KANUN LABARAI
Ko kun san mata dayawa a Kano basa wanka lokacin sanyi
Aminu Abdullahi
Wani bincike ya nuna yadda mata a Kano da ma saurarn sassan kasarnan ke kauracewa wanka lokacin sanyi.
A zantawar Kano Focus da wasu ‘yan mata a Kano sunce galibinsu kan kwashe kwanaki uku zuwa sati guda suna dakale a maimakon wanka.
Ko da yake al’umma na cewa lokacin sanyi lokaci ne da mata kan shiga takura ainun da hakan ke sanya su kauracewa wanka a lokuta da dama.
Amina Abubakar mai shekaru 23 da ke unguwar Na’ibawa a nan Kano ta sahidawa Kano Focus cewar da zarar lokacin sanyi ya yi , itakam ta yi sallama da wanka a kowacce rana.
Ta ce ta kan kwashe kwanaki uku a jere ba tare da wanka ba, sai dai ta dan wanke hannu da fuska ta kuma shafe su da mai.
A cewar ta da zarar sanyi ya yi tsanani to takan shafe mako guda ba tare da yin wanka ba.
“Kaga idan nayi kwaskwas dina shikenan koda fita zanyi danasa turare na shafa hoda babu mai gane cewa banyi wanka ba.
“Kuma ni abinda yasa bana wanka sosai saboda akwai sanyi kuma gaskiya zan iya kamuwa da cutar mura matukar nace zan dinga yi kullum,” a cewar ta.
Ita kuwa wata budurwa Hajara Abdullahi mai shekaru 24 da ke Unguwar Tunkuntawa ta ce maimakon wanka takan yi kwaskawarima ne da safe ta kuma mulke jikinta da mai.
Ta ce bayan kammala aikin yamma idan taga da faraga to sai ta yi wanka.
“Na kan yi wanka lokacin sanyi amma ba da safe ba sai bayan la’asar idan nayi girkin dare sai inyi wanka.
“Sai kuma da yamma ko washe gari zan sake wanka idan naga da hali.
“Amma idan zan fita unguwa nakanyi wanka da safe kamar bayan karfe goma.
“Idan kuma sammako zanyi barin wankan nakeyi saina dawo,” Inja Hajara.
Wata budurwar kuwa ‘yar shekaru 20, mai suna Rukayya Umar da ke Rijiyar Lemo ta ce tana yin wanka sau daya a sati ne kurum.
A cewar ta musamman idan ana sanyi mai tsanani bata ga dalilin bata lokaci wurin yin wanka ba.
Ta ce yin wanka kullum a lokacin sanyi ganganci ne, domin yin hakan kan haddasa mata ciwuka daban daban musaman cutar Nimoniya.
“Ko da yake ban fiye fita ba idan ba makaranta zanje ba, ko da naje makarantar ma a guri daya nake zaune, shiyasa bandamu nayi wanka ba.”
“Yin wanka lokacin sanyi yana takura min sosai. inji ta.
Ita kwa wata budurwa Hafsat Sulaiman ta ce ba ta da tsari wajen yin wanka lokacin sanyi.
“Ni bani da tsari wajen yin wanka lokacin sanyi, nakanyi wanka ne kawai idan naga rana ta fito.
“Ba a ganin alama ko kadan idan banyi wanka ba saboda yanayin sanyi baya nunawa.” A cewar ta.
Ta ce kafin shigowar sanyi tanayin wanka akalla sau uku a rana amma ba yadda ta iya dole ta rage yin wanka saboda matsalar da yin hakan kullum zai jawo mata.
Hausa
Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta koma Northwest University, Kano
Nasiru Yusuf Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar maidawa Jami’ar Northwest sunanta na asali, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
KANO FOCUS ta samo wannan sanarwa ne daga Keamishinan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Dr Yusuf Ibrahim Ko far mata, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Dr Kofar Mata ya ce “A zaman majalisar zartarwar ta gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf na 21 yau Juma’a 29th November 2024 (27th Jumada Awwal 1446) ta amince da maidawa ta Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmamawa ga Marigayi Dattijo uban ƙasa Dr. Yusuf Maitama Sule, an sawa sabuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar makarantar Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman yau, babbar makarantace daidai da kolejin ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada.
“Haka zalika makarantar Audu Bako Dambatta da kuma makarantar malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantune don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
“Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoi zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano, harda gyaran shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu. Allah Ya taimakemu.”
Hausa
Zan ɗora ƙaramar hukumar Nassarawa kan manufofin jagoran Kwankwasiyya – Ogan Ɓoye
Nasiru Yusuf Ibrahim
Ɗan Takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jam’iyyar NNPP Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya yiwa jama’arsa godiya kan goyon bayan da suke nuna masa.
Ogan Ɓoye ya ce yayi farin ciki matuƙa da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya yi alƙawarin cewa zai yi iya ƙoƙarinsa idan ya yi nasara a zaɓe wajen ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Ya ce, zai ɗora ƙaramar hukumar kan manufofin jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso na gina rayuwar talakawa ta hanyar inganta ilimi lafiya da tattalin arziki.
A ƙarshe Ogan Ɓoye ya yi kira ga jama’ar ƙaramar hukumar su fito ƙwansu da kwarkwata ranar zaɓe don kaɗa masa ƙuri’a.
Ogan Ɓoye dai na cikin fitattun jagororin matasan Kwankwasiyya da suka yi suna wajen tallafawa matasa ƙarfi.
Hausa
Ruwan sama na barazanar raba hanyar Dawakin kudu zuwa Tsakuwa
Nasiru Yusuf Ibrahim
Mamakon ruwan saman da ake yi a ‘yan kwanakin nan na barazanar raba hanyar da ta tashi daga Dawakin kudu zuwa garin Tsakuwa.
Wani mazaunin yankin Malam Umar Musa Aliyu Dukawa ya ce zaizayar ta shafi gadar fansallah ne dake Maishudi kan hanyar zuwa garin Tsakuwa.
Malam Musa ya ce a baya ma wurin ya taba riftawa, mutanen garin Tsakuwa suka yi gangami suka gyara.
Ya kara da cewa tsohon dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Dawakin kudu da Warawa Hon. Mustapha Bala Dawaki ya taba gyara hanyar.
A don haka ya ce akwai bukatar hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar kafin ruwan sama ya raba ta biyu.