe a fafata da su.
Malam Shaga ya ce Jamilu Ali Haruna da ke takarar shugabancin karamar hukumar Bunkure makahone da kuma tuni ya siyi takardar tsayawa takara.

Haka kuma akwai Adamu Ibrahim Maikoriya da yake ta karar Kansila a unguwar Sani Mainagge dake karamar hukumar Gwale da shima makaho ne.
Yace dukkan ‘yan takarar sun riga sun sayi takardar tsayawa takara kamar yadda doka ta tanada, kawai suna jiran a shiga zabe ne.
A cewar sa rabon da a samu wani mai bukata ta musamman ya shiga zaben tun lokaci da wani gurgu Malam Kabiru Ado Yakasai ya tsaya takarar shugabancin karamar hukuma Nasarawa kuma bai Nasara ba.
Ya ce al’umma sun yadda dashi amma sakamakon rashin iyayen gida haka aka kwace takarar daga hannun sa tare da yi masa alkawarin mukami mai tsoka.
Sai dai bayan da aka ci zabe ko mukamin masinja bai samu ba.
Rashin goyon baya
Malam Shaga yace duk da irin kokarin da masu bukata ta musamman ke yi wajen nuna kansu amma basa samun goyon bayan al’umma.
Ya ce sukan zama abin kallo ko ayi musu dariya ko kyara duk lokacin da suka nuna sha’awar su ta shiga al’amuran siyasa a dama dasu.
“Rashin gwadamu shi yasa mutane suke ganin kamar ba za mu iya ba amma matukar aka bamu dama zamu bada mamaki.
“Tsohon gwamnan jihar Nasarawa Tanko Almakura naga shima wakili ne a cikin kungiyar masu bukata ta musamman ta kasa domin yana fama da lalurar ji.
“Kuma kowa yaga irin kokarin da yayi wajen samun ‘yancin masu bukata ta musamman,” a cewar sa.
A don hakan ne ya bukaci al’umma da su dinga zabar masu bukata ta musamman domin suma su nuna tasu kwarewar
Za a basu Fom din takara kyauta
A nasa bangaren shugaban hukumar zabe ta jihar Kano farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ce fom din takara kyautane ga duk mai bukata ta musamman.
Sheka ya ce matukar jami’iyyu suka kawo su a matsayin wanda suka ci zaben cikin gida to hukumar za ta basu takarda tsayawa takara kyauta.
Ya ce hukumar tana siyar da takardar tsayawa takarar shugaban karamar hukuma akan N250,000 yayin da kuma takardar tsayawa takarar kasila take siyarwa akan N150,000.
Sai dai ta ce matukar aka kawo su a mtsayin wadanda aka tantance to za ta basu kyauta.
A cewarsa hukumar ta yi hakanne domin ta karfafawa masu bukata ta musamman gwiwa don ganin ana damawa dasu a cikin harkokin siyasa.

Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano

Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”

Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye

Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.

Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa

Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.

Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.
